((MAN KUNTU MAULAAHU FA ALIYYUN
MALAAHU))
(( ﻣﻦ ﻛﻨﺖ ﻣﻮﻻﻩ ﻓﻌﻠﻲ ﻣﻮﻻﻩ ((
‏( 1 ). Yana daga cikin abin da ke ba wa
mahankalta mamaki: Irin yadda 'Yan Shi'ah ke
gina addininsu a lokuta da dama a kan tsabar
jahilci da son zuciya; daya daga cikin misalan
hakan shi ne: Irin yadda su 'Yan Shi'ah suka riki
ranar goma sha takwas ga watan Zul Hijjah a
matsayin Idin da ake samun lada ta hanyar yin
bukukuwa a cikinsa; a cewarsu saboda a wannan
rana ce Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi
huduba a hanyarsa ta dawowa daga aikin hajjin
bankwana zuwa gida Madina ya yi wani jawabi a
wani guri da ake kira "Gadeer Khamm" ya ce a
cikin jawabin nasa: ((Man kuntu maulaahu fa
Aliyyun maulaahu)). Ma'anar wannan maga shi
ne: "Duk wanda nakasance maulansa to Aliyyu
ma maulansa ne".
Sai 'Yan Shi'ah suka nuna jahilci da son zuciya
suka ce: da wannan lafazi da Annabi mai tsira da
amincin Allah ya yi ke nan ya shaida wa Duniya
ne cewa: da zarar ya mutu to Aliyyu Bin Abi Dalib
ne khalifan Musulmai bayan mutuwarsa! Wannan
shi ne jahilci da son zuciya da 'Yan Shi'ah suka
nuna; domin dukkan masana harshen Larabci, da
kuma masana Alkur'ani da Sunnah suna sane da
cewa: Ma'anar "Maulaa" a nan shi ne "Waliyyi"
watau masoyi. Ma'anar wannan magana ta
Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne: "Wanda
duk na kasance masoyinsa ne to Aliyyu ma
masoyinsa ne".
Ga misalai daga Alkur'ani mai girma:-
1. Ayah ta 4 cikin Suratut Tahreem Allah Ya ce:-
{ ﻭﺍﻥ ﺗﻈﺎﻫﺮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻓﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻫﻮ ﻣﻮﻻﻩ ﻭﺟﺒﺮﻳﻞ ﻭﺻﺎﻟﺢ
ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ }.
Ma'ana: ((In kuka nemi taimakon juna domin
kuntata masa, hakika Allah Shi maulansa (watau
masoyinsa) da kuma Jibirilu, da saalihin
Muminai)).
A nan babu wani mai hankali da zai ce: Mala'ikah
Jibrilu da saalihin Muminai su ne shugabannin
Annabi mai tsira da amincin Allah, a'a sai dai ya
ce: su masoyansa ne.
2. Ayah ta 40 cikin suratul Anfal Allah Ya ce:-
{ ﻭﺍﻥ ﺗﻮﻟﻮﺍ ﻓﺎﻋﻠﻤﻮﺍ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻮﻻﻛﻢ ﻓﻨﻌﻢ ﺍﻟﻤﻮﻟﻰ ﻭﻧﻌﻢ
ﺍﻟﻨﺼﻴﺮ }.
Ma'ana: ((Idan suka juya baya, to ku sani lalle
Allah ne maulanku (masoyinku), kuma madallan
Maulaa (Masoyi), kuma madallan Mataimaki)).
3. Ayah ta 78 cikin suratul Hajj Allah Ya ce:-
{ ﻭﺍﻋﺘﺼﻤﻮﺍ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻫﻮ ﻣﻮﻻﻛﻢ ﻓﻨﻌﻢ ﺍﻟﻤﻮﻟﻰ ﻭﻧﻌﻢ ﺍﻟﻨﺼﻴﺮ }.
Ma'ana: ((Ku yi riko da Allah Shi ne Maulanku
(masoyinku), kuma madallan Maulaa (Masoyin),
kuma madallan Mataimakin)).
4. Ayah ta 11 cikin suratu Muhammad Allah Ya
ce:-
{ ﺫﻟﻚ ﺑﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻮﻟﻰ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻭﺍﻥ ﺍﻟﻜﺎﻓﺮﻳﻦ ﻻ ﻣﻮﻟﻰ
ﻟﻬﻢ }.
Ma'ana: ((Saboda hakika Allah Shi ne Maulan
(masoyin) wadannan da suka yi Imani, hakika
Kafurai ba Maulaa (masoyi) gare su)).
5. Ayah ta 13 cikin suratul Hajj Allah Ya ce:-
{ ﻳﺪﻋﻮ ﻟﻤﻦ ﺿﺮﻩ ﺍﻗﺮﺏ ﻣﻦ ﻧﻔﻌﻪ ﻟﺐﺀﺱ ﺍﻟﻤﻮﻟﻰ ﻭﻟﺐﺀﺱ
ﺍﻟﻌﺸﻴﺮ }.
Ma'ana: ((Yana kiran wanda cutawarsa ta fi
zama kusa a kan anfanawarsa, tir din wannan
Maulaa (masoyin), tir din wannan Abokin)).
6. Ayah ta 157 cikin suratul Baqrah Allah Ya ce:-
{ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻟﻲ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻳﺨﺮﺟﻬﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻈﻠﻤﺎﺕ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻨﻮﺭ }.
Ma'ana: ((Allah masoyin wadannan da suka yi
Imani ne yana fitar da su daga duffai zuwa ga
haske)). Ma'anar lafazin "Waliyyu" a nan shi ne
ma'anar lafazin "Maulaa" a can.
7. Ayah ta 55 cikin suratul Maa'idah Allah Ya ce:-
{ ﺇﻧﻤﺎ ﻭﻟﻴﻜﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻘﻴﻤﻮﻥ
ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﻳﺆﺗﻮﻥ ﺍﻟﺰﻛﺎﺓ ﻭﻫﻢ ﺭﺍﻛﻌﻮﻥ }.
Ma'ana: ((Abin sani dai shi ne: Allah da
manzonSa da wadanda suka yi Imani watau
wadannan da suke tsaida Salla kuma suke ba da
Zakka suna masu rukuu'i su ne masoyanku)).
Ma'anar lafazin "Waliyyu" a nan shi ne ma'anar
lafazin "Maulaa" a can.
8. Ayah ta 62 cikin suratu Yunus Allah Ya ce:-
{ ﺍﻻ ﺍﻥ ﺃﻭﻟﻴﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﺧﻮﻑ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻭﻻ ﻫﻢ ﻳﺤﺰﻧﻮﻥ }.
Ma'ana: ((Ku saurara lalle masu son Allah babu
wani tsoro a kan su kuma ba sa yin bakin ciki)).
Ma'anar lafazin "Auliyaa'u" a nan shi ne ma'anar
lafazin "Maulaa" a can.
9. Ayah ta 34 cikin suratul Anfal Allah Ya ce:-
{ ﺍﻥ ﺃﻭﻟﻴﺎﺅﻩ ﺍﻻ ﺍﻟﻤﺘﻘﻮﻥ }.
Ma'ana: ((Babu masoya gare Shi sai masu
taqawa)). Ma'anar lafazin "Auliyaa'u" a nan shi
ne ma'anar lafazin "Maulaa" a can.
10. Ayah ta 71 cikin Suratut Taubah Allah Ya ce:-
{ ﻭﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥ ﻭﺍﻟﻤﺆﻣﻨﺎﺕ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﺃﻭﻟﻴﺎﺀ ﺑﻌﺾ }.
Ma'ana: ((Muminai maza da Muminai mata
sashinsu masoya ne ga sashi)). Ma'anar lafazin
"Auliyaa'u" a nan shi ne ma'anar lafazin
"Maulaa" a can.
11. Ayah ta 73 cikin suratul Anfal Allah ya ce:-
{ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﻛﻔﺮﻭﺍ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﺃﻭﻟﻴﺎﺀ ﺑﻌﺾ }.
Ma'ana: ((Wadannan da suka kafirta sashinsu
masoya ne ga sashi)). Ma'anar lafazin

