WACECE MACE TA GARI? //4
ITACE MAI IBADA
Bauta dai shine dukkan abun da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi na daga zance da aiki.
Kuma duk mace ta gari zaka same ta da ibada, wato mai dagewa ce wurin bautar Ubangijinta. Sannan tana tsoron Allah da qanqan da kai garesa.
Kuma ta aminta tun daga farkon auren ta cewa aure ibada ne kuma Sunnah ne mai qarfi zata raya. Kuma duk abun da take yi a cikin gidan ta tun daga zaman auren tana da lada. Idan mace ta sa haka a ranta abubuwa dayawa a rayuwar aure zasu zo mata da sauki.
Itace mai dogaro ga Allah a cikin dukkan al'amuranta, kuma tana komawa gare shi a lokacin yalwa da lokacin tsanani. Kuma tana godiya gare Shi a cikin ko wane hali.
Mace ta gari sam bata wasa da sallolin ta biyar a gidan ta. Kuma ba a barin ta a baya wato tana tashi cikin dare ta roqi alkhairan duniya da lahira.
Tana qoqarin yin azumin nafila tare da izinin mijin ta.
Tana qoqarin yin kyauta da sadaqa.
Tana dagewa wurin yin addu'a. Duk abun da ya same ta na rayuwa to ta kan tsananta roqo.
Mai yawan ambaton Allah ce da Istigfari. Bakin ta danye yake wurin ambaton Allah ba ashar da maganganu marasa amfani ba.
Tana yin biyayya ga mijinta in har umurninsa bai sabawa mahalicci ba.
Kuma tana dagewa da sauran ibadodi na samun lada.
In baku manta ba Annabi (SAW) ya fada a hadisi:
(( ﺇِﺫَﺍ ﺻَﻠَّﺖِ ﺍﻟْﻤَﺮْﺃَﺓُ ﺧَﻤْﺴَﻬَﺎ، ﻭَﺻَﺎﻣَﺖْ ﺷَﻬْﺮَﻫَﺎ، ﻭَﺣَﻔِﻈَﺖْ ﻓَﺮْﺟَﻬَﺎ، ﻭَﺃَﻃَﺎﻋَﺖْ ﺯَﻭْﺟَﻬَﺎ، ﻗِﻴﻞَ ﻟَﻬَﺎ : ﺍﺩْﺧُﻠِﻲ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔَ ﻣِﻦْ ﺃَﻱِّ ﺃَﺑْﻮَﺍﺏِ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔِ ﺷِﺌْﺖِ .(( [ ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ].
" Idan Mace ta yi sallolinta biyar, ta yi azumin Ramadan, ta kuma kiyaye farjinta, sannan ta yi biyayya wa mijinta, Sai ace da ita: "Ki shiga aljannah daga qofar da ki ka gadama daga cikin qofofin Aljannah" [Ahmad ] .
Babu yanda za a yi a kira ki ta gari bayan kina tsallake sallah, wato yin sallah yana miki wahala.
Inaa! mace ta gari ta miki nisa, don ita rige-rige take wajen ganin ta kusanci Mahaliccin ta.
Yar'uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar

No comments