Gwamnatin tarayya ta dage kaddamar da sabon kamfanin jiragen sama na Najeriya me suna Nigeria Air a turanci har sai mama ta gani.
Ministan sufurin jiragen sama,Hadi Sirika ne ya bayyanawa manema labarai haka bayan kammala taron majlisar koli ta kasa a jiya, Labaraba.
Ministan ya ce, majalisar a yanzu ta jinginar da aikin kafa kamfanin sufurin jirgin sama na Najeriyar.
Duk da cewa ministan ya ce, dakatarwar ta wucin-gadi ce, amma kuma bai sanar da lokacin da za a dawo kan maganar ci gaba da aikin ganin jiragen kamfanin na Nigeria Air sun fara tashi ba, abin da ake ganin da wuya ya yiwu a nan da dan gajeren lokaci domin kasar na fuskantar manyan zabukanta a shekara mai zuwa.
Wannan sanarwa ta dakatar da kafa kamfanin sufurin jiragen saman na Najeriya ta zo ne da bazata, ganin cewa kasa da wata uku ya rage wato a watan Disamba na wannan shekara da ake ciki ta 2018 ya fara aiki.

No comments