MA'ANAR SALAFIYYAH:
Ma'anar Salafiyyah shi ne: bin hanyar magabata;
watau Sahabbai, da Taabi'ai, da Taabi'ut
Taabi'iina, da Taabi'ut Taabi'it Taabi'iina wajen
girmama Annabi mai tsira da amincin Allah, da
barin maganar kowa a duk lokacin da ta yi karo
da maganarsa, da nuna fashi da damuwa a duk
lokacin da aka ga wani ya yi watsi da maganar;
Saboda wannan matsayi lalle shi ne matsayin
Sahabbai, da Taabi'ai, da Taabi'ut Taabi'iina, da
Taabi'ut Taabi'it Taabi'iina.
Ga misalai kadan na irin yadda Sahabbai suke
girmama maganar Annabi, suke bin maganarsa
sau-da-kafa, suke kuma nuna fushinsu a kan duk
wani da ya ki bin maganarsa ya koma yana bin
maganar waninsa:-
1. Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 3093, da
Muslim Hadithi na 1759 cewa babban Sahabi
Sayyidina Abubakar As-Siddiq ya ce:-
(( ﻟﺴﺖ ﺗﺎﺭﻛﺎ ﺷﻴﺌﺎ ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻳﻌﻤﻞ ﺑﻪ ﺍﻻ ﻋﻤﻠﺖ ﺑﻪ ﻓﺎﻧﻲ ﺍﺧﺸﻰ ﺍﻥ ﺗﺮﻛﺖ ﺷﻴﺌﺎ ﻣﻦ ﺃﻣﺮﻩ
ﺍﻥ ﺃﺯﻳﻎ )).
Ma'ana: ((Ni ba zan bar yin wani abu da manzon
Allah ya kasance yana yi ba face sai na yi shi,
lalle ni ina jin tsoron cewa in na bar wani abu na
umurninsa in karkata)).
2. Daaramiy ya ruwaito cikin Sunan Hadithi na
451 cewa babban Sahabi Ubaadatu Bin Saamit ya
ambaci cewa Annabi mai tsira da amincin Allah
ya hana a canja Dirhami biyu da Dirhami daya.
Sai wani mutum ya ce: Ni ba na ganin laifin yin
hakan matukar dai in aka yi shi hanu da hanu!
Sai Ubaadatu ya ce:-
(( ﺃﻗﻮﻝ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻘﻮﻝ : ﻻ ﺍﺭﻯ ﺑﻪ
ﺑﺎﺳﺎ؟ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﻈﻠﻠﻨﻲ ﻭﺇﻳﺎﻙ ﺳﻘﻒ ﺃﺑﺪﺍ )).
Ma'ana: ((Ina cewa Annabi mai tsira da amincin
Allah ya ce Sannan kai kuma kana cewa: Ni ba na
ganin laifi cikin yin hakan? Wallahi Inuwar wani
rufin daki har abada ba zai hada ni da kai ba)).
3. Muslim ya ruwaito Hadithi na 1954 cewa akwai
wani dan'uwa ga Sahabi Abdullahi Bin Mugaffal
da ya jifa da tsakuwa ta hanyar kan farcen yatsar
hannunsa, sai ya hana shi ya kuma ce da shi:
Annabi mai tsira da amincin Allah ya hana yin jifa
ta hanyar kan farce; ya ce: ba ya iya farautar
dabbar daji, ba ya iya jiwa wani abokin gaba,
amma kuma ya kan karya hakori ya kan kuma
huda ido". Sai mutumin ya sake yin jifar. Sai ya
ce da shi:-
(( ﺃﺣﺪﺛﻚ ﺍﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻧﻬﻰ ﻋﻨﻪ ﺛﻢ
ﺗﺨﺬﻑ؟ ﻻ ﺃﻛﻠﻤﻚ ﺃﺑﺪﺍ )).
Ma'ana: ((Ina gaya maka cewa manzon Allah mai
tsira da amincin Allah ya hana yin jifa ta hanyar
farcen yatsa sannan kuma ka koma yin jifar? Har
abada ba zan yi magana da kai ba)).
Ga kadan daga cikin misalan irin yadda Taabi'ai
suke girmama maganar Annabi suke gabatar da
ita a kan maganar kowa, suke kuma nuna
fushinsu a kan duk wani wanda ya ki bin maganar
ya koma ya bi wata maganar koma bayanta:-
1. Al-Mirwaziy ya ruwaito cikin littafin Sunnah
athari na 94 cewa Taabi'i Umar Bin Abdil Aziz ya
rubuta wa mutane ya ce:-
(( ﺍﻧﻪ ﻻ ﺭﺃﻱ ﻷﺣﺪ ﻣﻊ ﺳﻨﺔ ﺳﻨﻬﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﺳﻠﻢ )).
Ma'ana: ((yadda lamarin yake shi ne: babu
mutum daya da za a yi aiki da ra'ayinsa indai
akwai sunnar da manzon Allah mai tsira da
amincin Allah ya sunnanta)).
