LALLE ABUBAKAR MAI YAWAN DARAJOJI NE A
GURIN ALLAH DA MANZONSA:
Sayyidina Abubakar Bin Abi Quhaafah Allah Ya
kara masa yarda Mutum ne mai yawan darajoji a
gurin Allah da manzonSa; ga ma wasu siffofi da
darajoji har guda biyar da manzon Allah mai tsira
da amincin Allah ya siffanta shi da su:-
1. Shi Abubakar Siddiqi ne; watau mai martabar
waliyyan Allah ta biyu ne bayan martabar farko
ta Annabci; kamar yadda Allah Ya jeranta
wadannan martabobi hudu na waliyyanSa a cikin
Suratun Nisaa'i aya ta 69 inda ya ce:-
(( ﻭﻣﻦ ﻳﻄﻊ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻓﺄﻭﻟﺌﻚ ﻣﻊ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﻧﻌﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻬﻢ
ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻭﺍﻟﺼﺪﻳﻘﻴﻦ ﻭﺍﻟﺸﻬﺪﺍﺀ ﻭﺍﻟﺼﺎﻟﺤﻴﻦ ﻭﺣﺴﻦ ﺃﻭﻟﺌﻚ
ﺭﻓﻴﻘﺎ )).
Ma'ana: ((Kuma wadannan da suka yi da'a ga
Allah da ManzonSa, to, wadannan suna tare da
wadanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga
Annabawa, da Siddiqai, da Shahidai, da Salihai.
Kuma wadannan sun kyautatu ga zama abokan
tafiya)).
2. Shi Abubakar shi ne mutumin da Annabi ya fi
son shi a cikin dukkan Mazaje.
3. Shi Abubakar mutum ne da Annabi ya ba da
umurnin a yi koyi da shi.
4. Shi Abubakar mutum ne da Allah Ya 'yanta shi
daga Wuta.
5. Shi Abubakar shi ne mutumin da yake
shugabantar dukkan manya majiya karfi in banda
Annabawa da Manzanni a cikin Aljannah.
Lalle banda wadannan darajoji biyar da muka
ambata yanzu, akwai wasu darajojin daban.
Ga hujjar wadannan darajoji biyar na Babban
Sahabi Abubakar da muka ambata daga
ingantattun hadithan manzon Allah mai tsira da
amincin Allah:-
(1). Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 3675, da Abu
Dawud Hadithi na 4653, da Tirmiziy Hadithi na
3697, da Nasaa'iy Hadithi na 8079, da Ahmad
Hadithi na 12127, da Ibnu Hibban Hadithi na
6865, da Bazzar Hadithi na 7094, da Dabaraaniy
Hadithi na 144, da Abu Ya'alaa Hadithi na 2910,
da Abdur Razzaq Hadithi na 20401 daga Sahabi
Uthman Bin Affan, da Sahabi Anas Bin Malik Allah
Ya kara musu yarda sun ce:-
(( ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺻﻌﺪ ﺍﺣﺪﺍ ﻭﺃﺑﻮ ﺑﻜﺮ ﻭﻋﻤﺮ
ﻭﻋﺜﻤﺎﻥ ﻓﺮﺟﻒ ﺑﻬﻢ، ﻓﻘﺎﻝ : ﺍﺛﺒﺖ ﺍﺣﺪ ﻓﺎﻧﻤﺎ ﻋﻠﻴﻚ ﻧﺒﻲ
ﻭﺻﺪﻳﻖ ﻭﺷﻬﻴﺪﺍﻥ )).
Ma'ana: ((Lalle Annabi mai tsira da amincin Allah
ya hau (dutsen) Uhudu tare da Abubakar da Umar
da Uthman, sai ya (dutsen) ya girgiza, sai ya ce:
Uhudu ka nitsu ba wasu ba ne a kanka in banda
wani Annabi, da wani Siddiqi, da wasu Shahidai
biyu)).
