TUSHEN KUSKURE A ADDININ MUSLUNCI SHI NE
KUSKUREN FAHIMTAR MA'ANAR KALMAR
SHAHADA
Abu ne sananne, Kalmar Shahada; "La'ilaha illal
lahu" ita ce tushen Addinin Muslunci. Gaba daya
Addinin Muslunci ya ginu ne a kan wannan tushe
da asali. Don haka babu yadda za ayi mutum ya
fahimci Addinin Muslunci bisa ingantacciyar
fahimta har sai ya fahimci wannar kalma a bisa
ingantacciyar fahimta.
Ma'anar wannar kalma; "La'ilaha illal lah" ita ce;
"Babu abin bauta bisa gaskiya da cancanta sai
Allah". Saboda Kalmar "ILAHU" ma'anarta ita ce;
"ABIN BAUTA". Allah ya ce:
ﻗﻞ ﻳﺎ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺗﻌﺎﻟﻮﺍ ﺇﻟﻰ ﻛﻠﻤﺔ ﺳﻮﺍﺀ ﺑﻴﻨﻨﺎ ﻭﺑﻴﻨﻜﻢ ﺃﻻ
ﻧﻌﺒﺪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﻧﺸﺮﻙ ﺑﻪ
ﺷﻴﺌﺎ ﻭﻻ ﻳﺘﺨﺬ ﺑﻌﻀﻨﺎ ﺑﻌﻀﺎ ﺃﺭﺑﺎﺑﺎ ﻣﻦ ﺩﻭﻥ ﺍﻟﻠﻪ
"Ka ce: ya ku Ahlul Kitabi; (Yahudawa da
Kiristoci), ku zo mu hadu a kan wata kalma da za
ta daidaita tsakaninmu da ku; KADA MU BAUTA
MA KOWA SAI ALLAH, KADA MU HADA SHI DA
KOMAI A CIKIN BAUTA, KUMA KADA SAHENMU
SU RIKI SASHE A MATSAYIN UBANGIJI KOMA
BAYAN ALLAH".
Ibnu Jarir Al- Dabariy (ra) ya ruwaito daga wasu
daga cikin Salaf cewa; kalmar da ake nufi a nan
ita ce: Kalmar Shahada; "La'ilaha illal lahu". Daga
cikinsu Abul Aliyah ya ce:
" ﻛﻠﻤﺔ ﺍﻟﺴﻮﺍﺀ : ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ "
Akwai ayoyi masu yawa da suke bayanin ma'anar
wannar kalma ta tushen Addini, daga ciki Allah ya
ce:
ﻭﺇﺫ ﻗﺎﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻷﺑﻴﻪ ﻭﻗﻮﻣﻪ ﺇﻧﻨﻲ ﺑﺮﺍﺀ ﻣﻤﺎ ﺗﻌﺒﺪﻭﻥ ‏( 26 ‏)
ﺇﻻ ﺍﻟﺬﻱ ﻓﻄﺮﻧﻲ ﻓﺈﻧﻪ ﺳﻴﻬﺪﻳﻦ ‏( 27 ‏) ﻭﺟﻌﻠﻬﺎ ﻛﻠﻤﺔ ﺑﺎﻗﻴﺔ ﻓﻲ
ﻋﻘﺒﻪ ﻟﻌﻠﻬﻢ ﻳﺮﺟﻌﻮﻥ ‏( 28 )
Ya ce:
ﻓﻤﻦ ﻳﻜﻔﺮ ﺑﺎﻟﻄﺎﻏﻮﺕ ﻭﻳﺆﻣﻦ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻓﻘﺪ ﺍﺳﺘﻤﺴﻚ ﺑﺎﻟﻌﺮﻭﺓ
ﺍﻟﻮﺛﻘﻰ ﻻ ﺍﻧﻔﺼﺎﻡ ﻟﻬﺎ
Ya ce:
ﻭﻣﺎ ﺃﺭﺳﻠﻨﺎ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻚ ﻣﻦ ﺭﺳﻮﻝ ﺇﻻ ﻧﻮﺣﻲ ﺇﻟﻴﻪ ﺃﻧﻪ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ
ﺃﻧﺎ ﻓﺎﻋﺒﺪﻭﻥ
Ya ce:
ﻭﻣﺎ ﻟﻲ ﻻ ﺃﻋﺒﺪ ﺍﻟﺬﻱ ﻓﻄﺮﻧﻲ ﻭﺇﻟﻴﻪ ﺗﺮﺟﻌﻮﻥ ‏( 22 ‏) ﺃﺃﺗﺨﺬ
ﻣﻦ ﺩﻭﻧﻪ ﺁﻟﻬﺔ
Ya ce:
ﻭﻣﺎ ﺃﻣﺮﻭﺍ ﺇﻻ ﻟﻴﻌﺒﺪﻭﺍ ﺇﻟﻬﺎ ﻭﺍﺣﺪﺍ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﻫﻮ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ ﻋﻤﺎ
ﻳﺸﺮﻛﻮﻥ
Duka wadannan ayoyin suna tabbatar da cewa;
ma'anar "ILAHU" ita ce: ABIN BAUTA.
