Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma daya daga cikin masu neman jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar shugaban kasa, ya ce Najeriya na cikin mawuyacin halin rashin lafiya da take bukatar ‘yan kasa nagari su gaggauta ceto rayuwarta.
Lamido na wannan kalami ne jiya, Litinin, a Abuja, ga manema labarai bayan kamala ganawa da wakilan kungiyoyin kudu da tsakiyar Najeriya.
Kazalika, tsohon gwamnan ya bukaci ‘yan majalisar tarayya da su tsige Buhari saboda laifukan yiwa kundin tsarin mulkin kasa karan tsaye.
“Duk abinda ke faruwa yanzu, na faruwa ne saboda Najeriya bat a da lafiya. Najeriya na bukatar shugaba da zai tafi da duk ‘yan kasa ba tare da nuna kabilanci ko bangaranci ba,” a kalaman Lamido.
Sannan ya kara da cewa, “tafiyar da harkokin gwamnati na fuskantar barazanar lalacewa a karkashin wannan gwamnati, shi yasa ake ta aiiyukan ta’addanci da kashe-kashe a Taraba, Adamawa, Zamfara da ragowar sassan Najeriya."
Kazalika, Lamidon ya zargi Buhari da yunkurin binne irin gudunmawar da mazan jiya suka bayar wajen gina Najeriya, mutanen da ya ce Buhari ko kafar su bai kama ba idan ana maganar gaskiya da rikon amana.
“Tun kafin zuwan Buhari akwai mutane masu kima da gaskiya, akwai Tafawa Balewa, Obafemi Awolowo, Aminu Kano, da Azikiwe, wadannan mutane babu wanda ke tantama a kan rikon amanrsu da dattako. Ko sau daya Buhari bai taba yabawa gudunmawar su ba,” a cewar Lamido
Naija.ng.

Sule Lamido ya lissafa ‘yan Najeriya da suka fi Buhari gaskiya da kima

No comments