Wani abin al'ajabi ya faru da wata mata 'yar kasar Ingila da taje kasar Sifaniya yawan shakatawa, matar ta fara korafin cewa tana jin ciwo a al'aurarta, dan haka ta nufi asibiti dan ganin likita.
Koda likitoci suka duba sai suka ga mataccen kunkuru a al'aurar tata, hakan yasa suka maza-maza suka kira 'yansanda.
Matar wadda ba'a bayyana sunanta ba ta bayyanawa 'yansanda cewa itama batasan yanda akayi kunkurun ya shiga jikinta ba.
Jaridar The Sun data ruwaito wannan labari tace labarin ya watsu sosai a kafafen labaran kasar ta Sifaniya saidai ita bata samu sahihan rahotanni da suka tabbatar da faruwarshi ba saboda ta tuntubi asibitin da aka ce an duba wannan mata amma sunce ba zasu iya cewa komai akai ba saboda dokar sirrin bayanan marasa lafiya.
Haka kuma sunyi kokarin samun hukumar 'yansanda amma hakan bata yiyuba.
No comments