TAMBAYA DA AMSA A KAN KAMA SALMANUL
AUDAH
TAMBAYA:
"Menen gaskiyar kamun da ake cewa
qasar.saudiyya tayi wadannan malumma:
(1- An kama manya kuma fitattun malamai
akasar saudiyya shahararru gida da waje.
Malaman sune:
a- shaikh allamah sulaimanul audah da kuma
b- aud alqarny...)".
AMSA:
Lallai na ga ana ta yada labarin kama wadannan
mutane guda biyu, amma sai dai ban ji cikakken
bayani a kai ba. Amma ga Mulahazaat dina a
kansu kamar haka:
1- Wadannan ba Malamai ne da ake dauka a
matsayin manyan Malamai kamar yadda aka fada
ba, su dai ana daukarsu ne a matsayin "Du'aat"
masu wa'azi wadanda suka shahara, kuma masu
sukar Gomnati.
2- Sa'annan su wadannan mutane ana kirga su a
cikin masu goyon bayan Kungiyar Ikhwan ko
mabiya Manhajinta, kungiya da take fada da
Gomnatocin Kasashen Musulmai, alhali hakan ya
saba karantarwar Qur'ani da Sunnar Manzon
Allah (saw).
Allah ya ce:
{ ﻳَﺎﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺃَﻃِﻴﻌُﻮﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﺃَﻃِﻴﻌُﻮﺍ ﺍﻟﺮَّﺳُﻮﻝَ ﻭَﺃُﻭﻟِﻲ
ﺍﻟْﺄَﻣْﺮِ ﻣِﻨْﻜُﻢْ } ‏[ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : 59 ]
"Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi da'a ma
Allah, ku yi da'a wa Manzon Allah da masu
jagorancin lamura daga cikinku (Shugabanni)".
Annabi (saw) ya ce:
« ﺍﺳﻤﻌﻮﺍ ﻭﺃﻃﻴﻌﻮﺍ، ﻭﺇﻥ ﺍﺳﺘﻌﻤﻞ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻋﺒﺪ ﺣﺒﺸﻲ، ﻛﺄﻥ
ﺭﺃﺳﻪ ﺯﺑﻴﺒﺔ ‏»
ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 9/ 62 )
"Ku saurari shugabanni ku yi musu da'a, ko da
bawa Bahabashe aka nada muku, wanda kansa
yake kamar zabibi".
Kuma ya ce:
« ﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭﺍﻟﻄﺎﻋﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺮﺀ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﻴﻤﺎ ﺃﺣﺐ ﻭﻛﺮﻩ، ﻣﺎ ﻟﻢ
ﻳﺆﻣﺮ ﺑﻤﻌﺼﻴﺔ، ﻓﺈﺫﺍ ﺃﻣﺮ ﺑﻤﻌﺼﻴﺔ ﻓﻼ ﺳﻤﻊ ﻭﻻ ﻃﺎﻋﺔ ‏»
ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 9/ 63 ‏) ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ
‏( 1469 3/ )
"Saurara ma shugaba da yi masa da'a wajibi ne a
kan mutum Musulmi cikin abin da yake so ko
yake ki, matukar ba a umurce shi da sabo ba,
idan an umurce shi da sabo to ba saurara masa
kuma babu yi musa da'a".
Kuma ya ce:
« ﻋﻠﻴﻚ ﺍﻟﺴﻤﻊ ﻭﺍﻟﻄﺎﻋﺔ ﻓﻲ ﻋﺴﺮﻙ ﻭﻳﺴﺮﻙ، ﻭﻣﻨﺸﻄﻚ
ﻭﻣﻜﺮﻫﻚ، ﻭﺃﺛﺮﺓ ﻋﻠﻴﻚ ‏»
ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 1467 3/ )
"Wajibi ne ka saurari shugaba ka yi masa da'a a
halinka na tsanani da na sauki, da halinka na
nishadi da na kiyayya, da kuma halin fifita kansu
a kanka".
