WACECE MACE TA GARI? //3
ITA CE MUSULMA MU'UMINA
Farkon matakin zama ta gari shine ta kasance musulma. Musulma kuma ita ce wacce ta yi imani da Allah ta kadaita Sa a matsayin abun bautar ta, Kuma ta miqa wuya ga Allah ta hanyar miqa wuya ga umurninSa da dokokinSa.
Kuma ta yi imani da Annabi Muhammad ta hanyar yi masa da'a a umurninsa da gasgatasa a labaransa, da nisantar haninsa, da bautawa Allah kadai ta hanyar da ya shar'anta. Ta tsaida Sallah da haqqoqinta. Ta bada zakka, ta azumci watan Ramadana kuma ta je aikin hajji in ta samu iko. Wannan ce cikakkiyar musulma.
Sannan ta dauki matakin zama Mu'umina, shine imani da Allah da Mala'ikunsa, da Manzannin sa, da Litattafan sa, da Ranar qarshe, da imani da Qaddara mai kyau ko mara kyau.
Ba zaki taba zama ta gari ba har sai kin yi imani da wainnan abubuwan tun daga nan ne zaki fara ginin zama ta gari.
Don wata a dabi'un ta da halayen ta sai ka tambayi kanka anya kuwa wannan matar ta yi imani da waincan abubuwan da na ambata kuwa. Saboda gaba daya ta bar imanin ta da rukunan musulunci sun yi rauni. Kuma ta siyarwa shaidan da imanin ta, tana shirka da Allah tamkar bata yi imani da Shi a matsayin abun bautar ta ba.
Yar'uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar

No comments