Showing posts with label labaran duniya. Show all posts
Showing posts with label labaran duniya. Show all posts
Kasar Amurka za ta ba mutumin da ya ba ta bayanai game da daya daga cikin 'ya'yan marigayi Osama Bin Laden kyautar dala miliyan daya (kimamin naira miliyan 360 ke nan).
Hamza Bin Laden wanda ake nema ruwa a jallo shi ne shugaban wata kungiyar masu kaifin kishin Islama ta al-Qaeda, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Ana zaton yana rayuwa ne a kusa da iyakar kasar Afghanistan da Pakistan.
A 'yan shekarun nan, ya saki wani faifan murya da bidiyo inda yake kiran mabiyansa da su kai wa kasar Amurka da sauran kasashen yamma hari a wani martani ga kisan mahaifinsa.
A shekarar 2011, wasu dakaru musamman suka kashe Osama Bin Laden a wani gida dake garin Abbottabad a kasar Pakistan.
Marigayin ne ya kitsa kai harin ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001, inda akalla mutane kimanin 3,000 suka rasa ransu a Amurka.
A ranar Juma'a, ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta sanar da soke kasancewar Hamza Bin Laden zama dan kasarta.
A watan Maris din shekarar 2018, ya bayyana a wani faifan bidiyo, inda ya bukaci 'yan Saudiyya da su kaddamar da jahadi a kan masarautar kasar.
BBChausa.

Kasar Amurka na neman dan Osama ruwa a jallo>Htdl

Shugaban jam'iyyar PDP,Uche Secondus ya bayyanawa manema labarai cewa ganawar da suka yi da kwamitin sulhu ba su bayar da wani sharadi ba, sun dai fadi matsalolinsu ne kan zaben da aka gudanar a makon daya gabata, amma masu yi musu fassara su sani cewa ba bukata bace suka bayar ba kuma sharadi bane.
Uche yace su fa tuni sun riga sun yanke shawarar zuwa kotu, kuma ko da kwamitin sulhun basu so su zauna da su ba amma saboda irin mutanen da ya kunsa masu mutunci shiyasa ma suka yadda suka zauna dasu.
Yace da aka yi zaman, tambayarsu akayi me nene matsalolinsu da zaben da suka ce basu yadda dashi ba? Suka kuma zayyana su kuma hakan ba wai zai hanasu zuwan kotun da suka yi niyyar yi bane.
Ya kara da cewa, sun bayyana karara cewa, idan ba gyara rashin gaskiyar da ya faru aka yi ba to ba maganar zaman lafiya, ai sai idan an warware rashin gaskiyar da aka kullane sannan za'a zauna a yi maganar zaman lafiya.
Yace mun gaya musu yanda sojoji suka yi kaka gida a zaben suka yiwa gwamnatin tarayya yanda take so tare da hadin bakin INEC.
Akan maganar zuwa kotu kuwa, Secondus yace duk da masu sa ido daga kasashen Duniya daban-daban sun yaba da zaben, su suna da gamsasshiyar hujja da zasu gabatarwa da kotu cewa ba'ayi gaskiya a zaben ba.
Yace, masu saka idon sun fadi cewa zaben yayi kyaune saboda an musu barazanar kisa, su kuma suna so su koma kasashensu da rai, matsa musu aka yi suka ce zaben yayi kyau ba da son ransu ba injishi.
Yace su sunada hujjojin rashin kyan zaben da masu saka idanun da sauran mutane basu gani ba dan haka babu wanda ya isa ya hanasu zuwa kotu.
Yace an yi rashi gaskiya sosai kuma idan basi yi abinda ya kamata ba to ba'asan abinda zai faru nan gaba ba.

