Wani sifetan yan sanda da aka hasko shi yana rike da gwalbar giya, lokacin da ya ke bakin aiki a jihar Legas, Emmanuel Egba, ya ce ba wai shi ne ya siya don ya sha ba, ya kwace ta ne daga hannun wani matukin mota.
Sifetan ya bayyana wannan dalilin a lokacin da jaridar The Guardian ta buga hoton sa a lokacin da ya ke rike da giyar a ranar 12 ga watan Satumba, 2018.
Wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar yan sanda na jihar Legas, Chike Oti, ya ce an cafke dan sandan bayan da kwamishinan yan sanda na jihar, Edgal Imohimi, ya ci karo da hoton dan sandan a jikin jaridar.
Sai dai sanarwar ta ce dan sandan ya karyata zargin da ake masa na cewar shi ne ya sayi giyar don amfanin kasa, inda ya bayyana cewaya kwaci giyar ne tare da wasu kayan maye daga hannun wani direba a lokacin da ya tsayar da shi a bakin hanya.
Dan sandan ya ce ya kwace giyar ne saboda tsoron kada direban ya sha ya bugu, har ya zamo hatsari ga rayukan masu amfani da tituna.
Oti ya kara da cewa rundunar na ci gaba da gudanar da bincike aka wannan ikirari na dan sandar, inda ya ce idan har aka same shi da aikata laifin to kuwa zai fuskanci hukunci.

#Naija.ng

Saboda in ceci rayukan jama'a yasa aka ganni rike da kwalbar giya ina aiki>>Dan sanda

No comments