*TAMBAYOYI DARI (100) DA AMSA AKAN MATA:  HAILA, JININ BIKI, SALLAH, AZUMI DA HAJJI.*
Fitowa ta 1
Daga: *_Sheikh Muhammad Saleh al-Uthaimeen, Rahimahullah_*
*TAMBAYA TA 1*
Shin mace me jinin biki zata zauna har kwana arba'in ne ba zatayi sallah ba kuma ba zatayi azumi ba, ko kuma abin lura daga gareta za tayi tsarki, tayi sallah, kuma nawa ne mafi hawan kwanakin da za tayi kafin ta yi tsarki?
*AMSA:*
Mace mai jinin biki bata da kyayyadadden lokaci sai dai duk lokacin da jini ya zo mata zata zauna ba za tayi sallah ba kuma ba za tayi azumi ba kuma mijinta ba zai iya saduwa da ita ba. Amma idan taga jini ya dauke, wato ta tsarkaka ko da ko kafin ta cika kwana arba'in ne ko da jinin iyakacin  kwana goma ne kawai yayi ko kwana biyar kawai sai ya dauke, to sai tayi wanka tayi sallah, tayi azumi kuma mijinta ya sadu da ita babu laifi acikin hakan.
Sai dai abin da yafi muhimmanci shine shi jinin biki al'amari ne kebantacce kuma hukuncinsa yana ratayuwa ne da shi, wato idan jinin yazo to hukuncinsa yana nan ba za tayi sallah da azumi ba. Kuma idan jinin bai zo ba to hukhncinsa baya nan. Duk lokacin da tayi tsarki to ta wofanta daga hukuncinsa.
Sai dai idan jinin ya karu matar ta Zamo mai jinin istihada, wato jinin ciwo ke nan, sai tayi lissafin iya kwanakin al'adarta sai tayi wanka tayi sallah. Sai ta nemi maganin wannan jinin na cuta.
Muhadu a fitowa ta 2 in sha Allahu Ta'ala
✍Tattarawa:
Dan uwanku a Musulunci
*_Umar Shehu Zaria_*
Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

TAMBAYOYI DARI (100) DA AMSA AKAN MATA: HAILA, JININ BIKI, SALLAH, AZUMI DA HAJJI

No comments