Kuma ya ce:
« ﻣﻦ ﺃﻃﺎﻋﻨﻲ ﻓﻘﺪ ﺃﻃﺎﻉ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻣﻦ ﻋﺼﺎﻧﻲ ﻓﻘﺪ ﻋﺼﻰ ﺍﻟﻠﻪ،
ﻭﻣﻦ ﻳﻄﻊ ﺍﻷﻣﻴﺮ ﻓﻘﺪ ﺃﻃﺎﻋﻨﻲ، ﻭﻣﻦ ﻳﻌﺺ ﺍﻷﻣﻴﺮ ﻓﻘﺪ
ﻋﺼﺎﻧﻲ، ﻭﺇﻧﻤﺎ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺟﻨﺔ ﻳﻘﺎﺗﻞ ﻣﻦ ﻭﺭﺍﺋﻪ ﻭﻳﺘﻘﻰ ﺑﻪ، ﻓﺈﻥ
ﺃﻣﺮ ﺑﺘﻘﻮﻯ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻋﺪﻝ، ﻓﺈﻥ ﻟﻪ ﺑﺬﻟﻚ ﺃﺟﺮﺍ ﻭﺇﻥ ﻗﺎﻝ ﺑﻐﻴﺮﻩ
ﻓﺈﻥ ﻋﻠﻴﻪ ﻣﻨﻪ ‏»
ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 4/ 50 ‏) ، ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 1466 3/ )
"Duk wanda ya yi mini da'a to ya yi da'a ma
Allah ne, wanda kuma ya saba mini to ya saba
ma Allah ne, duk wanda ya yi da'a ma shugaba
to ya yi mini da'a ne, wanda kuma ya saba ma
shugaba to ya saba mini ne. Lallai shugaba
garkuwa ne, a bayansa ake yaki kuma ake kariya
da shi, in ya yi umurni da jin tsoron Allah ya yi
adalci to lallai yana da lada a kan haka, in kuma
ya fadi sabanin haka to yana kansa".
3- Mutane ne da a kullum kokarinsu shi ne su
tunzura matasa su yi bore da tawaye wa
Gomnatin Saudiyya, wato Saudiyya ta shiga halin
da Misra, Libya, Yemen da Syria suka shiga na
yaki. Alhali Annabi (saw) ya ce:
« ﻣﻦ ﺃﺗﺎﻛﻢ ﻭﺃﻣﺮﻛﻢ ﺟﻤﻴﻊ ﻋﻠﻰ ﺭﺟﻞ ﻭﺍﺣﺪ، ﻳﺮﻳﺪ ﺃﻥ ﻳﺸﻖ
ﻋﺼﺎﻛﻢ، ﺃﻭ ﻳﻔﺮﻕ ﺟﻤﺎﻋﺘﻜﻢ، ﻓﺎﻗﺘﻠﻮﻩ ‏»
ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 1480 3/ )
"Duk wanda ya zo muku alhali lamarinku na
shugabanci yana hade karkashin mutum daya, ya
zo yana so ya tsaga sandarku (jagorancinku) ya
raba kanku to ku kashe shi".
Imamu Nawawiy ya ce:
ﻓﻴﻪ ﺍﻷﻣﺮ ﺑﻘﺘﺎﻝ ﻣﻦ ﺧﺮﺝ ﻋﻠﻰ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﻭ ﺃﺭﺍﺩ ﺗﻔﺮﻳﻖ ﻛﻠﻤﺔ
ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ ﻭﻳﻨﻬﻰ ﻋﻦ ﺫﻟﻚ ﻓﺈﻥ ﻟﻢ ﻳﻨﺘﻪ ﻗﻮﺗﻞ ﻭﺇﻥ
ﻟﻢ ﻳﻨﺪﻓﻊ ﺷﺮﻩ ﺇﻻ ﺑﻘﺘﻠﻪ ﻓﻘﺘﻞ
ﺷﺮﺡ ﺍﻟﻨﻮﻭﻱ ﻋﻠﻰ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 241 12/ )
"A cikin wannan Hadisi akwai umurni a kan yakar
wanda ya yi tawaye wa shugaba, ko kuma yake
so ya raba kan Musulmai da makamancin haka,
kuma Hadisin yana hani a kan haka, idan kuma
mutumin bai hanu ba to za a yake shi, kuma ko
da sharrinsa ba zai kau ba sai an kashe shi to a
kashe shi".
Saboda haka wajibi ne Gomnatin Saudiyya ta
dauki mataki a kansu ta hanyar kamawa da
tsarewa da dukkan matakai da za su kawo
karshen fitinarsu da sharrinsu.
4- Irin wadannan masu wa'azi suna da yawa,
masu kokarin tayar da fitina ta hanyar tunzura
talakawa musamman matasa su yi tawaye da
bore a kan Gomnati, daga nan kuma jami'an tsaro
su yi ta kashe mutane, har abin ya koma yakin
basasa kamar yadda yake faruwa a Libya, Yemen
da Syria a yau.
5- Gomnatin Saudiyya tsarin Shari'ar Muslunci
take bi, karkashin Bai'a ta Shari'a, amma abin
mamaki irin wadannan masu wa'azi mabiya
Kungiyar Ikhwan Bai'arsu ga Murshidin Kungiyar
Ikhwan ne a maimakon Bai'a ga Shugaban
Saudiyya. Alhali hakan ya saba ma Shari'a,
mutum in ya mutu a kan haka ya yi mutuwar
Jahiliyya.
