Wasu rahotanni daga jihar Adamawa na cewa ana can ana tattaunawa da tsohon shugaban hukumar yaki da yiwa arzikin kasa zagon gasa ta EFCC, Malam Nuhu Ribado akan ya barwa dan uwan matar shugaban kasa, Mahmood Halilu Ahmad takararshi ta gwamnan jihar inda shi kuma akamai alkawarin bashi minista kokuma shugaban hukumar kula da yankin Arewa maso gabas idan ya yadda.
Sahara Reporters tace, ta samu bayani daga wani na kusa da Ribadon inda ya tabbatar musu da cewa me gidan nashi zai iya amincewa da karbar daya daga cikin wadannan mukamai amma dai har yanzu ana tattaunawa.
Ana so dai a samu hadin gwiwa me karfi dan kayar da gwamna Jibrilla Bindow a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar.
Rahotanni dai sun bayyana cewa, kwamitin gudanarwa na APC yana goyon bayan dan uwan A'isha Buharin haka kuma mutane irin su tsohon gwamnan Borno da Legas, Buba Marwa da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da sauran wasu manyan mutane na yankin shi suke goyawa baya.

An yiwa Nuhu Ribado tayin mukamin minista dan ya barwa dan uwan A'isha Buhari takarar gwamnan Adamawa

No comments