Wani Shaihun malami, Farfesa Adegboyega Fawole na asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin, UITH ya gargadi al’umma da su guji dabi’ar nan ta tsotsar al’aura a yayin jima’i, abinda Farfesan ya ce ya haddasa samuwar wata cuta mai suna Human Papiloma virus (HPV) a makoshin mutane jinsin maza da mata da dama
Farfesa Fawole wanda kwararre ne a bangaren mata da a turance a ke kira da Gynaecology, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai jiya a Ilorin cewa cutar HPV cuta ce da ake daukarta ta hanyar jima’i
Kwayar cutar ta bayiros na haddasa nau’o’in cutar daji da dama da ya hada da cutar dajin dubura, da ta al’aura da dai sauransu
Duk da cewa cutar ta HPV cuta ce da za a iya daukarta ta hanyar yin jima’i da wanda ke dauke da kwayar cutar, amma ana kamuwa da cutar sosai ta hanyar tsotsar al’aura a yayin saduwa
A saboda haka ne ma Farfesa Fawole ya ke jan hankalin masu aikata wannan dabi’ar da cewa, yiwuwar kamuwarsu da cutar HPV yafi yawa sama da wadanda ba sa wannan ta’ada
Sai dai Farfesa ya kara da cewa babu laifi ga lafiyayyun mace da mijinta da suka tsaya kawai akan junansu su gabatar da tsotse-tsotsen tunda babu wata barazana ta kasancewar akwai wani ko wata a tsakani da zai iya yada cutar a tsakaninsu
Farfesan ya yi kira ga ma’aurata da su ke zuwa bincikar lafiyarsu daga lokaci zuwa lokaci don tabbatar da lafiayarsu da ta abokan zamansu.

Tsotsar Al’aura A Yayin Jima’i Na Da Matukar Illa Ga Lafiya- Inji Wani Likita

No comments