Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta soma fitowa a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.
Jarumar ta shaida wa kafar bbc hausa cewa ta fara gwada sa’arta a fina-finan Nollywood ne domin ta nuna basirar da take da ita ta yin fina-finai a ɓangarori daban-daban.
A cewarta, “Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a gajerun fina-finan turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood.
Fitaccen Jarumi kuma Furodusa a Fina-finan Nollywood Mike Ezuruonye da Jaruma Hadiza Gabon Ayayin Aikin fim ɗin Lagos Real Fake Life.
“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna ‘Lagos real fake life’.
“Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin ‘yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim”.
Hadiza Gabon ta ƙara da cewa “Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim ɗinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saɓa da addini da al’adata ba”.
Jarumar ta ce babu wani “bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don haka na ji daɗin soma fitowa a fina-finan Nollywood”.

Babu Bambamci Tsakanin Fina Finan Kannywood Da Nollywood – Inji Hadiza Gabon

Kamar Yadda Kowa Yasani A Wannan Zamani Damuke Ciki Babu Mawakan Hausa Da Tauraruwarsu Take Haskawa Kamara Wadannan Mawaka Guda Biyu Wato Umar M Sharif Da Nura M Inuwa.
Wannan Daliline Yasa Mukeso Muyi Muhawara Domin Banbance Aya Da Tsakuwa A Tsakanin su Ta Hanyar Jin Ra’ayoyin Masoyansu.
Muhawarar Anan Itace Acikin Wadannan Faishan Mawaka Guda Biyu Wanene Salonsa, Kida, Lafazi, Murya Yafi Burgeka Acikinsu???
Ajiye Ra’ayinku Domin Jin Wanye Zaici Wannan Muhawara

Salo, Kida, Lafazi, Murya: Wani Abu Ne Yafi Bambamta Wakar Nura M Inuwa Data Umar M Sharif?

Sabuwar tauraruwar masana’antar Kannywood tace zata koma makaranta kuma idan Allah yayi ta samu miji zata yi aure.
Sabuwar tauraruwar fina-finan hausan na Kannywood Maryam Yahaya ta bayanar cewa yin fim ba zai hanata yin karatu domin yin karatu yana cikin abubuwan dake gaban ta a rayuwa.
A wata hira ta musamman da tayi da BBC hausa, Maryam wanda ta kammala karatu ba da dadewa tace tana kokarin cigaba da yin karatu.
Jarumar shirin “Mansoor” tace idan Allah ya nufe ta da samun miji yanzu zata yi aure kuma zata cigaba da yin karatun ta.
Sabuwar tauraruwa wanda ta fara haskawa cikin “Mansoor” bayyana cewa idan tayi aure bazata cigaba da yin fim.
Maryam Yahaya ta shigo masana’antar kannywood da kafar dama domin bayan fitowar ta a cikin “Mansoor” ta samu damar fitowa a wasu shiri da dama.
Ko zamu iya cewa wannan matashiyar zata sauya jarumtakar manyan yan wasan masana’antar kamar su Rahama sadau, Nafisa Abdullahi, Halima Atete, Hadiza Gabon da dai sauransu?

Zan Koma Makaranta Kuma Idan Nasamu Miji Zanyi Aure – inji jaruma Maryam Yahaya

Mesut Ozil na shirin kin yadda ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a Arsenal, bayan da dan kwallon ke son komawa Manchester United in ji jaridar Daily Mirror.
Sunday Express ta wallafa cewar Liverpool ta bukaci Barcelona da ta daina matsawa Philippe Coutinho a lokacin da ta yi kokarin sayen dan kwallo, inda Liverpool ta ki sayar da shi.
The Sun kuwa cewa ta yi Manchester City ta damu matuka cewar Paris St-Germain za ta bai wa Arsenal makudan kudi domin ta dauki Alexis Sanchez.
An shaidawa Manchester United ta biya fam miliyan 75 idan tana son daukar dan wasan Lazio, Sergej Milinkovic-Savic, itya ma Manchester City na son sayen dan kwallon in ji Daily Express.
Everton za ta taya dan wasan Arsenal Olivier Giroud a watan Janairun 2018, har ma ta tanadi fam miliyan 40 in ji Daily Mirror.
Daily Mail kuwa ta wallafa cewar ran Arsene Wenger ya baci matuka da ya sayar da Kieran Gibbs ga West Brom, fiye da barin Alex Oxlade-Chamberlain da ya koma Liverpool.
Tura wannan labarin

Tirkashi: ''Ozil na shirin komawa Man United''

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan da ya yada zango a birnin Landan daga Amurka, inda ya halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 a makon jiya.
Fadar shugaban kasar ce ta tabbatar wa BBC komawar shugaban gida.
Sai dai ba ta yi karin haske ba game da abin da shugaban ya yi a Landan ba.
Shugaban ya isa Landan ne ranar Alhamis daga birnin New York na Amurka.
Kafin tafiyarsa, shugaban ya gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata.
Da ma dai fadar shugaban ta ce zai je Birtaniya bayan ya kammala taron.
Sanarwar da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya aikewa manema labarai a makon jiya ta ce shugaban "Zai je birnin Landan a kan hanyarsa ta komawa gida".
Sai dai Mr Adesina bai yi karin bayani kan abin da zai sa Shugaba Buhari zuwa London ba.
A watan jiya ne dai shugaban ya koma gida Najeriya bayan ya yi doguwar jinya a Birtaniya, inda ya shafe fiye da wata uku a can.

Buhari ya koma gida

Duniya kullun kara samun cigaba akeyi ta bangaren kirkiro sabbin kwalliya musamman ta bangaren mata yanda zasu rika jan hankulan mutane da birgewa, wannan wata baiwar Allahce data fito da sabon salon gashin gira, ana iya gani yanda tayi kitso dashi kamar gashin kai a wannan hoton.

Sabon Salo: Gashin gira da kitso

Diyar marigayi tsohon shugaban kasa Hajiya Fatima Gumsu Sani Abacha kenan take taka rawar shoki a gurin shagalin bikin zagayowar ranar haihuwarta, anokai da 'yan uwa sun taru dan tayata murna muma muna kara tayata murna da fatan Allah ya karo shekaru masu albarka.

Ashe rawar shoki hadda manya?: Fatima Sani Abacha na takawa a gurin shagalin zagayowar ranar haihuwarta

