ﺷﻴﺦ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ :
Yana bayani akan sirrin dake cikin Kalmar
shahada wato:
[ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ]
Da kuma Sirrin ISTIGHFARI wato:
{ ﺍﻹﺳﺘﻐﻔﺎﺭ }
Da kuma alaqar dake a tsakaninsu sai yake fada
game da fadin Allah Madaukakin Sarki:
﴿ ﻓَﺎﻋْﻠَﻢْ ﺃَﻧَّﻪُ ﻟَﺎ ﺇِﻟَٰﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻭَﺍﺳْﺘَﻐْﻔِﺮْ ﻟِﺬَﻧﺒِﻚَ ﻭَﻟِﻠْﻤُﺆْﻣِﻨِﻲﻥَ
ﻭَﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨَﺎﺕِ ۗ ﴾
(Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa
fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka,
"kuma sabõda mũminai maza da mũminai
mãtã").
Sai yace:
Lallai tabbatuwar Tauheedi yana kore dukkan
shirka gaba daya
Haka kuma yawaita Istighfari yana kore sauran
zunuban da ba shirkaba.
Mafi yabo da zikirin Allah shine fadar:
{ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ }
Kuma mafi girman Addua da neman gafarar
Allah,shine bawa yace:
[ ﺍﺳﺘﻐﻔﺮﺍﻟﻠﻪ ]
Allah ya umarcemu da Tauheed da kuma nemawa
kanmu gafara wato istighfari da kuma sauran yan
uwanmu masu imani baki daya.
ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ( 11/697 ) .
Ya Allah ka gafartawa dukkan musulman duniya
baki daya ka kuma tabbatar damu akan Tauheedi
da aqida mai kyau irinta Annabi s.a.w
No comments