Kai hatta Mushrikan Larabawa sun fahimci
ma'anar Kalmar shahada a bisa ma'ana ta
hakika, Allah ya ce:
ﺇﻧﻬﻢ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﺇﺫﺍ ﻗﻴﻞ ﻟﻬﻢ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺴﺘﻜﺒﺮﻭﻥ ‏( 35 ‏)
ﻭﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﺃﺋﻨﺎ ﻟﺘﺎﺭﻛﻮﺍ ﺁﻟﻬﺘﻨﺎ ﻟﺸﺎﻋﺮ ﻣﺠﻨﻮﻥ ‏( 36 )
Shi ya sa lokacin da Annabi (saw) ya nemi su
yarda da Kalmar "La'ilaha illal lahu", su bauta ma
Allah shi kadai sai suka ce:
ﺃﺟﻌﻞ ﺍﻵﻟﻬﺔ ﺇﻟﻬﺎ ﻭﺍﺣﺪﺍ ﺇﻥ ﻫﺬﺍ ﻟﺸﻲﺀ ﻋﺠﺎﺏ ‏( 5 ‏) ﻭﺍﻧﻄﻠﻖ
ﺍﻟﻤﻸ ﻣﻨﻬﻢ ﺃﻥ ﺍﻣﺸﻮﺍ ﻭﺍﺻﺒﺮﻭﺍ ﻋﻠﻰ ﺁﻟﻬﺘﻜﻢ ﺇﻥ ﻫﺬﺍ ﻟﺸﻲﺀ
ﻳﺮﺍﺩ ‏( 6 )
Don haka ma'anar wannar kalma; "La'ilaha illal
lahu" ita ce; "Babu abin bauta bisa gaskiya da
cancanta sai Allah". Saboda Allah ya ce:
ﺫﻟﻚ ﺑﺄﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻫﻮ ﺍﻟﺤﻖ ﻭﺃﻥ ﻣﺎ ﻳﺪﻋﻮﻥ ﻣﻦ ﺩﻭﻧﻪ ﻫﻮ ﺍﻟﺒﺎﻃﻞ
* Amma abin mamaki da yawa daga cikin
musulmai ba su fahimci ma'anar wannar kalma a
bisa ma'ana ta hakika ba. Ga nan kadan daga
cikin wadanda suka kuskure ma'ana ta hakika
game da Kalmar Shahada:
1. Sufaye masu Aqidar "Wahdatul Wujud", wato
Aqidar komai Allah ne, su suna fassara Kalmar
Shahadar ce da cewa: Babu wani abin bauta sai
Allah. Ma'ana; duk wani abin da ake bautawa
Allah ne. Wanda ya bauta ma gunki ma Allah ya
bauta, wanda ya bauta ma Shehu Inyas shi ma
wa Allah ya bauta. Wanda ya bauta wa Annabi
Isa (as) shi ma wa Allah ya bauta, wanda ya je
kabarin wani shehi ko waliyyi ya bauta masa shi
ma wa Allah ya bauta, saboda babu wani abin da
ake bautawa face Allah ne.
2. Ma'abota "Ilmul Kalam"; Mu'utazilawa,
Asha'ira, Maturidiyya da makamantansu. Suna
fassara Kalmar "ILAHU" da cewa;
ﺍﻟﻘﺎﺩﺭ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﺧﺘﺮﺍﻉ
Wai- mai iko a kan kirkiran halitta. Don haka
ma'anar "La'ilaha illal lahu" a wajensu, ita ce:
"Babu mai iko a kan kirkiran halitta sai Allah".