Tsohuwar jarumar finafinan Hausa matar Sani Musa Danja Zaki, Mansurah Isah taja hankulan wasu mutane da suke yiwa jaruman finafinan Hausa kudin goro a duk lokacin da aka samu wata ko wani jarumi da yin ba daidaiba, Mansurah tace suma fa mutanene kuma musulmai kuma masu zagin nasu basusan irin ayyukan alherin da suke aikatawa na farantawa Allah a boyeba.
Ta kara da cewa akwai jarumai da dama da take samu akan nemawa wasu bayain Allah da suke cikin halin kaka nikayi taimako kuma haka wadannan jaruman zasu bayar da taimako su kuma bukaceta da kada ta bayyanawa Duniya.
Gadai cikakken bayanin da Mansurah tayi:
"Assalamu alaikum. Yan uwana musulmai, wallahi wallahi kuji tsoron Allah. Ku tuna akwai hisabi, Duk abinda yan film sukayi, sai kunyi suka. Kar ku shiga tsakani BAWA da UBANGIJIN sa, domin bakusan abinda yake yi a boye dan farantawa ubangiji rai ba. Mun kawo case din UMMASALAMA domin a ceto ranta, wacce take bukatan taimako cikin gaggawa, wassu suka fara zagin yan film, wai mai sukeyi, Ina duk kudin da suke tarawa? Ku kusan abinda yan film din sukeyi? Ko halin da suke ciki? Shi yasa duk Sanda wani ko wata yar film ta kirani dan taimakawa, nakan so, na rubuta ba dan komai ba, dan asan abinda sukewa jamaan gari. Akwai case din yara da aka haifa da #diabeties, a nan na rubuta cewa duk wata suna bukatan #insulin domin Karin lafiyan su, waya tuna dasu a watan nan? Babu sai Yan film. Case da muke dashi bana ummasalama kadai bane, muna da case irin na ummasalama sunfi thousands ( dubu ), ko kusan guda nawa yan film suka biya musu kudin asibiti ko magani? Ko aika musu da kayan abinci? Kuma mutanen nan ba yan film bane. @adam_a_zango @officialsanidanja @yakubu_mohd @realalinuhu musha case dasu, duk Sanda na kai musu case din wassu dan su taimaka. Sai nayi musu alkawari cewa banzan fadawa kowa ba ko na rubuta a page Dina. Nasha nuna musu cewa gara duniya tasan abinda kukayi, domin wassu mutane jakuna ne, basu tauna magana kafin su fada, yan film suna iya kokarin su na taimakawa al'ummah Wanda ba yan film ba, Amma da zarran case na yar film ta taso, sai ku fara zagi kamar su ba musulmai bane, kamar in kun taimaka haram ne, kai kayi aikin ladan ka mana, tsakanin ka da ubangijin ka in kana da hali. Ka barwa Allah komai. Nasha kawo case page Dina, wallahi Christians sun sha min dm na bada gudunmowa, har mamaki suke bani, Amma wai musulmi ne zai fara zagi da zarra kace ya taimaka, ko waya kayi musu, zasuyi alkawari bazasu cika ba. Ina mai bada hakuri ga mijina da sauran yanfilm da ake zagi a dalilina, suyi hakuri su kuma ci gaba da aikin lada. Kuma neman taimako ta kowacce iri ne, banzan daina neman wa mutane ba, in har naji labari ko an kawo min case dinsu. Allah ya shige mana gaba ameen. Allah ka bani ikon ci gaba da taba rayuwan al'umman ka domin shine farin cikina."
"Ni tambaya ta a nan, kudin yan film ne kadai ake taimako dashi? Ko kuwa su kadai Allah yace suyi taimako? Ina laifin Wanda yace, wa mai son aikin lada gashi yayi? Ba'ace dole a taimaka ba, duk mai so ko mai hali bisimillah. Kai a matsayin ka na musulmi ai ya kamata kasan cewa duk abinda bawa zaiyi, sai Allah ya yarda mishi, aure, haihuwa, shiriya, arziki, taimako, lafia, mutuwa duk sai da yardan ubangiji. Kar ku bari bakin ciki da jahilci yaci gallaba azuciyan ku. Shikenan in dan film yayi sallah sai yace Allah kayiwa yan film albarka su kadai? Ko Wanda ba dan film ba, sai yace Allah yayiwa mutane albarka Amma banda dan film? Duk daya muke a gaban ubangiji. Wallahi taimakon da yanfilm sukeyiwa a waje, ba kadan bane. Amma baku gani. Daga anyi magana sai kuce dan film. Why? Menene dan film ne? Wata hallita ce daban ko yaya? Ba uwace ta haife su ba ko ba bayin Allah bane? Ko akwai inda aka fada acikin alqurani cewa kayi taimako Amma banda dan film ? Allah ubangiji ya saka da alheri ga dukanni masu taimako, Wanda suke taimakawa a boye dana fili ameen. Allah ya shirye mu gabaki daya. Masu taimako Allah ka Kara musu budi ameen, masu niya kuma Allah kada iko ameen."
Sai muce Allah shi kyauta.

"Jama'a Ku daina yiwa 'yan fim kudin goro bakusan aikin alherin da sukeyi a boyeba">>Mansurah Isah

WACECE MACE TA GARI? //5
ITACE MAI NEMAN ILIMI
Ilimi da aiki dashi shima yana daga cikin matakin farko ga dukkan macen da take son zama ta gari. Ya zama dole ta yi aiki da hadisin Manzon Allah (SAW) cewa: "Neman ilimi wajibi ne akan dukkan musulmi da musulma". Wannan yana nuna babba da yaro, mace ko namiji, tsoho da matashi.
Duk macen da ba ta da ilimi kuma bata neman sa to hakika zaman ta na gari zayyi mata wahala. Saboda bata da fitilar da zai rinqa haska mata hanyar ta (rayuwarta).
Kuma kada ki ce wai kin yi sauka shikenan kin bar neman ilimi a'a ki cigaba da zuwa in da za a  rinqa tunatar dake Allah, In da za a koya miki hanyoyin shiga Aljannah, in da za'a rinqa koya miki zamantakewar magabata don ke ma ki yi koyi dasu. In da za a koya miki yanda zaki tarbiyyantar da 'ya'yanki.
Kin ga in a gida kike dukkan wainnan garabasar zasu rinqa wuce ki, kuma a hankali sai shaidan yayi galaba a kanki ki zama kamar ba ke ce mahaddaciyar nan ba mai bin Allah.
Sannan shi ilimi kogi ne yana dayawa, cigaba da nema shine zai sanya miki son addini da son ibada, kuma za'a rinqa miki wa'azi a hankali kina gyara halin ki.
Da sauraren wa'azin malaman Sunnah, ko a radio ko a TV kada dai ki zauna baki da wata kafa da zata rinqa koyar dake addini.
Da koyan Qur'ani da karanta shi domin samun lada da koran shaidanu a gidan auren ki.
Sannan uwa uba ilimi zai taimaka ma 'ya'yanki, domin zaki taya su tilawa a gida, zaki musu assignment. Kin ga kuwa dole mace ta gari ta nemi ilimi.
Ba na addini kadai ba har da na zamani, don ki san me duniya take ciki, saboda idan kina tunani ta bangare daya zai iya kawo naqasu ga 'ya'yanki.
Yar'uwar ku Sadeeya Lawal Abubaka

WACECE MACE TA GARI? //5

WACECE MACE TA GARI? //4
ITACE MAI IBADA
Bauta dai shine dukkan abun da Allah Yake so kuma Ya yarda da shi na daga zance da aiki.
Kuma duk mace ta gari zaka same ta da ibada, wato mai dagewa ce wurin bautar Ubangijinta. Sannan tana tsoron Allah da qanqan da kai garesa.
Kuma ta aminta tun daga farkon auren ta cewa aure ibada ne kuma Sunnah ne mai qarfi zata raya. Kuma duk abun da take yi a cikin gidan ta tun daga zaman auren tana da lada. Idan mace ta sa haka a ranta abubuwa dayawa a rayuwar aure zasu zo mata da sauki.
Itace mai dogaro ga Allah a cikin dukkan al'amuranta, kuma tana komawa gare shi a lokacin yalwa da lokacin tsanani. Kuma tana godiya gare Shi a cikin ko wane hali.
Mace ta gari sam bata wasa da sallolin ta biyar a gidan ta. Kuma ba a barin ta a baya wato tana tashi cikin dare ta roqi alkhairan duniya da lahira.
Tana qoqarin yin azumin nafila tare da izinin mijin ta.
Tana qoqarin yin kyauta da sadaqa.
Tana dagewa wurin yin addu'a. Duk abun da ya same ta na rayuwa to ta kan tsananta roqo.
Mai yawan ambaton Allah ce da Istigfari. Bakin ta danye yake wurin ambaton Allah ba ashar da maganganu marasa amfani ba.
Tana yin biyayya ga mijinta in har umurninsa bai sabawa mahalicci ba.
Kuma tana dagewa da sauran ibadodi na samun lada.
In baku manta ba Annabi (SAW) ya fada a hadisi:
(( ﺇِﺫَﺍ ﺻَﻠَّﺖِ ﺍﻟْﻤَﺮْﺃَﺓُ ﺧَﻤْﺴَﻬَﺎ، ﻭَﺻَﺎﻣَﺖْ ﺷَﻬْﺮَﻫَﺎ، ﻭَﺣَﻔِﻈَﺖْ ﻓَﺮْﺟَﻬَﺎ، ﻭَﺃَﻃَﺎﻋَﺖْ ﺯَﻭْﺟَﻬَﺎ، ﻗِﻴﻞَ ﻟَﻬَﺎ : ﺍﺩْﺧُﻠِﻲ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔَ ﻣِﻦْ ﺃَﻱِّ ﺃَﺑْﻮَﺍﺏِ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔِ ﺷِﺌْﺖِ .(( ‏[ ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ].
" Idan Mace ta yi sallolinta biyar, ta yi azumin Ramadan, ta kuma kiyaye farjinta, sannan ta yi biyayya wa mijinta, Sai ace da ita: "Ki shiga aljannah daga qofar da ki ka gadama daga cikin qofofin Aljannah" [Ahmad ‏] .
Babu yanda za a yi a kira ki ta gari bayan kina tsallake sallah, wato yin sallah yana miki wahala.
Inaa! mace ta gari ta miki nisa, don ita rige-rige take wajen ganin ta kusanci Mahaliccin ta.
Yar'uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar

