Shugaban jam'iyyar PDP,Uche Secondus ya bayyanawa manema labarai cewa ganawar da suka yi da kwamitin sulhu ba su bayar da wani sharadi ba, sun dai fadi matsalolinsu ne kan zaben da aka gudanar a makon daya gabata, amma masu yi musu fassara su sani cewa ba bukata bace suka bayar ba kuma sharadi bane.
Uche yace su fa tuni sun riga sun yanke shawarar zuwa kotu, kuma ko da kwamitin sulhun basu so su zauna da su ba amma saboda irin mutanen da ya kunsa masu mutunci shiyasa ma suka yadda suka zauna dasu.
Yace da aka yi zaman, tambayarsu akayi me nene matsalolinsu da zaben da suka ce basu yadda dashi ba? Suka kuma zayyana su kuma hakan ba wai zai hanasu zuwan kotun da suka yi niyyar yi bane.
Ya kara da cewa, sun bayyana karara cewa, idan ba gyara rashin gaskiyar da ya faru aka yi ba to ba maganar zaman lafiya, ai sai idan an warware rashin gaskiyar da aka kullane sannan za'a zauna a yi maganar zaman lafiya.
Yace mun gaya musu yanda sojoji suka yi kaka gida a zaben suka yiwa gwamnatin tarayya yanda take so tare da hadin bakin INEC.
Akan maganar zuwa kotu kuwa, Secondus yace duk da masu sa ido daga kasashen Duniya daban-daban sun yaba da zaben, su suna da gamsasshiyar hujja da zasu gabatarwa da kotu cewa ba'ayi gaskiya a zaben ba.
Yace, masu saka idon sun fadi cewa zaben yayi kyaune saboda an musu barazanar kisa, su kuma suna so su koma kasashensu da rai, matsa musu aka yi suka ce zaben yayi kyau ba da son ransu ba injishi.
Yace su sunada hujjojin rashin kyan zaben da masu saka idanun da sauran mutane basu gani ba dan haka babu wanda ya isa ya hanasu zuwa kotu.
Yace an yi rashi gaskiya sosai kuma idan basi yi abinda ya kamata ba to ba'asan abinda zai faru nan gaba ba.

Kunji Abunda PDP Tace: Tunda babu gaskiya to ba maganar zaman lafiya: Dole muje kotu babu wanda ya isa ya hanamu>>HTDL

No comments