An gano wata halittar ruwa mai dogayen hakora
wanda ba a taba gani ba bayan guguwar Harvey
a Amurka.
Wata mata mai suna Preeti Desai ta ga wannan
halittar a gabar tekun Texas kuma ta sa hoton
a shafin Twitter, tana neman agaji. tambayoyi.
Matar ta tura hotuna da yawa sai ta rubuta,
''toh, masan ilimin halittu na twitter, mene ne
wannan?''
Wannan na daya daga cikin halittu tara na
kasar India wadanda ba a taba ganin irin su
ba.
An gano sababbin nau'in halittu guda 5000.
An tura tambaya ga masanin illimin halittu da
kiwon kifi Dokta Kennith Tighhe, wanda yake
tunanin macici ne mai hakora masu kaifi.
Ya kuma ce halittar za ta iya zama nau'in kifi
mai kama da maciji.
Sai dai ya ce irin wannan halittun guda uku ne
da ake samu a Texas, wadanda suke da
manyan hakora masu tsini.
Ana kyautata zaton cewa guguwar Harvey da
iska mai karfi ne sanadiyyar kawo wannan
halittar gabar teku.
Halittar da a ke kira Tusky Eli ana samunta ne
a cikin Tekun Atlantika.
Desai wanda ta je gabar tekun don nazarin
girman barnar da guguwar ta jawo, ta shaida
wa BBC cewa: ''ba a taba zaton samun
wannan halittar ba, ba abin da aka saba gani
ba ne a bakin teku. Ina tsammanin halittar ta
fito bakin tekun ne daga tsakiyar tekun."
Ta ce, ''Abin da ya fara zuwa raina shi ne
zakuwar sannin abin.''
Desai ta kara cewa, "na dauki hoton ne na tura
a shafin Twitter saboda na san masana
kimiyya da dama suna amfani da shi, daga nan
ne wata kawata ba tare da bata lokaci ba ta
kira Dokta Tighe.''
Ta ce ''ina bibiyan masana kimiyya da dama,
akwai alumma mai kyau da yawa, wadanda
suke taimakawa sosai, tun ba a lokutan da
tambayoyi da suke da alaka da son fahimtar
rayuwar halittu ko tsirrai ba."
A karshe ta ce ta bar wannan halitta a wurin da
ta tsince ta wato bakin tekun, a tunanin cewa
za ta koma inda ta fito.

No comments