WACECE MACE TA GARI? //5
ITACE MAI NEMAN ILIMI
Ilimi da aiki dashi shima yana daga cikin matakin farko ga dukkan macen da take son zama ta gari. Ya zama dole ta yi aiki da hadisin Manzon Allah (SAW) cewa: "Neman ilimi wajibi ne akan dukkan musulmi da musulma". Wannan yana nuna babba da yaro, mace ko namiji, tsoho da matashi.
Duk macen da ba ta da ilimi kuma bata neman sa to hakika zaman ta na gari zayyi mata wahala. Saboda bata da fitilar da zai rinqa haska mata hanyar ta (rayuwarta).
Kuma kada ki ce wai kin yi sauka shikenan kin bar neman ilimi a'a ki cigaba da zuwa in da za a  rinqa tunatar dake Allah, In da za a koya miki hanyoyin shiga Aljannah, in da za'a rinqa koya miki zamantakewar magabata don ke ma ki yi koyi dasu. In da za a koya miki yanda zaki tarbiyyantar da 'ya'yanki.
Kin ga in a gida kike dukkan wainnan garabasar zasu rinqa wuce ki, kuma a hankali sai shaidan yayi galaba a kanki ki zama kamar ba ke ce mahaddaciyar nan ba mai bin Allah.
Sannan shi ilimi kogi ne yana dayawa, cigaba da nema shine zai sanya miki son addini da son ibada, kuma za'a rinqa miki wa'azi a hankali kina gyara halin ki.
Da sauraren wa'azin malaman Sunnah, ko a radio ko a TV kada dai ki zauna baki da wata kafa da zata rinqa koyar dake addini.
Da koyan Qur'ani da karanta shi domin samun lada da koran shaidanu a gidan auren ki.
Sannan uwa uba ilimi zai taimaka ma 'ya'yanki, domin zaki taya su tilawa a gida, zaki musu assignment. Kin ga kuwa dole mace ta gari ta nemi ilimi.
Ba na addini kadai ba har da na zamani, don ki san me duniya take ciki, saboda idan kina tunani ta bangare daya zai iya kawo naqasu ga 'ya'yanki.
Yar'uwar ku Sadeeya Lawal Abubaka

No comments