2. Imamuz Zahbiy ya ce cikin littafin Taariikhul
Islam 7/298, da littafin Siyaru a'alaamin Nubalaa
4/472 cewa Taabi'i Abu Qilaabah Abdullahi Bin
Zaid ya ce:-
(( ﺍﺫﺍ ﺣﺪﺛﺖ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ ﻓﻘﺎﻝ : ﺩﻋﻨﺎ ﻣﻦ ﻫﺬﺍ ﻭﻫﺎﺕ ﻛﺘﺎﺏ
ﺍﻟﻠﻪ ﻓﺎﻋﻠﻢ ﺍﻧﻪ ﺿﺎﻝ )).
Ma'ana: ((Idan ka gaya wa Mutum Sunnah
sannan sai ya ce: Raba mu da wannan ka kawo
littafin Allah ka sani lalle shi batacce ne)).
3. Daaramiy ya ruwaito cikin Sunan Hadithi na
441 cewa Taabi'i Muhammad Bin Seerin ya
karanta wa wani mutum hadithin Annabi mai tsira
da amincin Allah, sai mutumin ya ce: Wane ma
ya ce kaza da kaza! Sai Ibnu Seerin ya ce:-
(( ﺃﺣﺪﺛﻚ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺗﻘﻮﻝ : ﻗﺎﻝ ﻓﻼﻥ
ﻛﺬﺍ ﻭﻛﺬﺍ؟ ﻻ ﺃﻛﻠﻤﻚ ﺃﺑﺪﺍ )).
Ma'ana: ((Ina karanta maka Hadithi daga Annabi
mai tsira da amincin Allah Sannan kai kuma kana
cewa: wane ma ya ce kaza da kaza? Har abada
ba zan maka magana ba)).
Ga kadan daga cikin misalan irin yadda Taabi'ut
Taabi'iina suke girmama maganar Annabi mai
tsira da amincin Allah, suke gabatar da ita a kan
maganar kowa, suna kuma sanar da kowa cewa:
idan sun ga wata magana tasu ta saba wa
maganar Annabi mai tsira da amincin Allah to su
yi aiki da maganar Annabi su bar maganar tasu:-
1. Imam Abu Hanifah ya ce: ((Idan Hadithi ya
inganta to shi ne mazhabata)).
2. Imam Malik ya ce: ((Ni ba kowa ba ne face
mutum; ina yin kure ina kuma yin daidai, ku yi
nazari game da ra'ayina dukkan abin da ya dace
da AAlkur'ani da Sunnah ku rike shi, dukkan abin
da bai dace da Alkur'ani da Sunnah ba ku bar
shi)).
3. Imamush Shaafi'iy ya ce: ((Musulmai sun yi
ijmaa'i a kan cewa duk wanda Sunnah daga
manzon Allah mai tsira da amincin Allah ta
bayyana a gare shi to ba ya halatta a gare shi ya
bar ta saboda maganar wani mutum)).

Taabi'it Taabi'iina suke girmama maganar Annabi
mai tsira da amincin Allah, suke gabatar da ita a
kan maganar kowa, suke kuma ganin cewa duk
mai barin yin aiki da hadithin Annabi ya koma ya
yi aiki da maganar wani to lalle wannan dan
bidi'ah ne:-
1. Imam Abu Muhammad Al-Hasanul Barbahaariy
ya ce cikin littafin Sharhus Sunnah athari na 105
shafi na 51 :-
(( ﺍﺫﺍ ﺳﻤﻌﺖ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻳﻄﻌﻦ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﺛﺎﺭ ﺃﻭ ﻳﺮﺩ ﺍﻻﺛﺎﺭ ﻓﺎﺗﻬﻤﻪ
ﻋﻠﻰ ﺍﻻﺳﻼﻡ ﻭﻻ ﺗﺸﻚ ﺍﻧﻪ ﺻﺎﺣﺐ ﻫﻮﻯ ﻣﺒﺘﺪﻉ )).
Ma'ana: ((Idan ka ji wani mutum yana sukan
hadithai, ko yana watsi da yin aiki da hadithai to
ka tuhume shi game da Musulunci kuma kada ka
yi shakkar cewa shi ma'abucin son zuciya ne dan
bidi'ah)).
2. Imam Ahmad Bin Hanbal yana cewa: ((Duk
wanda ya ki yin aiki da hadithin manzon Allah
mai tsira da amincin Allah to lalle yana kan gabar
halaka)).
Wannan shi ne ma'anar Salafiyyah, shi ne kuma
manufa da aqidar dukkan wani musulmin kirki,
amma mutumin da zai bar yin aiki da Hadithi a
bisa hujjar cewa: maganar Sahabi wane, ko
maganar Taabi'i wane, ko maganar Taabi'ut
Taabi'iina wane, ko maganar Taabi'ut Taabi'it
Taabi'iina wane ya saba wa maganar shi Annabin
to lalle wannan battacden dan bidi'ah ne. Allah
Ya taimake mu. Ameen.

No comments