KIRA ZUWA GA TAFARKIN MAGABATA NA
QWARAI (Manhajus Salafis Salih). *** 015
MATSAYIN WANDA YA SABA WA TAFARKIN
MAGABATA NA QWARAI.
– Ci gaba
Idan mutum ya ce ba zai iya aiki da tafarkin
magabata ba sai ya yi tsani da fahimtar wani
malaminsa ko shaihinsa, to a nan sai a tambayi
dalilinsa. Har idan dalilinsa shi ne rashin samun
wata hujja daga Nassi ko maganganun
magabata, to sai a ce ya yi amfani da qiyasin
malamai ke nan saboda rashin dalilin Sharia daga
magabata. Idan kuma wadannan kafofi na asali
su ne ba su gamsar da shi ba, to bai wadatu da
maganganun manzon Allah (S.A.W.) ba ke nan.
Hakan kuwa yana nufin raayinsa ya wuce gaban
sunnah ta manzon Allah (S.A.W.) ke nan. Allah
(S.W.T.) kuma Ya ambaci wadanda suka zani bin
son rayukansu, ya ce: “To idan ba su karba daga
gareka ba, to ka sani cewa suna bin soye-soyen
zuciyarsu ne kawai, kuma wane ne ya fi bata da
wanda ya bi son zuciyarsa ba tare da wata
shiriya daga Allah ba. Lallai ne, Allah ba Ya
shiryar da mutane azzalumai. (Qasas:50).
Irin wadannan ma su ganin ba za su iya
gamsuwa da tafarkin magabata na qwarai ba sai
sun jingina da wata fahimta ta mazhaba ko wani
shaihin malami, ko wani imam na sufanci, ko
masu aiki da hankalinsu wajen ba da fatawar
addini, suna cikin hatsari babba, domin saba wa
tafarkin sahabban manzon Allah (S.A.W.) da
wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa.
Wasu suna ganin cewa ba za a iya fahimtar
addini kai tsaye ba har idan an ce za a tsaya a
kan asali, dole sai an yi riqo da ra'ayoyin
malaman da suka biyo baya. To babu laifi idan
muka yi riqo da bayanan wadannan malaman
matuqar bai yi karo da tafarkin magabata ba.
Idan an samu karo da juna kuwa, to tafarkin da
Annabi (S.A.W.) ya dora magabata a kai shi ne
tafarki madaidaici, saba wa hakan kuwa halaka
ce. Don Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa a cikin
Hadisi: “Na bar ku a kan wata turba tatacciya
kuma fara fat, darenta kamar ranarta ya ke, babu
mai kauce mata face halakakke.” (Hakim da Ibn
Majah suka ruwaito wannan Hadisin).
Masu ganin cewa za su iya zayyana wani salon
ibada wadda annabi (S.A.W.) bai bar magabata a
kanta ba, don qarin lada, to ga wata fatawa ta
Imam Malik dan Anas. Daga Zubairu dan Bakar
cewa wani mutum ya zo ga Imam Malik ya ce
masa, Ya kai dan bawan Allah, daga ina ka dauki
haraminka? Sai Imam Malik ya ce, Daga Zul-
Hulaifah daidai wurin da Manzon Allah ya yi
haraminsa. Sai shi mutumin ya ce masa: “Ni
kuwa ina son daukar haramina ne tun daga
masallacin Annabi." Imam Malik ya ce masa,
Kada ka yi haka. Sai mutumin ya ce ma sa ina
so in dau haramina a masallaci daidai kabarin
Manzon Allah. Imam Malik ya sake ce masa,
Kada ka yi hakan, domin ina tsorace maka wata
fitina. Sai mutumin ya amsa da cewa, Yin hakan
wace fitina zai jawo? Ai qarin bai fi na yan
milamilai ba. Imam Malik ya ce masa, Wace fitina
ce ta fi girma fiye da ganin da kake yi cewa za ka
wuce wuri mai falala wanda Manzon Allah
(S.A.W.) ya taqaita mu a kai? Ni na ji ayar Allah
da ke cewa: “Wadanda suke saba wa umarnin
(Manzon Allah) su ji tsoron kada wata fitina ta
same su ko wata azaba mai radadi ta riske su.”
Imam Shadibi ne ya kawo wannan bayani a cikin
littafinsa mai suna Aliitisam (juzui na farko shafi
na 123). Malamin ya qara da cewa wannan fitina
da Imam Malik ya ambata tana fassara ayar ce
game da bidia da irin qa'i'doji ko dalilan da suke
gina ayyukansu da suna yin qari ko ragi a addini
ba tare da umarnin Annabi (S.A.W.) ba.
Wannan ya nuna cewa tafarkin magabata ba ya
karbar wani abu da bai tabbata daga manzon
Allah (S.A.W.) ba sai idan babu ingantacciyar
magana a kan wannan masala. Muminan farko
sahabban manzon Allah (S.A.W.), sun kasance
suna barin ra'ayoyinsu da fahimtarsu wajen
hukunci da zarar sun ci karo da maganar manzon
Allah (S.A.W.). Wata rana Umar dan Khaddab ya
yanke hukunci a kan diyyar yatsu na hannu,
amma da hadisin manzon Allah (S.A.W.) ya riske
sahabbai wanda ya saba da hukuncin da Umar ya
gabatar, sai muminan farko suka ajiye maganar
Umar don (su nuna dogaro da komawa ga)
Hadisin Manzon Allah (S.A.W.) shi ne tabbatacce
kuma addini.

No comments