WACECE MACE TA GARI? //4 ITACE MAI IBADA

WACECE MACE TA GARI? //3
ITA CE MUSULMA MU'UMINA
Farkon matakin zama ta gari shine ta kasance musulma. Musulma kuma ita ce wacce ta yi imani da Allah ta kadaita Sa a matsayin abun bautar ta, Kuma ta miqa wuya ga Allah ta hanyar miqa wuya ga umurninSa da dokokinSa.
Kuma ta yi imani da Annabi Muhammad ta hanyar yi masa da'a a umurninsa da gasgatasa a labaransa, da nisantar haninsa, da bautawa Allah kadai ta hanyar da ya shar'anta. Ta tsaida Sallah da haqqoqinta. Ta bada zakka, ta azumci watan Ramadana kuma ta je aikin hajji in ta samu iko. Wannan ce cikakkiyar musulma.
Sannan ta dauki matakin zama Mu'umina, shine imani da Allah da Mala'ikunsa, da Manzannin sa, da Litattafan sa, da Ranar qarshe, da imani da Qaddara mai kyau ko mara kyau.
Ba zaki taba zama ta gari ba har sai kin yi imani da wainnan abubuwan tun daga nan ne zaki fara ginin zama ta gari.
Don wata a dabi'un ta da halayen ta sai ka tambayi kanka anya kuwa wannan matar ta yi imani da waincan abubuwan da na ambata kuwa. Saboda gaba daya ta bar imanin ta da rukunan musulunci sun yi rauni. Kuma ta siyarwa shaidan da imanin ta, tana shirka da Allah tamkar bata yi imani da Shi a matsayin abun bautar ta ba.
Yar'uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar

WACECE MACE TA GARI? //3

KU KARANTA TARIHI, DON AKWAI WA'AZI A
CIKINSA!
ﺍﻗﺮﺅﻭﺍ ﺍﻟﺘﺎﺭﻳﺦ ﺇﺫ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻌﺒﺮ *** ﺿﻞ ﻗﻮﻡ ﻟﻴﺲ ﻳﺪﺭﻭﻥ
ﺍﻟﺨﺒﺮ
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) yake cewa:
ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻤﺸﻬﻮﺭ ﻣﻦ ﻣﺬﻫﺐ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺃﻧﻬﻢ ﻻ ﻳﺮﻭﻥ ﺍﻟﺨﺮﻭﺝ
ﻋﻠﻰ ﺍﻷﺋﻤﺔ، ﻭﻗﺘﺎﻟﻬﻢ ﺑﺎﻟﺴﻴﻒ ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻓﻴﻬﻢ ﻇﻠﻢ، ﻛﻤﺎ ﺩﻟﺖ
ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ﺍﻟﻤﺴﺘﻔﻴﻀﺔ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ -
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ; - ﻷﻥ ﺍﻟﻔﺴﺎﺩ ﻓﻲ ﺍﻟﻘﺘﺎﻝ ﻭﺍﻟﻔﺘﻨﺔ
ﺃﻋﻈﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺴﺎﺩ ﺍﻟﺤﺎﺻﻞ ﺑﻈﻠﻤﻬﻢ ﺑﺪﻭﻥ ﻗﺘﺎﻝ ﻭﻻ ﻓﺘﻨﺔ .
ﻓﺈﻧﻪ ﻳﺪﻓﻊ ﺃﻋﻈﻢ ﺍﻟﻔﺴﺎﺩﻳﻦ ﺑﺎﻟﺘﺰﺍﻡ ﺃﺩﻧﺎﻫﻤﺎ، ﻭﻟﻌﻠﻪ ﻻ ﻳﻜﺎﺩ
ﻳﻌﺮﻑ ﻃﺎﺋﻔﺔ ﺧﺮﺟﺖ ﻋﻠﻰ ﺫﻱ ﺳﻠﻄﺎﻥ، ﺇﻻ ﻭﻛﺎﻥ ﻓﻲ
ﺧﺮﻭﺟﻬﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺴﺎﺩ ﻣﺎ ﻫﻮ ﺃﻋﻈﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺴﺎﺩ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﺯﺍﻟﺘﻪ .
"Abin da ya shahara a mazhabar Ahlus Sunna shi
ne; ba sa ganin halaccin tawaye ma shugabanni,
da kuma yakarsu da makami, ko da kuwa suna
da zalunci. Kamar yadda ingantattun Hadisai
masu yawa suka zo daga Annabi (saw). Saboda
barnan da yake cikin yakar nasu, da fitinar da
take cikin hakan, girmanta ya fi barnan da za a
samu a sakamakon zaluncinsu in ba a yakesu ba,
ko ba a tada fitina ba. Saboda ana kawar da
barna mafi girma ne a cikin barna guda 2, ta
hanyar amfani da karamar barnar. Ta yiwu kusan
ba a san wata jama'a da ta yi tawaye ma
shugaba mai iko ba, face barna mafi girma ta
faru a dalilin tawayen fiye da barnar da suka
kawar".
Duba Minhajus Sunna 3/ 391.
* Abin lura:
1. Ma'ana; barnar zubar da jinane da kisan
mutane da shugabanni suke yi in an yi musu
tawaye, ya fi barnar zaluncin da suke yi wa
mutane in aka yi hakura aka bi su. Don haka sai
ayi ta hakuri da zaluncin da suke yi, don gudun
barnar da zai faru na kashe mutane da barnata
dukiya in an yi musu tawayen, kamar yadda yake
faruwa a wasu kasashen musulmi a yau.
2. Sai mun gyara kawukanmu, mun gyara
Addininmu sai Allah ya gyara mana shugabanni.
** WAIWAYE ADON TAFIYA, TARE DA DR. SANI R/
LEMO:

KU KARANTA TARIHI, DON AKWAI WA'AZI A CIKINSA! DR. SANI UMAR R-LEMO (HAFIZAHULLAH)