3. 'Yan Kungiyar Ikhwanul Muslimuna, su kuma
suna fassara Kalmar Shahadar ce da cewa; BABU
HUKUMA SAI TA ALLAH.
Sayyid Qutub a cikin Tafsirinsa "Fiy Zilalil Qur'an"
ya tabbatar da haka a wurare da dama, daga ciki
ya ce:
« ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ‏» ﻛﻤﺎ ﻛﺎﻥ ﻳﺪﺭﻛﻬﺎ ﺍﻟﻌﺮﺑﻲ ﺍﻟﻌﺎﺭﻑ ﺑﻤﺪﻟﻮﻻﺕ
ﻟﻐﺘﻪ : ﻻ ﺣﺎﻛﻤﻴﺔ ﺇﻻ ﻟﻠﻪ، ﻭﻻ ﺷﺮﻳﻌﺔ ﺇﻻ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻻ ﺳﻠﻄﺎﻥ
ﻷﺣﺪ ﻋﻠﻰ ﺃﺣﺪ، ﻷﻥ ﺍﻟﺴﻠﻄﺎﻥ ﻛﻠﻪ ﻟﻠﻪ .
Kuma du ya ce:
ﻭﻣﻌﻨﻰ : ‏« ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ‏» .. ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﺮﻓﻮﻥ ﺃﻥ ﺍﻷﻟﻮﻫﻴﺔ ﺗﻌﻨﻲ
ﺍﻟﺤﺎﻛﻤﻴﺔ ﺍﻟﻌﻠﻴﺎ
Ya ce:
ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ ﺃﻥ : ‏« ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ‏» ﺛﻮﺭﺓ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺴﻠﻄﺎﻥ
ﺍﻷﺭﺿﻲ
Ya ce:
ﺃﻥ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻫﻮ ﺃﻭﻻ ﺇﻗﺮﺍﺭ ﻋﻘﻴﺪﺓ : ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻤﺪﻟﻮﻟﻬﺎ
ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﻲ ﻭﻫﻮ ﺭﺩ ﺍﻟﺤﺎﻛﻤﻴﺔ ﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺃﻣﺮﻫﻢ ﻛﻠﻪ، ﻭﻃﺮﺩ
ﺍﻟﻤﻌﺘﺪﻳﻦ ﻋﻠﻰ ﺳﻠﻄﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﺎﺩﻋﺎﺀ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺤﻖ ﻷﻧﻔﺴﻬﻢ .
Ya ce:
ﻭﺷﻬﺎﺩﺓ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ، ﺃﻱ ﺇﻓﺮﺍﺩﻩ ﺑﺎﻟﺤﺎﻛﻤﻴﺔ ﻓﻲ ﺣﻴﺎﺗﻬﻢ
ﺍﻷﺭﺿﻴﺔ
Wannan ya sa suke ganin shirka a wajensu shi ne
shirkan siyasa, saboda Tauhidi shi ne Tauhidin
Hukuma. Wannan ya sa suke mutuwa a kan
kokarin kawar da gomnatin zalunci. Tun
kafuwarsu har zuwa yau a kan abin da suke ta
gwagwarmaya kenan, alhali Manzannin Allah da
Annabawa sun yi yaki ne a kan tabbatar da
Tauhidin Bautar Allah da kawar Shirka ma Allah a
cikin bauta.
** Abin lura shi ne:
Fahimtar hakikanin ma'anar Kalmar Shahada da
riko da ita, da tafiya a kanta, da aiki da ita, tare
da abin da take hukuntawa, shi ne asali da
tushen tafiya a kan hanya madaidaiciya, kuskure
a fahimtar ma'anar kalmar kuwa, shi ne asali da
tushe na kaucewa ga hanya madaidaiciya; hanyar
Annabawa da Siddiqai da Shahidai da Salihan
bayi.

TUSHEN KUSKURE A ADDININ MUSLUNCI SHI NE KUSKUREN FAHIMTAR MA'ANAR KALMAR SHAHADA DR. ALIYU MUHD SANI (HAFIZAHULLAH)

No comments