(2). Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 4379, ma
Muslim Hadithi na 2384, da Tirmiziy Hadithi na
3885, da Nasaa'iy Hadithi na 8052, da Ibnu
Majah Hadithi ne 101, da Ahmad Hadithi na
17844, da Hakim Hadithi na 6740, da Ibnu Hibban
Hadithi na 6885, da Dabaraaniy Hadithi na 18644,
da Baihaqiy Hadithi na 12879 daga Sahabi Anas
Bin Malik, da Sahabi Amr Bin A'as Allah Ya kara
musu yarda suka ce:-
(( ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺳﻴﻞ ﺍَﻱ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﺣﺐ
ﺇﻟﻴﻚ؟ ﻗﺎﻝ : ﻋﺎﻳﺸﺔ . ﻓﻘﻴﻞ ﻟﻪ : ﻣﻦ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ؟ ﻗﺎﻝ : ﺍﺑﻮﻫﺎ )).
Ma'ana: ((Lalle an tambayi Annabi mai tsira da
amincin Allah: wanene ne daga cikin mutane ya fi
soyuwa a gare ka? Sai ya ce: A'isha. Sai aka ce
da shi: daga cikin Maza fa? Sai ya ce:
Mahaifinta)).
(3). Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 3662, da
Ahmad Hadithi na 23293, da Hakim Hadithi na
4451, da Dabaraaniy Hadithi na 8344, da Bazzar
Hadithi na 2827, da Baihaqiy Hadithi na 10348
daga Sahabi Abdullahi Bin Mas'ud, da Sahabi
Huzaifah Allah Ya kara musu yarda sun ce:-
(( ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﺍﻗﺘﺪﻭﺍ ﺑﺎﻟﻠﺬﻳﻦ ﻣﻦ
ﺑﻌﺪﻱ ﺍﺑﻲ ﺑﻜﺮ ﻭﻋﻤﺮ )).
Ma'ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin
Allah ya ce: Ku yi koyi da Wadannan biyun a
bayana: Abubakar da Umar)).
(4). Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 3679, da
Hakim Hadithi na 3557, da Ibnu Hibban Hadithi
na 6864 daga Sahabiya uwar Muminai A'isha, da
Sahabi Az-Zubair Bin Awwam Allah Ya kara musu
yarda suka ce:-
(( ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ ﻻﺑﻲ ﺑﻜﺮ : ﺍﻧﺖ
ﻋﺘﻴﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺭ )).
Ma'ana: ((Lalle manzon Allah mai tsira da
amincin Allah ya ce wa Abubakar: Kai ne
'yantaccen Allah daga Wuta)).
(5). Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 3665, da Ibnu
Majah Hadithi na 95, da Ahmad Hadithi na 603,
da Ibnu Hibban Hadithi na 6904, da Bazzar
Hadithi na 490, da Dabaraaniy Hadithi na 17717,
da Abu Ya'alaa Hadithi na 624 daga Sahabi
Aliyyu Bin Dalib, da Sahabi Anas Bin Malik, da
Sahabi Abdullahi Bin Abbas Allah Ya kara musu
yarda sun ce:-
(( ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ : ﺍﺑﻮ ﺑﻜﺮ ﻭﻋﻤﺮ ﺳﻴﺪﺍ
ﻛﻬﻮﻝ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻣﻦ ﺍﻻﻭﻟﻴﻦ ﻭﺍﻻﺧﺮﻳﻦ ﺍﻻ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ
ﻭﺍﻟﻤﺮﺳﻠﻴﻦ )).

ya ce: Abubakar da Umar shugabanni ne na
manya majiya karfi na Aljannah tun na farkonsu
har na karshensu amma banda Annabawa da
Manzanni)).
Lalle wannan shi ne matsayin Sahabi Abubakar a
idanun Shari'ar Musulunci. Kuma lalle 'yan bidi'ar
da suka maida ginshikin addininsu shi ne zagin
shi da la'antar shi sun tabe. Allah Ya taimake mu
Ya raba mu da sharrin bidi'ah. Ameen.

No comments