12. Ayah ta 19 cikin suratul Jaathiyah Allah Ya
ce:-
{ ﻭﺍﻥ ﺍﻟﻈﺎﻟﻤﻴﻦ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﺃﻭﻟﻴﺎﺀ ﺑﻌﺾ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻭﻟﻲ ﺍﻟﻤﺘﻘﻴﻦ }.
Ma'ana: ((Lalle Azzalumai sashinsu masoya ne
ga sashi, Allah kuwa Masoyin Masu taqawa ne)).

Tabbas abin da wadannan nassoshi ke tabbatar
wa al'ummar duniya shi ne:-
- Allah Madaukakin Sarki Masoyin Muminai ne,
su ma Muminai masoyan Allah ne.
-Annabi mai tsira da amincin Allah masoyin
Muminai ne, su ma Muminai masoya Annabi ne.
- Aliyyu Dan Abi Taalib Allah Ya kara masa yarda
masoyin Muminai ne, su ma Muminai masoyan
shi ne.
- Dukkan Muminai masoya ne ga yan'uwa su
Muminai.
- Dukkan Kafurai masoya ne ga yan'uwa su
Kafurai.
(2). Wani abu da ya kamata a ce 'Yan Shi'ah sun
fahimta shi ne: da dai ma'anar lafazin "Maulaa"
shi ne ma'anar lafazin "Khilaafah", haka nan da
dai Annabi mai tsira da amincin Allah Khilaafanci
da Khaliifa ne yake nufi to da sai ya ce: ((Man
kuntu maulaahu, fa Aliyyun maulaahu ba'ada
mautii)). Watau duk wanda nake shugabantarsa
na mulki da Addini yanzu to Aliyyu shi ne
Khalifahna bayan mutuwata!! To amma Annabi
bai fadi haka ba, abin da kawai ya fada shi ne:
((Man kuntu mulaahu fa Aliyyun maulaahu)) kowa
kuwa ya san cewa Sayyidina Ali ba khalifah ba ne
a lokacin da Annabi yake raye, saboda babu
yadda za a yi a samu Khalifah sai dai idan shi
Annabi mai tsira da amincin Allah ba ya Duniya
tukuna. Allah Ya taimake mu ya raba mu da
sharrin Shaidan. Ameen.

((MAN KUNTU MAULAAHU FA ALIYYUN MALAAHU)) DR. IBRAHIM JALO JALINGO(HAFIZAHULLAH)

No comments