Wasan da aka buga tsakanin Kasashen Sifaniya da Ingila, jiya, Asabar, ya kare da sakamon 2-1, Inda Sifaniyar ta yi nasara akan Ingila, saidai wani lamari da ya dauki hankulan mutane shine ihun da aka rikawa Sergio Ramos a filin.
'Yan kallo a filin wasan Wembley sun rika wa Ramos Eho a duk lokacin da ya taba kwallo saboda nuna jin haushinsu akan muguntar da ya yiwa Mohamed Salah a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai da aka buga wanda yayi sana diyyar karyewar Salah din.
Bayan kammala wasan,Ramos ya shaidawa manema labarai cewa, Banso ace irin wannan tarbar aka min ba, ya kara da cewa, sun tuna da abu da ya daya faru a wasan karshe amma babu wanda ya tuna da barazanar kisa da aka min ni da iyali na ba, kamar yanda Givesport ta ruwaito.

Yanda akawa Ramos Ihu a Ingila saboda abinda yawa Salah da kuma abinda yace bayan wasa

No comments