Wani faifan bidiyo da ya fito na tauraron fina-finan Hausa, Nura Hussain inda ya saka wani wa'azin malamin addinin Islama Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya caccaki shugaban kasa, Buhari da ma masu goyon bayanshi.
Anji malamin yana cewa yanzu dai shekara hudu sun tafi, babu abinda ya kara mana saidai talauci, du abinda kake da kadara ka sayar, shekara hudu ta tafi babu abinda suka karu sai yunwa da talauci da kara rarrabuwar mutane da kuma tsoro, to dayan biyu, in mun gayara yanzu ko muyi gyaran shekara takwas ko mu yi gyaaran shekara hudu. Fisabilillahi, barnar da muke ciki yanzu, muna bukatar shekara takwas ko muna bukatar shekara hudu mu gyara?
Malamin ya kara da cewa duk wanda ya jawo mana shekara hudu Allah ya la'aneshi.
Nura Hussain bayan yayi salati ga fiyayyen halitta yace, Ahmad Abubakar Gumi kamar yanda kace Allah ya la'anemu saboda muna yin Buhari to kaine Allah ya la'ana, kaine la'antacce a gurin Allah, ya kara da cewa, manzon Allah (S.A.W) ya ce mana. La'ana tana komawa wanda suka yi ta. Idan kayi la'ana wannan la'anar tana tashi sama sai ta duba taga kaine la'ananne ko kuwa wanda ka yi wa shine la'ananne? Sai ta fadawa wanda i dace, saboda haka la'antar zata koma gareka dan baka da hujjar la'anar mu.
Ya kara da cewa, mun mun yarda da cewa shugaba Muhammadu Buhari shugabane Wanda kace ya karamana talauci wannan karya kake yi, domin talauci dane muka san cewa muna cikin talauci, domin bamu san ina muka dosa ba, domin dibar kudimmu ake ana raba muku, baka da kanti, baka da shago, baka da sana'a, ba yanda za'ayi kaso janar Muhammadu Buhari saboda yace kowa saidai ya ci guminsa.
A karshe dai yace, kamata yayi idan malamin siyasa zai yi ya fito yayi ta karara ya dena boye-boye.

#arewamini

Kaine la'ananne Ba Mu Ba - Inji Nura Hussain ya mayarwa da Dr. Ahmad Gumi martani

1 comment:

  1. Mudai bamuda abin cewa

    Amma dai duk wanda yayi da kyau zaiga dakyau

    ReplyDelete