Annabi (saw) ya ce:
« ﻣﻦ ﺧﻠﻊ ﻳﺪﺍ ﻣﻦ ﻃﺎﻋﺔ، ﻟﻘﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﻻ ﺣﺠﺔ ﻟﻪ،
ﻭﻣﻦ ﻣﺎﺕ ﻭﻟﻴﺲ ﻓﻲ ﻋﻨﻘﻪ ﺑﻴﻌﺔ، ﻣﺎﺕ ﻣﻴﺘﺔ ﺟﺎﻫﻠﻴﺔ ‏»
ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 1478 3/ )
"Duk wanda ya cire hanunsa daga da'a ma
shugaba to zai hadu da Allah a Ranar Qiyama ba
shi da wata hujja, kuma duk wanda ya mutu
alhali babu bai'a ta shugaba a wuyansa to ya
mutu mutuwar jahiliyya".
Kuma ya ce:
« ﻣﻦ ﻛﺮﻩ ﻣﻦ ﺃﻣﻴﺮﻩ ﺷﻴﺌﺎ، ﻓﻠﻴﺼﺒﺮ ﻋﻠﻴﻪ، ﻓﺈﻧﻪ ﻟﻴﺲ ﺃﺣﺪ ﻣﻦ
ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺧﺮﺝ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻠﻄﺎﻥ ﺷﺒﺮﺍ، ﻓﻤﺎﺕ ﻋﻠﻴﻪ، ﺇﻻ ﻣﺎﺕ ﻣﻴﺘﺔ
ﺟﺎﻫﻠﻴﺔ ‏»
ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 1478 3/ )
"Duk wanda ya kyamaci wani abu daga
shugabansa to ya yi hakuri, saboda babu wani a
cikin mutane da zai fita daga karkashin biyayyar
shugaba gwargwadon taki daya kuma ya mutu
face ya yi mutuwar jahiliyya".
Kuma ya ce:
« ﺧﻴﺎﺭ ﺃﺋﻤﺘﻜﻢ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺗﺤﺒﻮﻧﻬﻢ ﻭﻳﺤﺒﻮﻧﻜﻢ، ﻭﻳﺼﻠﻮﻥ ﻋﻠﻴﻜﻢ
ﻭﺗﺼﻠﻮﻥ ﻋﻠﻴﻬﻢ، ﻭﺷﺮﺍﺭ ﺃﺋﻤﺘﻜﻢ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺗﺒﻐﻀﻮﻧﻬﻢ
ﻭﻳﺒﻐﻀﻮﻧﻜﻢ، ﻭﺗﻠﻌﻨﻮﻧﻬﻢ ﻭﻳﻠﻌﻨﻮﻧﻜﻢ ‏» ، ﻗﻴﻞ : ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ،
ﺃﻓﻼ ﻧﻨﺎﺑﺬﻫﻢ ﺑﺎﻟﺴﻴﻒ؟ ﻓﻘﺎﻝ : ‏« ﻻ، ﻣﺎ ﺃﻗﺎﻣﻮﺍ ﻓﻴﻜﻢ ﺍﻟﺼﻼﺓ،
ﻭﺇﺫﺍ ﺭﺃﻳﺘﻢ ﻣﻦ ﻭﻻﺗﻜﻢ ﺷﻴﺌﺎ ﺗﻜﺮﻫﻮﻧﻪ، ﻓﺎﻛﺮﻫﻮﺍ ﻋﻤﻠﻪ، ﻭﻻ
ﺗﻨﺰﻋﻮﺍ ﻳﺪﺍ ﻣﻦ ﻃﺎﻋﺔ ‏»
ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ‏( 1481 3/ )
"Mafifitan shugabanninku su ne wadanda kuke
sonsu kuma suke sonku, suke yi muku addu'a
kuke yi musu addu'a, mafi sharrin shugabanninku
su ne wadanda kuke kinsu suke kinku, kuke tsine
musu suke tsine muku".
Sai aka ce: Ya Manzon Allah, shin ba za mu yi
musu tawaye da makami ba?
Sai ya ce: "A'a, kar ku yake su matukar sun
tsayar da Sallah a cikinku, idan kun ga abin da
kuke ki daga shugabanninku to ku ki aikin nasa,
amma kar ku cire hanu daga yi masa da'a".
To amma su irin wadannan mutane a kullum suna
jayayya da shugabanni, suna kokarin yakarsu.
6- Shi wancan Salmanul Audan a lokacin da ake
rikicin Misra ya fitar da wasu tambayoyi a kan
Hukumar Saudiyya don ya tunzura matasa,
wadanda ya kira su da sunan:
ﺃﺳﺌﻠﺔ ﺍﻟﺜﻮﺭﺓ
To amma Alhamdu lillah, sai Allah ya mayar da
kaidinsa kansa, har yanzu kasar Saudiyya tana
zaune cikin aminci da zaman lafiya.
Allah ya yi mana tsari da fitina da malamanta.

TAMBAYA DA AMSA A KAN KAMA SALMANUL AUDAH DR. ALIYU MUHD SANI (HAFIZAHULLAH)

No comments