Wannan kyakkyawar baiwar Allahn me suna Asma'u Nyako ta bayyana cewa wani ko wata na amfani da hotonta wajen yada hotunan batsa da sunan cewa wai itace, Asma'u ta fito tayi tir da wannan aika-aika sannan kuma ta nesanta kanta da masu yin hakan, ta kara da cewa wadanda suka santa sunsan bazatayi irin wannan abun na zubar da mutunciba.
Tayi rokon cewa duk wanda ya samu wannan labari nata yayi kokarin yadashi domin ta wanke kanta daga wadancan masu shirin bata mata suna, wasu da suka bayyana ra'ayoyinsu akan wannan batu na Asama'u sun bayyana cewa tabbas me amfani da sunan A'isha Abbas Sadiq ta rika musu magana ta manhajojin aika sakonnin hira da cewa tana so su zama abokai kuma tana amfani da hoton wannan baiwar Allahn, wasu lokutan ma tana aikawa da hotunan batsa da sunan cewa natane.
Wasu sunyi kira ga Asama'u akan cewa tayi hankali watakila wani tsohon saurayintane da suka bata yake kokarin bata mata suna ko kuma makamancin haka.
Asma'utace bata taba gamuwa da ko sanin wani me wannan sunanaba haka kuma tayi ftan cewa Allah ya tonawa meyi mata wannan abu asiri. Tayi kira ga mutane da suyi hattara dayin ko wace irin mu'amala da me wannan sunan.
No comments