Shahararren me bayar da Umarni na Finafinan Hausa, Falalu A. Dorayi yayi wani zungureren rubutu akan wani zargi da yayi cewa sarkin Kano Muhammad Sanusi na II ya nada mawakin kudancin kasarnan wato Korede Bello sarkin mawaka, Korede Bello dai ya halarci hawan Fanisau da akayi a garin Kano cikin shagulgulan babbar sallah da suka gabata, kuma an yimai nadi ya hau doki tare da yarima Adam dan Sarkin Kano.
To bayan nanne sai Korede Bellon ya saka hotunan a dandalinshi na sada zumunta da muhawara yayi rubutun dake nuna alamar cewar kamar an bashi sarautar sarkin mawaka a Kano din, to saidai babu wata alama ta bikin nuna wannan nadi da akawa Korede Bello ko kuma ita masarautar Kano bata bayyana hakan ba.
Da wancan rubutun na Korede Bellone Falalu yayi amfani ya caccaki sarakuna da masu kudi sa sanannun mutane na yankin Arewa akan cewa basu kishin mutanensu da al'adarsu, ra'ayoyin 'ya 'yansu kawai suke bi da mafi yawanci bama a kasarnan suke karatu ba.
Ga rubun da Falalu yayi kamar haka
"
G A S K I Y A K O KARE CE..... Zanyi tsokaci akan Hutunan da suke sama. Duk da dai ba halina bane shiga sabgar mutane.
Ina magana ne akan nadin Sarautar SARKIN WAKA da ake cewa an yi wa wani mawakin kudu KOREDE BELLO a Kano.
In ta tabbata kamar yadda mawakin ya wallafa a page dinsa..
To lallai mawakan hausa na Arewa sai addua. Nasan duk rashin basirar Mawakanmu ba suyi Lalacewar da sai an tsallaka Lagos za'a samo musu Sarki ba.
Koda yake ba abin mamaki bane dama haka manyan Arewan namu suke, lokacin bukatarsu suke nemanmu, lokacin moriyar sai dai mu gani a wajan yan kudu.
Ina mamakin yadda ciki yake manta kyautar jiya. Duk wahalar da mawaka kiyi akan masu kudi, masu Sarauta, da Yan siyasa na Arewa wajan yi musu wakokin yabo da kwarzantasu abin takaici sai kaga babu wani lada.
Tun da aka nada Sarkin kano na Yanxu Dan maje, Nazir Sarkin Waka ya sashi a gaba da yabo da kirari a cikin wakenma akwai inda ya hararomasa zama Sarkin kano, kuma Allah da ikonsa ta tabbata.... Bayan ya zama Sarkin Kano bai bar wake shi ba har gobe. Kuma in zaayi adalci a duk wakokin da akaiwa Sarkin kano banajin akwai wadda ta kai ta Nazir Ahmad Tasiri.
Tabbas nazir yafi Korede bello cancantar sarautar duk da bamu san irin kalaman da Korede ya zuba a wakar da yaiwa Sarkin ba.. Sarautar waka a garin hausawa sai mai jin hausa, a tsallake a dauko wani ko hausa cikakkiya ba ya ji, bai taba yin Waka da hausa ba, bai yiwa kano da Kanawa ko baiti daya ba, bai yiwa Sarkin kano waka ba, a bashi wannan mukami? Shikenan anci yaki an barmu da kuturun bawa.
A bayyane yake mafi yawan manyanmu na Arewa suna mutunta ra'ayin Yayansu ne kawai, su kuma Yayan nasu ba su girma a kasar ba ma, ba su damu da komai na hausa da Al'ada ba, Wannan yasa
Biki, suna, bthday, murnar kammala karatu, baiko da duk wani abin murna Mawakan kudu ake daukowa su baje kolinsu. In aka ce su dauko mawakan arewa sai suce Yan kauye ne.
Idan har Nazir bai zama Sarkin Mawakan Sarkin Kano ba to banga Wanda ya kaishi ba. Ku girmama al'ummar ku sai wata al'ummar ta girmama ta. Ni nasan dan kudinku da kudin yayanku suke zuwa sabgarku. A tallafi gida kafin waje.
Wannan Ra'ayin Baba Falalu ne."
Da wallafa wannan rubutu na Falalu sai abokan aikinshi da sauran wasu masu taka rawa a masana antar finafinan hausa suka fara bayyana ra'ayoyi akan wannan batu.
Saidai wani bawan Allah ya kalubalanci Falalu inda yacemai maganar da yayi bata da tushe domin bashida wata hujja akan cewa an nada Kerode Bello sarkin mawakan Hausa kumama yawancin mawakan in banda irin su Ala duk kwaikwayar mawakan yankin kudu sukeyi, mutumin ya kara da cewa kai hatta su masu shirya finafinan mafi yawanci kwaikwayar finafinansu sukeyi basa amfani da ainihin al'adar hausa.
To saidai wannan batu bai yiwa falalu dadiba domin ya mayarwa da mutumin raddi dama wasu da suka bayyana ra'ayoyinsu.
Gadai yanda ra'ayoyin mutane suka kasance akan wannan batu.
No comments