Wannan mutumin dan kasar India me suna Dadarao Bilhore ya dukufa yana ta gyara ramukan dake kan titi tun bayan da danshi me suna Prakash ya fado daga kan mashin/babur sadiyyar haka ya fasa kai kuma daga baya ya mutu.
Shekaru 3 kenan da faruwar hakan kuma tun wancan lokaci mutumin yake cike ramuka inda yace yawan ramukan da ya cike sun kai 600 a Babban birnin kasar ta India Mumbai kamar yanda Buzzfeed ta ruwaito.
Shekaru 3 kenan da faruwar hakan kuma tun wancan lokaci mutumin yake cike ramuka inda yace yawan ramukan da ya cike sun kai 600 a Babban birnin kasar ta India Mumbai kamar yanda Buzzfeed ta ruwaito.
Rahoton yace ramukan kan titi na daya daga cikin matsalolin da kasar ta India ke fama dasu kuma a shekarar 2017 akalla mutane 10 na mutuwa kullun dalilin wannan matsalar.
No comments