Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta yi karin haske dangane da umarnin hana amfani da wayoyin hannu a wurin zabe.
Ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito cewa an hana amfani da wayoyin kwata-kwata ba, INEC ta ce akwai bukatar ta sake fitowa ta yi karin bayani.
Hukumar ta ce ba a hana kowa zuwa wurin zabe da wayar sa ba. Amma da zarar ka shiga cikin akurkin da mai jefa kuri’a ke kebewa shi kadai ya jefa a cikin akwatin da ake tara kuri’u, to ba a yadda ka kunna waya ko ka yi amdani da ita a lokacin ba.
Kakakin Yada Labarai na INEC, Rotimi Oyekanmi ne ya yi wannan jawabi a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a yau Laraba.
Oyekanmi ya yi bayanin ne a matsayin martani ga Shugaban Jam’iyyar APC, Uche Secondus, wanda ya soki hukuncin da INEC ta yanke na hana yin amfani da wayar selula a wurin zabe.
Kakakin na INEC ya kara da cewa ’yan Najeriya na sane da irin kabulalen da INEC ke fuskanta wajen yadda a yanzu kuma cinikin kuri’u a wurin zabe ya zama ruwan dare a kasar nan.
Ya ce to wannan ne ya kawo dalilin da masu ruwa da tsaki a sha’anin gudanar da zabe suka roki INEC da ta fito da hanyoyin da a za a iya magance wannan matsala.
“Da zaran ka shiga dan akurkin da aje jefa kuri’a, ka jefa kuri’ar ka, ka fito, shikenan, ka na da damar da za ka kunna wayar ka.”
Idan ba a manta ba, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ya bayyana cewa ta na tunanin haramta shiga dakin jefa kuri’a da wayar selula.
Shugaban Hukumar ne, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a wani taro da wata kungiyar sa ido kan zabe, mai suna YIAGA ta shirya a Otal din Sheraton, ranar Juma’ar da ta gabata.
Ya bayyana duk wanda ya je rumfar zabe da nufin jefa kuri’a, to da ya karbi takardar sunayen jam’iyyun da ake dangwala wa kuri’a, za a karbi wayar sa kafin ya je ya dangwala, domin a dakile harkallar sayar da kuri’a a rumfar zabe.
“INEC za ya yi kokarin hana yin amfani da wasu na’urori da ake amfani da su a sayi kuma a sayar da kuri’un zabe, musamman wayoyin GSM.” Inji Yakubu.
Shugaban na INEC ya cewa masu yin amfani da wayoyi su na daukar hoton kati tare da jam’iyyar da suka dangwala wa kuri’a, na nuni da irin yadda ake sayen kuri’u ne, domin su nuna tabbas wadda aka saya din suka dangwala wa.
“Haka suke yi, domin bayan sun dangwala sun jefa a cikin akwati, idan sun je gida kuma suna nuna wa dillalan cinikin kuri’un ga tabbacin cewa sun zabi jam’iyyar su.
“Sai dai kuma ya ce ai akwai masu dabarar tsiya a Najeriya, domin mutum 100 zai iya amfani da hoton takardar kuri’a daya da ake yawo da ita a WhatsAPP kowa ya ce wannan ne hoton sa wanda ya dauka a lokacin da ya dangwala wa wannan jam’iyyar.”
A wurin kuma har ila yau, Yakubu ya nuna muhimmancin kara wayar wa jama’a kai dangane da illolin da ke tattare da saida kuri’a, wanda tamkar sayar da ‘yancin mutum ne ya yi da kan sa.
Sai dai kuma na yi nuni da matsalolin da ke tattare da INEC wajen gurfanar da wadanda suka karya dokokin zabe, ciki har da mai saye da mai sayar da kuri’ar sa.
Yakubu ya ce doka ta ba INEC ikon gurfanar da wadanda suka karya dokokin zabe, amma inda matsalar ta ke, kafin ka gurfanar da mutum sai ka kama shi tukunna.
“To ita INEC ba ‘yar san daba ce, kuma idan ma ta kama din sai ta yi bincike kafin ta gurfanar. Wadannan kuwa duk aikin ne na jami’an tsaro. Kenan akwai bukatar hadin-guiwa tsakanin INEC da jami’an tsaro domin hukunta masu karya dokokin zabe, ciki kuwa har da masu sayen kuri’u a ranar zabe.
Ya kuma kara da cewa hukumar na kokarin ganin ta fara gurfanar da masu daukar nauyin wasu zabubbukan ‘yan takara. Ta ce a yanzu akwai tuhume-tuhumen laifuka kan wasu da suka karya dokokin zabe sama da 100 a zabukan da suka gudana a baya.
A karshe ya ce za a tura ma’aikatan zabe 16,000 a zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar sati mai zuwa.
Premiumtimeshausa.

No comments