Showing posts with label Bangaren Addini. Show all posts
Showing posts with label Bangaren Addini. Show all posts
Babban malamin addinin musulunci na kasar Masar, Shawki Ibrahim Abdel-Karim Allam, ya fitar da wata fatawa inda ya haramta amfani da kudin intanet na Bitcoin.
A fatawar da a ka wallafa ranar Litinin, Shawki Allam ya ce ba a yarda musulmai su siya ko su siyar ko kuma su biya haya da wannan tsari na Bitcoin ba.
Ya ce amfani da kudin intanet na da hadari domin zai iya haifar da zamba da yaudara, kuma kasancewar tsarin maras tabbas, ya na iya cutar da jama'a da ma kasashe.
Babban malamin ya ce sai da ya nemi taimakon masana tattalin arziki kafin ya yanke wannan hukunci.
Mene ne Bitcoin?
Bitcoin na da abubuwa biyu da suka bambanta shi: kudin intanet ne kuma ana ganinsa a matsayin wani abu da za a iya amfani da shi a madadin kudi.
kan intanet sabanin kudaden takarda ko sulalla da ke aljihunka
Duk da cewa akwai wasu na'urorin bayar da kudi (ATM) na musamman da ke bayar da Bitcoin, ya fi dacewa a yi tunaninsu kamar 'yan kudaden intanet.
Kuma babu gwamnati ko kuma bankin da ke buga Bitcoin.
Wannan na nufin "ba kudin da doka ta amince da shi ba ne, ba za ka iya biyan harajinka ko kuma ka yi amfani da shi wajen biyan bashi ba", in ji Dr Garrick Hileman na fannin koyar da kasuwanci a jami'ar Cambridge.
Ana samar da Bitcoins ne ta wata hanya mai sarkakiya da ake ce wa "haka" (wato "mining, a Ingilishi), sannan wasu komfuntoci da ke hade a fadin duniya za su saka ido kansa.
Ana samar da kimanin Bitcoin 3,600 a ko wace rana - kuma a halin yanzu akwai kimanin kudin miliyan 16.5 da ke yawo.
Sai dai kuma, kamar dukkan kudade, darajarsa ya dangata ne ga iya kudin da mutane suke son saye shi tare da sayar da shi.

bbchausa.

Haramcin Kudin Internet Bitcoin - Fatawa

"Manzon Allah (S.A.W) Ma Ya Roki Allah Ya La'anci Duk Wani Shugaba Mai Kuntatawa Al'ummarsa.

"Zagin Da Ake Yi Min Ba Zai Hana Ni Ci Gaba Da Fadin Gaskiya Ba.

"Duk Malamin Da Zai Yi Amfani Da Kuri'arku Munafiki Ne", Kalaman Sheik Ahmad Gumi

Zagin da ake yi min ba zai hanani ci gaba da fadin gaskiya ba>>Sheikh Gumi

Wani faifan bidiyo da ya fito na tauraron fina-finan Hausa, Nura Hussain inda ya saka wani wa'azin malamin addinin Islama Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya caccaki shugaban kasa, Buhari da ma masu goyon bayanshi.
Anji malamin yana cewa yanzu dai shekara hudu sun tafi, babu abinda ya kara mana saidai talauci, du abinda kake da kadara ka sayar, shekara hudu ta tafi babu abinda suka karu sai yunwa da talauci da kara rarrabuwar mutane da kuma tsoro, to dayan biyu, in mun gayara yanzu ko muyi gyaran shekara takwas ko mu yi gyaaran shekara hudu. Fisabilillahi, barnar da muke ciki yanzu, muna bukatar shekara takwas ko muna bukatar shekara hudu mu gyara?
Malamin ya kara da cewa duk wanda ya jawo mana shekara hudu Allah ya la'aneshi.
Nura Hussain bayan yayi salati ga fiyayyen halitta yace, Ahmad Abubakar Gumi kamar yanda kace Allah ya la'anemu saboda muna yin Buhari to kaine Allah ya la'ana, kaine la'antacce a gurin Allah, ya kara da cewa, manzon Allah (S.A.W) ya ce mana. La'ana tana komawa wanda suka yi ta. Idan kayi la'ana wannan la'anar tana tashi sama sai ta duba taga kaine la'ananne ko kuwa wanda ka yi wa shine la'ananne? Sai ta fadawa wanda i dace, saboda haka la'antar zata koma gareka dan baka da hujjar la'anar mu.
Ya kara da cewa, mun mun yarda da cewa shugaba Muhammadu Buhari shugabane Wanda kace ya karamana talauci wannan karya kake yi, domin talauci dane muka san cewa muna cikin talauci, domin bamu san ina muka dosa ba, domin dibar kudimmu ake ana raba muku, baka da kanti, baka da shago, baka da sana'a, ba yanda za'ayi kaso janar Muhammadu Buhari saboda yace kowa saidai ya ci guminsa.
A karshe dai yace, kamata yayi idan malamin siyasa zai yi ya fito yayi ta karara ya dena boye-boye.

#arewamini

Kaine la'ananne Ba Mu Ba - Inji Nura Hussain ya mayarwa da Dr. Ahmad Gumi martani

1. Tun Bashi Da Komi Na Aure Shi.
Amsa: Ke Me Kike Da Shi Sanda Kuka Yi Auren?
2. Ko Rigar Kirki Ba Shi Da Shi, Ni Nake Rufa Masa Asiri, Ba Shi Da Ko Sisi.
Amsa: Ke Kika Yi Masa Arzikin, Idan Ke Kika Yi Masa Karbe Abinki.
3. Namiji Ba Shi Da Amana!
Amsa: Karin Aure Ma Rashin Amana Ne? To A Faranta Maki A Sabawa Allah Kenan!
Rariya.

Ga Karatun Mata Idan Mijin Su Zai Kara Aure!!!

Wannan hoton wata tsohuwace tukuf dake karatun Qur'ani, hoton ya yadu a shafukan sada zumunta inda mutane da dama suka ta saka mata Albarka.

Tsufan Kirki

"idan kaga musulmi dan arewa me hankali yana zagin buhari to matsiyaci munafukine, da zaka tambyi mutum akan me yasa yake zagin buhari ? ze ce maka buhari ya kawo yunwa fatara da talauci to kawai ka samasa kaulasan domin baisan Allah ba bashi kuma tauhidi" a cewar malamin

Zagin Buhari Sifface Ta Munafurci - sheik kabiru Gombe