*TAMBAYOYI DARI (100) DA AMSA AKAN MATA:  HAILA, JININ BIKI, SALLAH, AZUMI DA HAJJI.*
Fitowa ta 1
Daga: *_Sheikh Muhammad Saleh al-Uthaimeen, Rahimahullah_*
*TAMBAYA TA 1*
Shin mace me jinin biki zata zauna har kwana arba'in ne ba zatayi sallah ba kuma ba zatayi azumi ba, ko kuma abin lura daga gareta za tayi tsarki, tayi sallah, kuma nawa ne mafi hawan kwanakin da za tayi kafin ta yi tsarki?
*AMSA:*
Mace mai jinin biki bata da kyayyadadden lokaci sai dai duk lokacin da jini ya zo mata zata zauna ba za tayi sallah ba kuma ba za tayi azumi ba kuma mijinta ba zai iya saduwa da ita ba. Amma idan taga jini ya dauke, wato ta tsarkaka ko da ko kafin ta cika kwana arba'in ne ko da jinin iyakacin  kwana goma ne kawai yayi ko kwana biyar kawai sai ya dauke, to sai tayi wanka tayi sallah, tayi azumi kuma mijinta ya sadu da ita babu laifi acikin hakan.
Sai dai abin da yafi muhimmanci shine shi jinin biki al'amari ne kebantacce kuma hukuncinsa yana ratayuwa ne da shi, wato idan jinin yazo to hukuncinsa yana nan ba za tayi sallah da azumi ba. Kuma idan jinin bai zo ba to hukhncinsa baya nan. Duk lokacin da tayi tsarki to ta wofanta daga hukuncinsa.
Sai dai idan jinin ya karu matar ta Zamo mai jinin istihada, wato jinin ciwo ke nan, sai tayi lissafin iya kwanakin al'adarta sai tayi wanka tayi sallah. Sai ta nemi maganin wannan jinin na cuta.
Muhadu a fitowa ta 2 in sha Allahu Ta'ala
✍Tattarawa:
Dan uwanku a Musulunci
*_Umar Shehu Zaria_*
Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

TAMBAYOYI DARI (100) DA AMSA AKAN MATA: HAILA, JININ BIKI, SALLAH, AZUMI DA HAJJI

Complete Tafsir Sheikh Abdulmudallib muhd
Auwal Gusau (Hafizahullah)• na daya zuwa na
Ashirin da biyar 1- 25 lakcoci 4 1438/2017
TARE DA : Jibwis Social Media Kano State •
Day 1 DOWNLOAD HERE
Day 2 DOWNLOAD HERE
Day 3 DOWNLOAD HERE
Day 4 DOWNLOAD HERE
Day 5 DOWNLOAD HERE
Day 6 DOWNLOAD HERE
Day 7 DOWNLOAD HERE
Day 8 DOWNLOAD HERE
Day 9 DOWNLOAD HERE
Day 10 DOWNLOAD HERE
Day 11 DOWNLOAD HERE
Day 12 DOWNLOAD HERE
Day 13 DOWNLOAD HERE
Day 14 DOWNLOAD HERE
Day 15 DOWNLOAD HERE
Day 16 DOWNLOAD HERE
Day 17 DOWNLOAD HERE
Day 18 DOWNLOAD HERE
Day 19 DOWNLOAD HERE
Day 20 DOWNLOAD HERE
Day 21 DOWNLOAD HERE
Day 22 DOWNLOAD HERE
Day 23 DOWNLOAD HERE
Day 24 DOWNLOAD HERE
Day 25 DOWNLOAD HERE
# Lakcocin Ramadan#
1- DOWNLOAD HERE
2- DOWNLOAD HERE
3- DOWNLOAD HERE
4- DOWNLOAD HERE
            Kuyi Sauraro lafiya
°°°°°°°°°°°
Ku cigaba da kasan cewa da
www.facebook.com/socialmediakano
JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO•
wannan tafseeran sun zo muku ne karkashin kwamitin 
JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO

Complete Tafsir Sheikh Abdulmudallib muhd Auwal Gusau (Hafizahullah)• na daya zuwa na Ashirin da biyar 1- 25 lakcoci 4 1438/2017

Complete Tafsir Dr. Sani Umar Rijiyar lemo
(Hafizahullah)• 1438/2017
TARE DA : JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO•
Day 1 DOWNLOAD HERE
Day 2 DOWNLOAD HERE
Day 3 DOWNLOAD HERE
Day 4 DOWNLOAD HERE
Day 5 DOWNLOAD HERE
Day 6 DOWNLOAD HERE
Day 7 DOWNLOAD HERE
Day 8 DOWNLOAD HERE
Day 9 DOWNLOAD HERE
Day 10 DOWNLOAD HERE
Day 11 DOWNLOAD HERE
Day 12 DOWNLOAD HERE 
Day 13 DOWNLOAD HERE
Day 14 DOWNLOAD HERE
Day 15 DOWNLOAD HERE
Day 16 DOWNLOAD HERE
Day 17 DOWNLOAD HERE
Day 18 DOWNLOAD HERE
Day 19 DOWNLOAD HERE
Day 20 DOWNLOAD HERE
Day 22 DOWNLOAD HERE
Day 23 DOWNLOAD HERE
Day 24 DOWNLOAD HERE
Day 25 DOWNLOAD HERE
Day 26 DOWNLOAD HERE
Day 27 DOWNLOAD HERE
        Kuyi Sauraro lafiya
°°°°°°°°°°°
Ku cigaba da kasan cewa da
www.facebook.com/socialmediakano
JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO

Complete Tafsir Dr. Sani Umar Rijiyar lemo (Hafizahullah)• 1438/2017 TARE DA : JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO

Complete Tafsir. Dr. Abdullah Sale pakistan
(Hafizahullah)• 1438/2017
TARE DA : Jibwis Social Media Kano State •
Day 1 DOWNLOAD HERE
Day 2 DOWNLOAD HERE
Day 3 DOWNLOAD HERE
Day 4 DOWNLOAD HERE
Day 5 DOWNLOAD HERE
Day 6 DOWNLOAD HERE
Day 7 DOWNLOAD HERE
Day 8 DOWNLOAD HERE
Day 9 DOWNLOAD HERE
Day 10 DOWNLOAD HERE
Day 11 DOWNLOAD HERE
Day 12 DOWNLOAD HERE
Day 13 DOWNLOAD HERE
Day 12 DOWNLOAD HERE
Day 13 DOWNLOAD HERE
Day 16 DOWNLOAD HERE
Day 17 DOWNLOAD HERE
Day 18 DOWNLOAD HERE
Day 19 DOWNLOAD HERE
Day 20 DOWNLOAD HERE
Day 21 DOWNLOAD HERE
Day 22 DOWNLOAD HERE
Day 23 DOWNLOAD HERE
Day 24 DOWNLOAD HERE
Day 25 DOWNLOAD HERE
Day 26 DOWNLOAD HERE
     Kuyi Sauraro lafiya
        °°°°°°°°°°°
Wannan tafsirai zun zo muku ne karkashin kulawar jibwis social media kano
Ku cigaba da kasan cewa da
JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO•

