TAWAKKALI GA ALLAH BA YA WADATARWA GA
BARIN AIKATA SABABI
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah (r) ya ce:
ﻣﻦ ﻇﻦ ﺃﻥ ﺍﻟﺘﻮﻛﻞ ﻳﻐﻨﻲ ﻋﻦ ﺍﻷﺳﺒﺎﺏ ﺍﻟﻤﺄﻣﻮﺭ ﺑﻬﺎ ﻓﻬﻮ
ﺿﺎﻝ ﻭﻫﺬﺍ ﻛﻤﻦ ﻇﻦ ﺃﻧﻪ ﻳﺘﻮﻛﻞ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻗﺪﺭ ﻋﻠﻴﻪ ﻣﻦ
ﺍﻟﺴﻌﺎﺩﺓ ﻭﺍﻟﺸﻘﺎﻭﺓ ﺑﺪﻭﻥ ﺃﻥ ﻳﻔﻌﻞ ﻣﺎ ﺃﻣﺮﻩ ﺍﻟﻠﻪ .
ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ( 528 8/ )
"Duk wanda ya yi zaton cewa; Tawakkali yana
wadatarwa ga barin aikata Sabuba da Shari'a ta
yi umurni da su to shi Batacce ne. Wannan ya
zama kamar wanda ya yi zaton cewa; zai yi
Tawakkali a kan abin da aka kaddara masa na
Sa'ada (shiga Aljanna) da Shakiyanci (shiga
wuta) ba tare da ya aikata abin da Allah ya
umurce shi da shi ba".
Manzon Allah (saw) ya ce:
« ﻣﺎ ﻣﻨﻜﻢ ﻣﻦ ﺃﺣﺪ ﺇﻻ ﻭﻗﺪ ﻛﺘﺐ ﻣﻘﻌﺪﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﺠﻨﺔ، ﻭﻣﻘﻌﺪﻩ
ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺭ » ﻗﺎﻟﻮﺍ : ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﺃﻓﻼ ﻧﺘﻜﻞ ﻋﻠﻰ ﻛﺘﺎﺑﻨﺎ، ﻭﻧﺪﻉ
ﺍﻟﻌﻤﻞ؟ ﻗﺎﻝ : « ﺍﻋﻤﻠﻮﺍ ﻓﻜﻞ ﻣﻴﺴﺮ ﻟﻤﺎ ﺧﻠﻖ ﻟﻪ » ﺛﻢ ﻗﺮﺃ : { ﻓﺄﻣﺎ
ﻣﻦ ﺃﻋﻄﻰ ﻭﺍﺗﻘﻰ ﻭﺻﺪﻕ ﺑﺎﻟﺤﺴﻨﻰ ﻓﺴﻨﻴﺴﺮﻩ ﻟﻠﻴﺴﺮﻯ }
[ ﺍﻟﻠﻴﻞ : 5 ] ﺇﻟﻰ ﻗﻮﻟﻪ { ﻓﺴﻨﻴﺴﺮﻩ ﻟﻠﻌﺴﺮﻯ } [ ﺍﻟﻠﻴﻞ : 10 ]
ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ
Abin lura:
1- Allah ya halicci dukkan abubuwa ne tare da
sabubansu.
2- Ana neman abubuwan da Allah ya kaddara wa
bawa ne ta hanyan aikata sabuba da Shari'a ta
sanyasu a matsayin sabuba na samun ababen da
bayi suke nema.
3- Kamar yadda ba za ka samu abin da Allah ya
kaddara maka na samun Sa'ada (shiga Aljanna)
tun kana cikin mahaifiyarka ko Shakiyanci (shiga
wuta) ba, har sai ka yi aikin Sa'adar (shiga
Aljannan), haka a neman arziki da abin duniya
ma, dole sai ka yi aiki da sababi na samun
arzikin, amma sababi da Shari'a ta zo da shi.
Kamar kasuwanci da noma da kiwo da sauran
hanyoyi na neman halal, wajen neman arziki da
abin duniya.
4- Sabuban samun abu sun kasu kashi biyu; -
sawa'un na samun abin duniya ne ko na lahira:
(a) Sabuba da Shari'a ta Shar'anta mana.
(b) Sabuba wadanda Shari'a ta yi hani a kansu.
Kashi na farko, in ka yi aiki da su da niyyar da'a
ma Allah, za ka samu lada, kuma insha Allahu za
ka samu biyan bukata.
Kashi na biyu, in ka yi aiki da su za ka samu
zunubi ko da kuwa ka samu biyan bukata.
Misalinsa shi ne; Mai neman arziki ta hanyar
sata ko fashi da makami, ko sata da biro, ko
zamba da ha'inci cikin cinikayya, ko da ka tara
dukiya, ka samu biyan bukata to kana da zunubi,
saboda Allah bai shar'anta wadannan sabuba da
ka samu arzikin ta hanyarsu ba.
Allah ya ba mu arziki mai albarka na halal, ya yi
mana afuwa a kan kurakurenmu.

No comments