Kunji Abunda PDP Tace: Tunda babu gaskiya to ba maganar zaman lafiya: Dole muje kotu babu wanda ya isa ya hanamu>>HTDL

DA DUMIDUMINSA
Jami'an Tsaro Sun Cika Hannu Da Buba Galadima
Jami'an tsaro sun damke kakakin yakin neman zaben jam'iyyar PDP, Injinya Buba Galadima a yau Lahadi.
Majiyar ta DAILY NIGERIAN ta bayan cewa daya daga cikin 'ya'yan Buba Galadima ta tabbatarwa manema labarai cewa jami'an tsaro sun damke mahaifinta a unguwar Wuse 2 dake birnin tarayya Abuja.
Rariya

JAMI AN TSARO SUN DAMKE BUBA GALADIMA

Wata halitta da jama'a suke tunanin Aljani ne ya bayyana cikin suffar dattijo 'WAI' ya sauko daga sararin samaniya a kan keke, lokacin da ake taron Kwankwasiyya a karamar hukumar Birni.

Da mutane suka tambaye shi, me ya kawo ka? Sai yace "Nazo ne domin naga Kwankwaso"

#Sarauniya.

KALLI ALJANIN DA AKE TUNANIN YA HALARCI TARON KWANKWASIYYA

Ashe ba'a zuwa kasuwa da da tsaleliyar mace? karanta abinda ya faru da wannan da ya shiga kasuwa da antinshi
Wani ma'abocin shafin Twitter ya dauki hankulan mutane sosai bayan da ya bayar da labarin shigar kasuwar da yayi kasuwa tare da Antinshi, yace, na biya ta kasuwa da antina, sai tace, kai ya zaka kawoni nan? An gayama ana zuwa kasuwa da tsaliliyar mace.
Ya dauki hoton antin tashi tana zaune cikin mota yayin da wani me KekeNapep/ Adaidaita sahu ke kare mata kallo, hakan ya dauki hankulan mutane sosai.

Ashe ba'a zuwa kasuwa da da tsaleliyar mace? karanta abinda ya faru da wannan da ya shiga kasuwa da antinshi

A nan, dattijo mai shekaru 70, Alhaji Yakubu Nafsi- Nafsi ne wanda aka daura masa aure da yarinya 'yar shekara 15 a jihar Neja wanda rahotanni sun nuna cewa al'adarsa ke nan na auren kananan 'yan mata.

Yanda dan shekaru 70 ya aure 'yar shekaru 15


Cin amana abune me matukar bata rai da karya zuciyar wanda akawa, musamman idan cin amanar aurece ko kuma tsakanin masoya kuma ace da wanda baka tsammanine, hakane ta faru da wani magidanci inda ya kama kaninshi da matarshi turmi da tabarya.
Oleg Kirkunov dan kasar Rasha me shekaru 54 ya gayyaci dan uwanshi, Evgeny me shekaru 65 gidanshi inda suka ci abincin dare aka yi zumunci, saboda dare yayi sai dan uwan me gidan yace zai kwana kamin da safe ya wuce, kamar yanda The Sun UK ta ruwaito.
Tsakar dare Oleg ya irin juya dinnan sai baiga matarshi kusa dashi ba, sai ya tashi ya tafi nemanta, yana tsakar gida sai ya jiyo motsi/nishi a wani daki, ya karasa, ai kuwa sai yaga abinda bai yi tsammani ba, matarshi ce da dan uwanshi suke lalata.
Dama mafaraucine, sai kawai ya dauko bindigarshi ta farauta ya kakkabe, ya dirkawa matarshi harsashi a kai, dan uwan nashima da yaga haka sai yayi sauri ya saka kaya dan ya tsere, aikuwa shima be barshi ba, ya dirka mishi harsashi, nan duk su biyun suka fafi a mace.
Oleg na gama harbe su sai ya dauki waya ya kira 'yan sanda yace musu ga abinda ya aikata, nan aka zo aka tafi dashi.
Rahotanni sun bayyana cewa, za'a ajiyeshi nan zuwa watan Janairu kamin a gama bincike dan yanke mai hukunci.
Saidai wani abin ban mamaki da ya faru shine, mutane da dama a shafukan sadarwa na yanar gizo sun jinjinawa magidancin da wannan kisan da yawa matarshi da dan uwanshi inda suka rika kiranshi da gwarzo.
Wasu ma sunce ko da sune abinda zasu aikata kenan, basu damu da zaman gidan yari ba.

Magidanci ya bindige matarshi da dan uwanshi daya kama suna lalata har lahira