Fitacciyar jarumar fim din Hausa, Hadiza Gabon tayi wata tambaya ga masoyanta a dandalinta na sada zumunta inda ta tambayesu abinda suka fatan samu a rayuwarsu, Hadiza ta fara da kanta inda tace ita abinda take fatan samu shine dukiyar halal.
Daga nan sai masoyanta suka yita fadin irin abubuwan da suma suke fatan samu a rayuwarsu.
Daga cikinsu akwai wanda ya bayyana cewa "shi yana so Allah ya azurtashi domin ya sayawa mahaifiyarshi abinda take so". Gaskiya wannan fata nashi ya isa abin birgewa, ita kanta Hadizar saida tamai addu'a ta musamman, muna mishi addu'ar Allah ya cika mai wannan buri nashi, Amin.
No comments