Complete Tafsir. Dr. Abdullah Sale pakistan (Hafizahullah)• 1438/2017

SHUGABAN YAN KOGO GOGAGGEN
MAKARYACI NE
ABUN YA BANI MAMAKI KAMAR YADDA AUDU YAKE* *KIRARIN CEWA SHINE SHUGABAN MASU WA'AZI
TO TA TABBA SHINE
SHI TACECCEN MAKARYA CI NE.
Ga yadda Abun ya ke
Abduljabbar Nasiru kabara ya bude baki baya jin kunya baya jin tsoran Allah yace babu inda annabi (s a w) yace a dage tufafi (wando).
      *Ga Audion* *Yadda ya fada daga bakin sa*
DOWNLOAD HERE
Yace  duk wanda ya fada to karya yake,
To anan zaku kara gane karyar sa kamar yadda ya gada  a wajan waliyiya…
1- To kamar yarda yace babu inda Annabi yafada to yanzu zan nuna masa wajan,
Malaman musulunci sun fitar da Hadisai a cikin littafan su
Gasu kamar haka
[Bukhari, Abu dawud, Ibn Majah da Ahmad suka fitar dashi.
Hadisin yana cewa Annabi (saw) yace
"Duk abinda ya wuce idon
sawu na tufafi (Riga, gwado/kwarjalle) to yana cikin wuta.
A wani hadisin kuma daga Abu
hurairah (ra) Yace Annabi (saw) yace: "Allah ba zai kalli wanda ya ja tufafinsa akasa ba saboda girman kai".
Acikin wani Hadisi kuma
Annabi (saw) ya ce: "Mutum uku Allah ba zai yi magana dasu ba a ranar Al- Qiyamah kuma ba zai dube su ba (kallo na rahma)
kuma zai tsarkake su ba kuma suna da azaba mai girma; na farko daga cikinsu shi ne mai sakin tufafinsa ya wuce idon sawu".   [Imam Muslim da Abu dawud, da Nisa'i da Ibn Majah da Ahmad da Darimi].
2- Abu na Gaba   shine rashin sanin Qur'ani da yayi
Shi gogagge wato idan yana Karatun Qur'ani Anan zaka gane wallahi anyi Asarar Kudin tara,
Amma idan waka ce to abun zai baka mamaki, ga yadda Abun yake.
A cikin Surah Maryam 59
Inda Allah yake cewa:-
فَخَلَفَ مِنۢ بَعْدِهِمْ خَلْفٌ أَضَاعُوا الصَّلٰوةَ وَاتَّبَعُوا الشَّهَوٰتِ ۖ فَسَوْفَ يَلْقَوْنَ غَيًّا
To kuma  Gogaggen Mai wa'azi Sai yace 
وخلفة في خلف أضا عوا الصلوة واتبعوا الشهوت فسوف يلقون غيا
Ga Audion daga bakin sa
              *Karatun Sarkin Kogo*
----------
*Gyaran daga bakin Sheikh ja'afar Mahmud adam*
Allah Sarki Abun A zubar da hawaye amma  su yan kogo sun kasa gyara masa irin wannan tabar gazaka da yayi.
Ga audion kaji yadda ya sassara wannan aya
Sannan ka saurari gyaran daga bakin gangaran kafi gwani wane gwani ciki fal shakku wato sheikh ja'afar Mahmud adam, Allah yayi masa rahma
Mai sauraro kayi Alkalanci na gaskiya idan kaji...
3- Abu na gaba shine abu na uku
shima dai tabar gaza ce akan Qira'ar gogaggen makaryaci.
A cikin surah Al-Ahzaab : aya ta 58.  Allah yana cewa
وَالَّذِينَ يُؤْذُونَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنٰتِ بِغَيْرِ مَا اكْتَسَبُوا فَقَدِ احْتَمَلُوا بُهْتٰنًا وَإِثْمًا مُّبِينًا
Shi kuma gogagge tacaccan makarya ci sai ya ce
الذير مون المو منين بغير مااكتسبو فقد احتملوا بهتنا واثما مبينا.
Allah sarki Amma Abun mamaki an rasa wanda zai gyara masa.
shima ga Audion ka saura -
*karatun Sarkin kogo*
*Shima Gyaran daga bakin Sheikh ja'afar Mahmud adam*
Sannan ka saurari gyaran daga bakin gangaran kafi gwani wane gwani ciki fal shakku wato sheikh ja'afar Mahmud adam, Allah yayi masa rahma.
   
Mai Sauraro Kaine Alkhali kana da hankalin da zaka fahinci yadda Abun yake
°°°°°°°°°°°°°°°°
Wannan shine fita ta daga cikin jerangiyar abubuwan da zan kawo muku na karerayin Audu wazirin Shi'a
nan gaba insha Allah har video zan haska yadda Abubuwan suke gudana .

SHUGABAN YAN KOGO GOGAGGEN MAKARYACI NE ABUN YA BANI MAMAKI KAMAR YADDA AUDU YAKE* *KIRARIN CEWA SHINE SHUGABAN MASU WA'AZI TO TA TABBA SHINE SHI TACECCEN MAKARYA CI NE.

