DALILIN DA YA SA KUNGIYAR IZALA TAKE DA
TSARIN SHUGABANCI
Abu ne sananne Allah ya wajabta mana hadin kai
a kan igiyarsa, ya wajabta haduwa a cikin
aiyukan Ibada da sauran aiyukan alheri, kamar
Da'awa zuwa ga Addininsa, wato kira zuwa ga
Tauhidi da bin Shari'arsa da Sunnar Manzonsa
(saw), da kuma aikin umurni da kyakkyawa da
hani ga mummuna, da sauran aiyuka na Shari'a
da aka shar'anta yinsu cikin Jama'a. Kuma ya
wajabta mana taimakekeniya a kan da'a da
aiyukan alheri na Maslahar rayuwa.
Duka wadannan aiyuka da muka ambata aiyuka
ne na haduwar jama'a, to don haka Shari'a ta
shiryar da mu zuwa ga samar da Shugabanci da
Jagoranci a cikinsu, saboda Maslahar al'ummar
Musulmai tana cikin tarayya da haduwarsu cikin
aiyukan alheri. Shi ya sa hatta a halin tafiya
Annabi (saw) ya yi umurni da nada shugaba inda
ya ce:
« ﺇﺫﺍ ﺧﺮﺝ ﺛﻼﺛﺔ ﻓﻲ ﺳﻔﺮ ﻓﻠﻴﺆﻣﺮﻭﺍ ﺃﺣﺪﻫﻢ ‏»
ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ‏( 3/ 36 )
{Idan mutum uku suka fita bulaguro to su nada
dayansu a matsayin shugabansu}.
Imamul Khattabiy yana sharhi sai ya ce:
ﺇﻧﻤﺎ ﺃﻣﺮ ﺑﺬﻟﻚ ﻟﻴﻜﻮﻥ ﺃﻣﺮﻫﻢ ﺟﻤﻴﻌﺎ ﻭﻻ ﻳﺘﻔﺮﻕ ﺑﻬﻢ ﺍﻟﺮﺃﻱ ﻭﻻ
ﻳﻘﻊ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﺧﻼﻑ ﻓﻴﻌﻨﺘﻮﺍ .
ﻣﻌﺎﻟﻢ ﺍﻟﺴﻨﻦ ‏( 2/ 260 261 - )
"Kawai Annabi (saw) ya yi umurni da hakan ne
don samun hadin kai, don kar ra'ayoyi ya raba
kansu, kuma don kar sabani ya afku a tsakaninsu
su watse".
Shaikhul Islami ya ce:
ﺍﻟﻨﺒﻲ - ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ - ﺩﺍﺋﻤﺎ ﻳﺄﻣﺮ ﺑﺈﻗﺎﻣﺔ ﺭﺃﺱ،
ﺣﺘﻰ ﺃﻣﺮ ﺑﺬﻟﻚ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻔﺮ ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﺛﻼﺛﺔ، ﻓﺄﻣﺮ ﺑﺎﻹﻣﺎﺭﺓ ﻓﻲ
ﺃﻗﻞ ﻋﺪﺩ ﻭﺃﻗﺼﺮ ﺍﺟﺘﻤﺎﻉ .
ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﻨﺒﻮﻳﺔ ‏( 557 1/ )
"A kullum Annabi (saw) yana umurni da samar da
shugaba a cikin haduwar jama'a, har sai da ya yi
umurni da haka idan mutum uku sun kasance a
halin tafiya, sai Annabi (saw) ya yi umurni da
shugabanci a mafi karancin adadi, kuma a mafi
gajartan haduwar jama'a".
Annabi (saw) yana umurni da hakan ne saboda
Maslahar Jama'a ba ta cika a same ta yadda ake
so sai karkashin jagoranci.
Shaikhul Islami ya ce:
ﺇﻥ ﺑﻨﻲ ﺁﺩﻡ ﻻ ﺗﺘﻢ ﻣﺼﻠﺤﺘﻬﻢ ﺇﻻ ﺑﺎﻻﺟﺘﻤﺎﻉ ﻟﺤﺎﺟﺔ ﺑﻌﻀﻬﻢ
ﺇﻟﻰ ﺑﻌﺾ ﻭﻻ ﺑﺪ ﻟﻬﻢ ﻋﻨﺪ ﺍﻻﺟﺘﻤﺎﻉ ﻣﻦ ﺭﺃﺱ ﺣﺘﻰ ﻗﺎﻝ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ { ﺇﺫﺍ ﺧﺮﺝ ﺛﻼﺛﺔ ﻓﻲ ﺳﻔﺮ
ﻓﻠﻴﺆﻣﺮﻭﺍ ﺃﺣﺪﻫﻢ }. ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ...
ﻓﺄﻭﺟﺐ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺗﺄﻣﻴﺮ ﺍﻟﻮﺍﺣﺪ ﻓﻲ ﺍﻻﺟﺘﻤﺎﻉ
ﺍﻟﻘﻠﻴﻞ ﺍﻟﻌﺎﺭﺽ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻔﺮ ﺗﻨﺒﻴﻬﺎ ﺑﺬﻟﻚ ﻋﻠﻰ ﺳﺎﺋﺮ ﺃﻧﻮﺍﻉ
ﺍﻻﺟﺘﻤﺎﻉ .
ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( 390 28/ )
"Lallai Maslahar 'Yan Adam ba ta cika sai sun
hadu a abu guda, saboda bukatar sashensu ga
sashe, kuma babu makawa in sun hadun sai an
samu shugaba, shi ya sa Annabi (saw) ya ce:

dayansu a matsayin shugabansu}. Abu Dawuda
ne ya ruwaito shi...
SAI ANNABI (SAW) YA WAJABTA SHUGABANTAR
DA MUTUM DAYA A CIKIN KARAMAR HADUWA
WACCE TA BIJIRO A HALIN TAFIYA, DON YA
FADAKAR A KAN WAJABCIN SAMAR DA
SHUGABANCI A SAURAN NAU'O'IN HADUWA".
Wannan shi yake nuna muhimmancin samar da
shugabanci ga Kungiyar Sunna da ta hada kan
Musulmai a kan Littafin Allah da Sunnar
Manzonsa (saw), kuma take Da'awa zuwa ga
Tauhidi da Sunna take yakar Shirka da Bidi'a,
kamar yadda lamarin yake a Kungiyar Izala a
Nigeria.
Amma shugabancin da ake nufi a nan ba BABBAN
SHUGABANCI irin na Shugaban Gomnati mai iko
ba ne, wanda ake wajabta wa kowa yi masa
Bai'a da da'a. Saboda wannan kam ya takaita ne
a kan shugaban gomnati mai karfi da iko, wanda
Allah da Manzonsa (saw) suka wajabta yi masa
da'a a kowane hali in ba a kan sabon Allah ba. A
irinsa ne Shaikhul Islami yake cewa:
ﺇﻥ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﻄﺎﻉ ﻫﻮ ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻟﻪ ﺳﻠﻄﺎﻥ، ﺳﻮﺍﺀ ﻛﺎﻥ
ﻋﺎﺩﻻ ﺃﻭ ﻇﺎﻟﻤﺎ .
ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﻨﺒﻮﻳﺔ ‏( 561 1/ )
"Lallai shugaban da ake yi masa da'a shi ne
wanda ya kasance yake da karfin iko sawa'un ya
kasance Adali ne ko Azzalumi".
Wannan shi yake banbanta tsakanin shugabancin
Kungiyar Sunna kamar Kungiyar Izala da
shugabancin Kungiyoyi masu wajabta Bai'a da
da'a wa shugabanninsu kamar yadda ake yi wa
shugaban gomnati, kamar yadda lamarin yake a
Kungiyar Ikhwan.
Kuma wannan shi yake nuna jahilcin 'Yan
Kungiyar Salafiyyun masu yi wa hukuncin Bidi'a
diban karan mahaukaciya suna jefa shi kan
Kungiyoyin Sunna jefawan kan mai uwa da wabi,
ba tare da lura da ilimi da basira ba.

DALILIN DA YA SA KUNGIYAR IZALA TAKE DA TSARIN SHUGABANCI DR. ALIYU MUHD SANI (HAFIZAHULLAH)

No comments