Sabuwar tauraruwar masana’antar Kannywood tace zata koma makaranta kuma idan Allah yayi ta samu miji zata yi aure.
Sabuwar tauraruwar fina-finan hausan na Kannywood Maryam Yahaya ta bayanar cewa yin fim ba zai hanata yin karatu domin yin karatu yana cikin abubuwan dake gaban ta a rayuwa.
A wata hira ta musamman da tayi da BBC hausa, Maryam wanda ta kammala karatu ba da dadewa tace tana kokarin cigaba da yin karatu.
Jarumar shirin “Mansoor” tace idan Allah ya nufe ta da samun miji yanzu zata yi aure kuma zata cigaba da yin karatun ta.
Sabuwar tauraruwa wanda ta fara haskawa cikin “Mansoor” bayyana cewa idan tayi aure bazata cigaba da yin fim.
Maryam Yahaya ta shigo masana’antar kannywood da kafar dama domin bayan fitowar ta a cikin “Mansoor” ta samu damar fitowa a wasu shiri da dama.
Ko zamu iya cewa wannan matashiyar zata sauya jarumtakar manyan yan wasan masana’antar kamar su Rahama sadau, Nafisa Abdullahi, Halima Atete, Hadiza Gabon da dai sauransu?

Zan Koma Makaranta Kuma Idan Nasamu Miji Zanyi Aure – inji jaruma Maryam Yahaya

No comments