Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa ta na tunanin haramta zuwa rumfunan zabe dauke da wayoyin hannu.
Shugaban Hukumar ne, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a wani taro da wata kungiyar sa ido kan zabe, mai suna YIAGA ta shirya a Otal din Sherato, ranar Juma’ar da ta gabata.
Ya bayyana duk wanda ya je rumfar zabe da nufin jefa kuri’a, to da ya karbi takardar sunayen jam’iyyun da ake dangwala wa kuri’a, za a karbi wayar sa kafin ya je ya dangwala, domin a dakile harkallar sayar da kuri’a a rumfar zabe.
“INEC za yay i kokarin hana yin amfani da wasu na’urori da ake amfani da su a sayi kuma a sayar da kuri’un zabe, musamman wayoyin GSM.” Inji Yakubu.
Shugaban na INEC ya cewa masu yin amfani da wayoyi su na daukar hoton kati tare da jam’iyyar da suka dangwala wa kuri’a, na nuni da irin yadda ake sayen kuri’u ne, domin su nuna tabbas wadda aka saya din suka dangwala wa.
“Haka suke yi, domin bayan sun dangwala sun jefa a cikin akwati, idan sun je gida kuma suna nuna wa dillalan cinikin kuri’un ga tabbacin cewa sun zabi jam’iyyar su.
“Sai dai kuma ya ce ai akwai masu dabarar tsiya a Najeriya, domin mutum 100 zai iya amfani da hoton takardar kuri’a daya da ake yawo da ita a WhatsAPP kowa ya ce wannan ne hoton sa wanda ya dauka a lokacin da ya dangwala wa wannan jam’iyyar.”
“Don haka mu na duba yiwuwar shaida wa duk wani mai wayar hannu ta zamani cewa kada ma ya zo da waya a rumfar zabe.”
A wurin kuma har ila yau, Yakubu ya nuna muhimmancin kara wayar wa jama’a kai dangane da illolin da ke tattare da saida kuri’a, wanda tamkar sayar da ‘yancin mutum ne ya yi da kan sa.
Sai dai kuma na yi nuni da matsalolin da ke tattare da INEC wajen gurfanar da wadanda suka karya dokokin zabe, ciki har da mai saye da mai sayar da kuri’ar sa.
Yakubu yace doka ta ba INEC ikon gurfanar da wadanda suka karya dokokin zabe, amma inda matsalar ta ke, kafin ka gurfanar da mutum sai ka kama shi tukunna.
“To ita INEC ba ‘yar san daba ce, kuma idan ma ta kama din sai ta yi bincike kafin ta gurfanar. Wadannan kuwa duk aikin ne na jami’an tsaro. Kenan akwai bukatar hadin-guiwa tsakanin INEC da jami’an tsaro domin hukunta masu karya dokokin zabe, ciki kuwa har da masu sayen kuri’u a ranar zabe.
Ya kuma kara da cewa hukumar na kokarin ganin ta fara gurfanar da masu daukar nauyin wasu zabubbukan ‘yan takara. Ta ce a yanzu akwai tuhume-tuhumen laifuka kan wasu da suka karya dokokin zabe sama da 100 a zabukan da suka gudana a baya.
A karshe ya ce za a tura ma’aikatan zabe 16,000 a zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar sati mai zuwa.
Premiumtimeshausa.

2019: Akwai yiwuwar INEC za ta hana zuwa rumfar zabe da wayoyin hannu

No comments