Ga Amsarmu Zuwa Ga Abba Koki Tare Da Raddi Da Zuwa ga Wanda Yake Bawa Kariya Abduljabbar
WANENE YAKASHE DALHA??(
.
WANNAN DA'AWAR ITA SARKIN GIDA YAYI
BAYAN YA KAFA HUJJA KAMAR HAKA:
.
*YAZO CIKIN SIYAR 28/255.
.
MARWAN YA KALLI DALHA RANAR YAQIN
JAMAL ,SAI YACE:
ﻟﺎ ﻃﻠﺐ ﺛﺄﺭﻱ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﻴﻮﻡ , ﻓﺮﻣﻰ ﻃﻠﺤﺔ ﺑﺎﻟﺴﻬﻢ ﻓﻘﺘﻠﻪ .
"NI KAM BA NA NEMAN WATA FANSA TA
JININ S. USMAN, SAI YAJEFI DALHA DA
MASHI YAKASHESHI".
.
** DAKUMA FADINSA:
.
MARWAN YA FADAWA DAN S. USMAN:
ﻗﺪ ﻛﻔﻴﻨﺎﻙ ﺑﻌﺾ ﻗﺘﻠﺔ ﺑﻴﻚ
HAKIKA MUN ISAR MAKA- MUNYI MAKA
AIKI- GAME DA BANGARE NA WADANDA
SUKA KASHE MAKA BABANKA".
.
KUMA ALHALIN DALHA YANA CIKIN
WADANDA SUKE DA'AWAR NEMAN FANSAR
JININ S. USMAN, SAI GASHI MA'AIKACI
AGIDAN S. USMAN DIN YA CE DALHA DINNE
YAKASHE SHI; DON HAKA DAMAN MASU
CEWA JININSA SUKE NEMA SUNE DIN SUKA
KASHESHI DASUKAGA ZATA KAWABE SAI
SUKA FITO SUNA DA'AWAR JININSA SUKE
NEMA.
.
AMSA GAMEDA WANNAN TUHUMAR TASA:
.
1: RUWAYAR DKA KAWO TAFARKO
ﻟﺎ
ﻃﻠﺐ ﺑﺜﺄﺭﻱ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﻴﻮﻡ
BAGAWI YA KAWO TA CIKIN MU'UJAM NA
SAHABA 3/411. BATA INGANTA BA KUMA
SABODA ABUBBA KAMAR HAKA:
.
* AKWAI QATADA BN DI'AMAH ASSADUSIY
ACIKIN ISNADINTA, WANDA KUMA YANA
TADLISI, KUMA BAI SARRAHA SAMA'INSA
DAGA JARUD BA.
YAZO CIKIN: ﺗﻌﺮﻳﻒ ﻫﻞ ﺍﻟﺘﻘﺪﻳﺲ SHAFI 35,,
LAMBA TA 92:
ﻗﺘﺎﺩﺓ ﺑﻦ ﺩﻋﺎﻣﺔ
HAFIZ YACE:
ﻛﺎﻥ ﺣﺎﻓﻆ ﻋﺼﺮﻩ , ﻭﻫﻮ ﻣﺸﻬﻮﺭ ﺑﺎﻟﺘﺪﻟﻴﺲ .
** ﺟﺎﺭﻭﺩ ﺑﻦ ﺑﻲ ﺳﺒﺮﺓ YANA QARAMI SANDA
KISSAR TAFARU; DON HAKA BAI HALACCI
YAKIN JAMALBA, BARE KUMA YABADA
LABARIN ABUNDA YAFARU ACAN.
SANNAN N RUWAITO TA DA LAFAZIN:
ﻟﺎ ﺩﺭﻙ ﺑﺜﺄﺭﻱ ﺑﻌﺪ ﺍﻟﻴﻮﻡ
HAKIM YA KAWO TA CIKIN
MUSTADRAK3/417.
BATA INGANTA BA KUMA SABODA JAHALAR
SHARIKH DA UTBAH.
2: RUWAYA TABIYU:
ﻗﺪ ﻛﻔﻴﻨﺎﻙ ﺑﻌﺾ ﻗﺘﻠﺔ ﺑﻴﻚ .
AN RUWAITO TA DA LAFAZIN ﺣﺪ ﻗﺘﻠﺔ ﺑﻴﻚ
DAKUMA ﺑﻌﺾ ﻗﺘﻠﺔ ﺑﻴﻚ
KHALIFA BNL KAYYAD YA KAWO TA CIKIN
TARIKH 1/181.
.
HAKA IBN ASAKIR CIKIN TARIKHU
DIMASHQ.
HAKIM CIKIN MUSTADRAK 3/370:
KUMA BATA INGANTABA;
.
* SABODA JAHALAR ﻋﻢ ﻳﺤﻴﻰ ﺑﻦ ﺳﻌﻴﺪ
ﺍﻟﺄﻧﺼﺎﺭﻱ .
.
*SANNAN KUMA JUWAIRIYYA SHI KADAI
YARUWAICETA DAGA YAHYA, BAI SAMU
MUTA BA'A BA, SANNAN KUMA BA'ASANSHI
DA RUWAYA AGURINSABA.
.
* AKWAI IBDIRA BI CIKIN LAFUZZAN
RUWAYAR; DON HAKA TA SABAWA SAURAN
RUWAYOYINDA KE NUNA MARWAN NE
YAKASHE DALHA.
.
** ATAKAICE DAI HUJJOJINNASA BASU
INGANTABA.
GAME DA WANDA YA KASHE DALHA
MALAMAI SUN KASU GIDA BIYU:
.
1: WADANDA SUKE GANIN BA MARWANNE
YAKASHE DALHA BA,
IBN KASIR YAFADA CIKIN BIDAYA 7/248:
ﻭﻗﺪ ﻗﻴﻞ : ﺍﻟﺬﻱ ﺭﻣﺎﻩ ﻏﻴﺮﻩ , ﻭﻫﺬﺍ ﻋﻨﺪﻱ ﻗﺮﺏ , ﻭﺇﻥ
ﻛﺎﻥ ﺍﻟﺄﻭﻝ ﻣﺸﻬﻮﺭﺍ .
HAKIKA ANCE BA SHI -MARWAN - BANE
YAJEFI DALHA DAMASHINDA YAKASHESHI,
KUMA WANNAN RA'AYIN SHINE YAFI KUSA
DA DAIDAI AGURINA, KODA DAI MAGANAR
FARKO- CEWA MARWANNE YAKASHE
DALHAN- TA SHAHARA DAYAWA.
.
2: WADANDA SUKA TAFI KAN CEWA
MARWANNE YAKASHE DALHA DIN, SUN
KAFA HUJJA DA RUWAYOYI DA BINCIKE
YANUNA DAYAN WADANNANNE:
.
* WADANDA SANADIN BAI INGANTABA KAI
TSAYE, WANDA KUMA RUWAYOYIN SUN KAI
GUDA BIYAR, AMMA DUKA BASU DA
INGANCI.
.
** RUWAYOYINDA ISNADINSU KALAU YAKE,
SAI DAI ILLAR RUWAYARSU,
MARUWAITANSU BASU HALACCI KISSAR BA;
DON HAKA YA AKAI KUMA SUKA BADA
LABARIN ABUNDA YAFARU AFILIN YAQIN,
BAYAN BASU HALACCE SHIBA, BA TARE DA
KUMA SUN FADI AGUN WA SUKA JI BA.
.
ATAKAICE DAI KENAN MARWAN BA SHI NE
YAKASHE DALHA BA.

WANENE YAKASHE DALHA

Lacca kenan da aka gabatar a Ranar Asabar 12/8/2017,
An gabatar da Lacca a makarantar koyan sharia ta Aminu kano legal dake nan kano.
Mai taken: Mafificin Sahabbai.
Tare da  Shekh Abubakar Abdussalam (Baban gwale).
Ta'aliki: Dr Muslim Ibrahim.
*YANA DA KYAU KU SAURARA KUJI DOMIN ZAKU KARU
Kuyi Sauraro lafiya
°°°°°°°°°°°

Download here


Ku cigaba da kasan cewa da
Jibwis social media kano
Like →→ www.facebook.com/socialmediakano
JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO•

Mafificin Sahabbai mp3 Sheikh Abubakar Abdussalam Baban gwale

HUDUBOBIN JUMA'AH NA KANO
Tareda:  JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO •
Hudubobin da a ka gabatar Rana juma'a
™8-09-2017™ a wasu daga cikin masallatan garin kano
             °°°°°°°°°°°
1- Hudubar juma'a Daga masallacin Usman bin Affan dake kofar gadon kaya Tare da Dr. Abdullah Usman Gadon kaya (Hafizahullah)
DOQNLOAD HERE
2-Hudubar Jum'a daga masallacin Ihya'ussunnah Kofat nasarawa tare da Dr. Sani Ashir kano (Hafizahullah)
DOWNLOAD HERE
3-Huduba juma'a daga masallacin Uhud maikalwa
tare da Dr. Kidir Bashir (Hafizahullah)
DOWNLOAD HERE
4-Hudubar juma'a daga masallacin Umaral faruq unguwa uku kano
tare da Dr. Abdulqadir isma'il kano (Hafizahullah)
DOWNLOAD HERE
5- Hudubar juma'a daga masallacin juma'a na Ihya'ussunnah gwammaja
tare da sheikh mubarak Lawan gauren maje (Hafizahullah)
DOWNLOAD HERE
6-Hudubar juma'a daga masallacin Markaz imamul bukhari R/zaki tare da Dr. Rabiu Umar r-lemo (Hafizahullah)
DOWNLOAD HERE
8-Hudubar juma'a daga masallacin Khalid bin
walid tare da malam Abba Abdallah gwale (Hafizahullah)
DOWNLOAD HERE
9- Hudubar juma'a daga masallacin juma'a na Jami'u Abu huraira gobirawa titin yan sumohal tare da Sheikh Shehu Mansur Dala (Hafizahullah)
DOWNLOAD HERE
10-Huduba juma'a daga masallacin Malunfashi Area tare da imam mutawakill mustapha (Hafizahullah)
DOWNLOAD HERE
11- Hudubar Juma'a daga masallacin Abubakar Sadiq
daga bakin Malam Abdul'aziz Husain (Hafizuhullah)
DOWNLOAD HERE
12-Hudubar daga ga Masallacin Juma'a na Tudun Murtala Kano
Tare da Barr Ishaq Adam Ishaq (Hafizahullah)
DOWNLOAD HERE
         Kuyi Sauraro lafiya
              °°°°°°°°°°°
Ku cigaba da kasan cewa da
Jibwis social media kano
Like →→ www.facebook.com/socialmediakano
JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO

HUDUBOBIN JUMA'AH NA KANO Tareda: JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO •

*ALLAH YA JIKAN SHEIKH MUHAMMAD NASIRUDDEEN AL-ALBANI!!*
✍��Rubutawa: *_Dr Rabi'u Umar Rijiyar Lemo, Kano_*.
21/07/2017.
Tun sama da shekaru ar'ba'in baya da suka wuce, babban malamin hadisin wannan karni Sheikh Muhammad Nasiruddeen Al-Albani ya wallafa wani littafi mai matukar fa'ida da tarin ilimi, mai suna
ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺣﺠﺔ ﺑﻨﻔﺴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻘﺎﺋﺪ ﻭﺍﻷﺣﻜﺎﻡ
A cikin wannan littafin shehin malamin ya yi bayanin wajabcin komawa Sunnah a babin akida da shari'a da haramcin saba mata. Haka nan malamin ya yi bayanin bacin gabatar da kiyasi da waninsa a kan Sunnah.
A fasali na uku kuwa shehin malamin bayani ya yi a kan Hadisul Aahad (wanda ba mutawatiri ba) hujja ne a babin Akida da hukunce-hukuncen shari'a, babu wani bambanci da shi da hadisi Mutawaatiri. A wannan fasali dai shehin malamin ya yi bayanin kin karbar hadisi ingantacce, da hujjar wai Aahad ne, bidi'a ne, ya sabawa abin da magabata na kwarai suke kai, na karba da aiki da dukkan hadisin da ya inganta daga Annabi S.A.W, a babin Akida da waninta.
A karshe Shehin malamin ya cike da bayanin Taqlidi da hukunce-hukuncensa.
Wannan littafi yana kyau malamai da daliban ilimi su karanta shi, su fahimce shi, su fito da abin da yake cikinsa, don kare mutane daga fadawa shubuhohin su BABAN BOLA, masu kwashe kwashen munanan ra'ayi da soke ingantattun hadisan Manzon Allah S.A.W.
Allah ka jikan Sheikh Albani, ka yi masa rahama, ka saka masa da Aljannar Firdausi, saboda kare sunnar Manzon Allah S.A.W da ya yi a rayuwarsa.

ALLAH YA JIKAN SHEIKH MUHAMMAD NASIRUDDEEN AL-ALBANI!! Dr. Rabiu Umar Rijiyar lemo (hafizahullah)

Dr. Abdullah Usman Gadon Kaya
GA YAKIN BADAR YA TUNKARO!!!
Tunda anzo karshen Kamfen, ga Shawarwari na
gare mu kamar haka.
@ mu kyautatawa Ubangiji Zato akan cewa Tabbas
zamu Samu Nasarar Murkushe Wannan Mulki na
Zalunci , Danniya, Handama, Babakere, nuna
Bangaranci da banbanci karara, karya Tattali Arziki
da Imani, MULKIN DA ALLAH YASA TAFI YAWA A
CIKINSA.
@ Mu yawaita adduah, da Komawa ga Allah , da
rokon sa dere da rana akan yasa zamu ci Nasarar
wannan Yaki, don kuwa wadan nan mutanen
Wallahi Bamu iya samun nasara akan su In ba
mun koma ga Allah ba. Wannan shi ne sirrin.
@ Jama, a ku sani, in ba Allah ba, ba wanda ya
isa ya kwace Mulkin daga hannun wadan nan, da
suka dandana suka ji dadin sa, suka SHA JINI
TALAKAWA SUKA MORE, Allah kadai shi zai mana
Gatan da Bamu Tsammani. Saboda su
-suke da Kudi a hannu.
- jamian Tsaro na hannunsu.
- Tsagerun Kasa na Hannunsu.
MU KUMA ALLAH NA HANNUN MU ,
ALHAMDULILLAH!
@ A karancin Shekaru na Ban taba ganin Shugaban
da ya gamu da Mugun bakin jini daga Jama, arsa
ba, irin Wannan Malafar, saboda Ketar sa da
Mugun Nufin sa ya fito Fili .wajibi ne Mu bada duk
abinda muka Mallaka , na kudi tunani, karfi,
shawara, lokaci, mu kawar da wannan Sharri, ko
ma sha iska. Jikokin mu sa rayu a Kasar su
sakata su wala.
@ kuyi cin cirindo da Gaggawa wajen Mallakar
Katin Zabe, don shi ne Takwabin yakin. Kada ku
sayar da yancin ku da Mutuncin ka, ka bada
damar Barna da zalunci su ci gaba da wanzuwa.
@ A bun bakin ciki na samu labarin , ana karbe
Katin wasu ana basu mutanen kauye kuma Buhun
taki, na Birni kuma Buhun Shinkafa, wanda akarena
masa Hankali kuma Dubu Daya.
@ Dole ne mu fito kwai da kwarkwata, mu jure mu
daure mu jajirce, wajen wannan Yaki na kawo
Adalci da korar Zalunci fata fata.
@ Kada Barazana, ko Hayaniya su kore mu daga
gindin Akwati , mu jure duk Rintsi mu bi Hakkin mu
sai mun Tabbatar gaskiya ta tabbata.
@ idan ta kama mu yi shimfida a kawo mana
abinci daga gida ne , wallahi wajibi ne muyi hakan.
@ jama, a Kada mu goyi bayan Hargitsi da
hayaniya sam! Sun shirya zasuyi Ta Bare, tunda
sun tabbatar basu da nasara, kada mu biye musu.
Duk wanda zai kawo muku Hayaniya ku dauke shi
cancak daga Rumfar zabe ku kaishi daki ku kulle
shi sai an gama zabe ku sako shi.
BA GIRIN GIRIN BA DAI TAYI MAI!!!
@ wajibi ne mu Tsananta Adduah shi kansa
Bukhari din Allah ya datar dashi wajen aiki, da
kuma adalci, Allah ya raba shi da Sharrin masu
sharri , ciki da waje , ya raba shi da Miyagun da
suka fito daga Pdp suka kewaye shi, don sune
abin Tsoro kada su hana shi aiki.
@ wallahi idan ta kuskure mana Bamu samu
Nasara ba fa akwai matsala fa! Sai dai Hijira
Kawai , Allah ya takaita.
@ kada a manta da maganar Hana mata saka
lalle, yana da muhimmamnci kwarai, kada suje a
hana su zabe.
@ Jama, a muyi ta adduah , duk wani mai Nufin
mu da Sharri Allah ya mayar masa kansa, mYa
Allah kada ka basu damar Magudi, ya Allah, kayi
mana maganin Jamian Tsaro masu Mugun nufi
akan mu ranar zabe ya taimaki masu kishin kasar
su da Al ummarsu da taimakon gaskiya.
Sai Takarda ta gaba.

Dr. Abdullah Usman Gadon Kaya GA YAKIN BADAR YA TUNKARO!!!

