*ALLAH YA JIKAN SHEIKH MUHAMMAD NASIRUDDEEN AL-ALBANI!!*
✍��Rubutawa: *_Dr Rabi'u Umar Rijiyar Lemo, Kano_*.
21/07/2017.
Tun sama da shekaru ar'ba'in baya da suka wuce, babban malamin hadisin wannan karni Sheikh Muhammad Nasiruddeen Al-Albani ya wallafa wani littafi mai matukar fa'ida da tarin ilimi, mai suna
ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺣﺠﺔ ﺑﻨﻔﺴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻘﺎﺋﺪ ﻭﺍﻷﺣﻜﺎﻡ
A cikin wannan littafin shehin malamin ya yi bayanin wajabcin komawa Sunnah a babin akida da shari'a da haramcin saba mata. Haka nan malamin ya yi bayanin bacin gabatar da kiyasi da waninsa a kan Sunnah.
A fasali na uku kuwa shehin malamin bayani ya yi a kan Hadisul Aahad (wanda ba mutawatiri ba) hujja ne a babin Akida da hukunce-hukuncen shari'a, babu wani bambanci da shi da hadisi Mutawaatiri. A wannan fasali dai shehin malamin ya yi bayanin kin karbar hadisi ingantacce, da hujjar wai Aahad ne, bidi'a ne, ya sabawa abin da magabata na kwarai suke kai, na karba da aiki da dukkan hadisin da ya inganta daga Annabi S.A.W, a babin Akida da waninta.
A karshe Shehin malamin ya cike da bayanin Taqlidi da hukunce-hukuncensa.
Wannan littafi yana kyau malamai da daliban ilimi su karanta shi, su fahimce shi, su fito da abin da yake cikinsa, don kare mutane daga fadawa shubuhohin su BABAN BOLA, masu kwashe kwashen munanan ra'ayi da soke ingantattun hadisan Manzon Allah S.A.W.
Allah ka jikan Sheikh Albani, ka yi masa rahama, ka saka masa da Aljannar Firdausi, saboda kare sunnar Manzon Allah S.A.W da ya yi a rayuwarsa.

No comments