DAGA CIKIN MANYAN LADUBBAN RANAR JUMA'A
Ranar juma'a itace idi na sati sati kuma ita rana
mafi alkhairi acikin sati,shiyasa Annabi s.a.w ya
sunnanta mana wadansu Ladubba da sunnoni na
musamman saboda dacewa alkhairi da falalar
wannan rana, ranar juma'a tana da Ladubba
masu yawa ga wasu daga cikin su:-
1-Wankan Juma'a.
"Wankane irin na janaba baya da wani bambanci
sai niyya kadai".
2-Sannan tufafi mafi kyau.
"Wato ana so ka yi ado na musamman dan ranar
juma'a, mafi kyawun tufafin mu sune fararen
tufafi".
3-Sanya Turare.
"Babu inda yafi dacewa kaje kama kamshi kamar
masallaci dakin Allah ,kuma babu ranar da yafi
dacewa aji kama kamshi irin ranar juma'a".
4-Yin Aswaki ko gyara baki da man gyana baki
ko hakora
5-Zuwa masallaci da wuri.
"Wanda yaje afarkon lokaci yana samun ladar
saka da Raqumi".
6-Tafiya a kafa zuwa juma'a shine mafi alkhairi
akan tafiya akan abin hawa.
"Wanda ya tafi a kafa duk taku daya yana samun
lada mai yawa"
7-Yin Sallar gaisuwar masallaci lokacin da
kashiga Masallaci.
"Koda liman yana Hudubane zakayi sallar raka'a
guda biyu na gaisuwar masallaci kamar yadda
Annabi s.a.w ya sunnanta"
8-Karanta Suratul Kahfi.
9-Sauraran Huduba da yin Shiru lokacin da Liman
yake Huduba.
"Yin magana lokacin Huduba sai sanya mutum
yayi asarar Juma'arsa".
10-Fuskantar Alqibla da kallon liman lokacin da
yake Huduba.
11-Kada ka riqa Qetara mutane.
12-Yawaita Salati ga Annabi s.a.w
13-Yawaita yin Sadaka.
14-Yawanta addua da rokon Allah a bayan Sallar
la'asar dan dacewa da lokacin amsa addua a
ranar juma'a.
15-Bai tabbataba daga Annabi s.a.w ko Sahabbai
ba akan yin Sallar nafila raka'a biyu bayan kiran
Sallar farko.
16-Bai tabbata ba daga Annabi s.a.w ko wani
daga cikin Sahabbansa ba suna yin nafila bayan
kiran sallar farko ba.
17-Kuma bai tabbataba a sunna yin gaisuwar
juma'a da happy Juma'at da sauran irinsu.
18-Yana cikin sunnar Annabi s.a.w daga
Hannuwa dan yin addua a lokacin Huduba ko
tsakanin Huduba guda biyu.
19-Sallar juma'a bata da wata sallar nafila
kafinta,sai dan bayan Sallar juma'a akwai nafilar
juma'a raka'a biyu ko raka'a hudu.
Allah ne mafi sani.
Allah yayi sakayyar aljanna ga wanda ya karanta
kuma yayi aiki da shi kuma ya yada zuwa ga
sauran yan uwa musulmai.
Amin.
ﺍﻟﻠـﻬﻢ ﺻـﻞ ﻋﻠـﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭ ﻋﻠـﻰ ﺁﻝ ﻣﺤـﻤﺪ ﻛﻤﺎ ﺻـــﻠﻴﺖ ﻋﻠـﻰ
ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭ ﻋﻠـﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ، ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠـﻰ ﻣﺤﻤـﺪ ﻭ ﻋﻠـﻰ ﺁﻝ
ﻣﺤﻤﺪ ﻛﻤﺎ ﺑﺎﺭﻛﺖ ﻋﻠـﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭ ﻋﻠـﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻓﻲ
ﺍﻟﻌــــــﺎﻟﻤﻴﻦ ﺇﻧﻚ ﺣﻤﻴﺪ ﻣﺠﻴﺪ

No comments