Adadin mutane da suke da shekaru sama da 70 a Japan ya haura kaso 20 na aadadin al'umar Kasar wanda hakan babbar barazana ce.
Kamfanin dillancin labarai na Kyodo ya fitar da alkaluman da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Japan ta bayar wanda ke nuna cewar akwai mutane miliyan 26.18 da suka haura shekaru 70 wanda yawansu ya kama kaso 20.7 na jama'ar kasar.
Al'umar Japan na ci gaba da tsufa inda a shekarar da ta gabata aka bayyana adadin a matsayin kaso 19.9.
Alkaluman sun ce, adadin masu shekaru saa da 65 kuma ya karu sama da na bara da mutane dubu 440 inda ya kama mutane miliyan 35.57 kuma kaso 28.1 na yawan jama'ar Japan din.
A karon farko mata 'yan sama da shekaru 65 a Japan sun haura su miliyan 20 a karon farko.
Wannan adadi na mata masu shekaru sama da 65 a Japan ya kama miliyan 20.12 kuma kaso 31 na yawan matan kasar.
TRThausa.

Japan na fama da karancin matasa masu jini a jiki

No comments