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*YANKE FARCE DA YIN ASKI GA WANDA ZAI YI
LAYYA: ME YA TABBATA A SUNNA?*
*Rubutawar: Dr. Mansur Sokoto*
2 ga Dhul Hajji1438H (24/8/2017)
A can baya inda muka fito, albarkacin kiran
Danfodiyo da tajdidin Sheikh Abubakar Mahmud
Gummi *_(Allah ya jikan su da gafara gaba
daya)_* ba mu bukatar sai mun fadada sharhi a
kan mas’ala idan muka kawo Hadisin da ya
tabbatar da ita. Musamman kuma a yan shekarun
nan na baya, bayan bayyanar matasan Malamai
masu kira zuwa ga Sunnah a cikin kungiyar Izala
da wadanda ma ba a cikin ta ba. Amma a yan
kwana kwanan nan abin ya fara sauyawa saboda
bayyanar wasu wadanda babu wata Sunnah da
suka bari sai sun dauki sungumi suna son rusa
ta. Suna amfani da sunan Malikiyya, alhali Imam
Malik da Malikawan Malamai sun yi hannun riga
da wannan tafarki nasu.
Hana yanke farce da cirar gashi ga wanda yake
niyyar yin layya, Sunnah ce da Nana Ummu
Salma (R) ta cirato mana daga Manzon Allah (S)
a hadisi ingantacce wanda Imamu Muslim ya
riwaito a cikin ingantacce kuma karbabben
Littafinsa (Hadisi na 1977). Wannan shi kadai ya
isa a wurin Ahlus Sunnah ba sai an tafi da nisa
ba. To, amma sai suka sanya shakku game da
Hadisin, wai Nana A’isha ta soke shi. Allah ya
tsare ta da soke abinda ya tabbata daga Manzon
Allah (S).
1. Da farko dai, yana da kyau a sani, ba Nana
Ummu Salma ce kadai ta tabbatar da wannan
Sunnar ba. A’a, Sunnah ce da Sahabbai suka sani
kuma suka yi aiki da ita. Domin Ishaq bn
Rahawaihi a cikin Musnad nasa (1817) da Al-
Hakim cikin Mustadrak (7521) sun yo riwaya da
ingantaccen isnadi daga Sarkin Malaman Tabi’ai
Sa’id bn Musayyib an tambaye shi, me zai ce a
kan fatawar wani Malami Yahaya bn Ya’mar da
yake cewa, idan mutum yana da niyyar yin layya
aka shiga goman farko ba zai aske gashi ko ya
yanke farce ba? Sai ya ce, haka ne. Lallai
Sahabban Manzon Allah (S) haka suka fada.
Shi ma Yahaya bn Ya’mar da ya yi waccan
fatawar ya karfafa ta da ruwaya daga Ali bn Abi
Talib (R) kamar yadda Imam At-Tahawi ya
ruwaito a cikin Sharh Mushkil Al-Athar
(14/42-43) da Ibn Abi Khaithama a cikin At-
Tarikh nasa (2/124).
2. Nana A’isha (R) ba ta yi maganar Hadisin
Ummu Salma ba sam, balle ace ta soke shi. Abin
da ya faru shi ne, kamar yadda Imam Al-Bukhari
(hadisi na 1700) da Muslim (Hadisi na 1321)
suka riwaito cewa, Ziyad bn Abi Sufyan ya aika
ma Nana A’isha wasika yana tambayar ta akan
fatawar Ibn Abbas (R) da ya ce, idan mutum zai
yi Hadaya, duk abinda aka haramta ma Alhaji shi
ma an haramta masa. Sai Nana A’isha ta ce, bai
yi daidai ba. Ta ce, domin ni na shirya dabbobin
Hadayar Manzon Allah (S) da hannuna, sannan
ya sanya masu alama da hannayensa, ya aiki
mahaifina (Sayyidina Abubakar) da su zuwa
Makka (A shekara ta tara kenan, da ya yi Amirul
Hajji), kuma ba abinda ya fasa yi har aka soke
hadayar tasa.
To, ka ga a nan mas’aloli biyu ne daban daban.
Hadisin Ummu Salma yana maganar wanda zai yi
layya yana zaune a garinsa. Hadisin Nana A’isha
kuma yana maganar wanda ya aika dabbobi
zuwa Makka domin ayi masa Hadaya kamar
yadda Manzon Allah (S) ya yi. Don haka, Nana
A’isha (R) ta yi gyara ne ga fatawar Ibn Abbas
(R) da ya mayar da wanda ya aika hadaya a
matsayin Alhaji; ba ya aski, ba ya sanya
dunkakken tufa, ba ya farauta, kuma ba ya
saduwa da iyali har sai an soke ko an yanka
hadayarsa. Haka magabata irin su Imam Ahmad
bn Hambal da Yahaya bn Sa’id Al-Ansari suka
fassara wadannan Hadisai guda biyu. Duba: At-
Tamhid na Ibn Abdil Barr (17/234) da Masa’il
Salih ga Imam Ahmad (2/262) da kuma Lata’if
Al-Ma’arif na Ibn Rajab (Shafi na 272).
Idan ma kuma aka ce, lallai babu banbanci a
tsakanin Hadisan biyu, sabanin yadda su
wadancan magabata suka fada, to tafarkin
Malamai a irin wannan shi ne, Hadisai biyu
ingantattu sun yi hannun riga, kuma akwai
hanyoyin da ake bi a hada hancinsu, ayi aiki da
su gaba daya ba tare da an yi watsi da ko guda
ba. A nan sai a gabatar da wanda yake “ﺧﺎﺹ ” ya
kebance wanda yake “ﻋﺎﻡ ”. Ma’ana, sai ace, halal
ne ga wanda zai yi hadaya ya yi duk abinda aka
hana alhazai su yi kamar yadda Nana A’isha ta
ce, amma ban da yanke farce da aske gashi
saboda Hadisin Nana Ummu Salma. Kun ga a
nan, ba a dauki daya, aka jefa daya a Bola ba.
*Matsayar Malaman Fiqihu a Kan Wannan
Sunnah:*
Sanannen abu ne cewa, magabata suna gina
fatawoyinsu ne a kan Hadisan Annabi (S) da
kuma fatawoyin Sahabbansa. Sukan samu sabani
gwargwadon yadda nassi ya zo a wurin su ko
kuma yadda suka fahimce shi.
A cikin wannan mas’ala, akasarin Malamai sun yi
aiki da wannan Sunnar; sun hana a cire farce ko
a aske gashi idan mutum yana da niyyar yin layya
kuma watan Dhul Hijja ya riga ya kama. Cikin su
akwai masu kai wannan hani a matsayin haramci
kamar Imam Ahmad da Shafi’i da Ishaq bn
Rahawaihi da Rabi’ah – Malamin Imam Malik, da
Dawud bn Ali da Abu Thaur da Auza’i da Ibn
Hazm da sauran su. Kuma wannan ita ce fatawar
Sarkin Malaman Tabi’ai Sa’id bn Al-Musayyib.
Allah ya jikan su baki daya. Akwai kuma
wadanda suka ce, wannan hanin ba ya da
tsanani, makaruhi ne. Kamar yadda Malikawa da
wasu daga cikin Shafi’awa suka yi fatawa. A
cikin tabi’ai kuma Al-Hassan Al-Basri shi aka
sani da daukar wannan matsayin.
Amma Imam Abu Hanifa – daga cikin Malaman
Mazhabobi - shi kadai ne bai yi fatawa da
wannan hanin ba. Kuma babu wani nassi daga
wurin sa da ya nuna sukar wancan Hadisi na
Ummu Salama balai ace ya jingina sokewar ga
Nana A’isha. Babu shakka, almajiransa sun yi ta
kai da komo don kare matsayin nasa. Amma duk
abinda suka kawo ba zai hana ayi aiki da wannan
tabbatacciyar Sunnah ba. Yin aiki da ita ma ciko
ne ga ita kanta ibadar ta yin layya kamar yadda
Ibnul Qayyim ya fada. A cikin almajiran Abu
Hanifa ma akwai wadanda suka yi aiki da
wannan Sunnah kamar Imam At-Tahawy da Mulla
Ali al-Qari da kuma Ibn Abidin mai Hashiya.
Daga karshe, ina kira ga yan uwana Musulmi
gaba daya da mu san matsayin Manzon Allah (S),
mu ba shi hakken da Allah ya ba shi na
girmamawa da darajantawa. Babu kuwa wata
girmamawa da ta rage mana fiye da kimanta
umurninsa da haninsa, da rashin gabatar da
umurnin kowa ko haninsa a kan nasa. Allah ya yi
muna muwafaqa, ya sa mu cikin cetonsa.
*_Alhamdu lillah_*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *YANKE FARCE DA YIN ASKI GA WANDA ZAI YI LAYYA: ME YA TABBATA A SUNNA?