Jerin laifukan cin hanci 5 da suka gagari EFCC

Duk da irin jajircewa da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari keyi wajen yaki da rashawa ta hanyar amfani da hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati (EFCC), gwamnatin ta samu koma baya a lokuta da yawa ta hanyar rashin nasara a kotu, wasu lokutan kuma wadanda ake zargin su daukaka kara.
Wasu daga cikin shari'ar da gwamnatin ta sha kaye sun hada da
1) Shari'ar tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa
2) Shari'ar yar uwar tsohon shugaba Jonathan, matar Aziboala Robert
3) Shari'ar Justice Hyeladzira Ajiya Nganjiwa,
4) Shari'ar Justice Adeniyi Ademola da
5) Shari'ar Patience Jonathan, uwargidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
A shari'ar Attahiru Bafarawa da wasu mutane biyu, babban kotun Sakkwato ta wanke Bafarawa daga zargin laifuka 22 da EFCC tayi zargin ya aikata.
Babban kotun tarayya da ke Abuja itama ta wanke matar dan uwan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Aziboala Roberts, Stella daga zargin laifuka biyu cikin 9 da EFCC ke zarginta da aikatawa na karkatar da kudi $40 miliyan.
Bayan tafka muhuwara kan sumame da aka kai gidajen alkalai da jami'an DSS su kayi, wata kotun Legas ta wanke Justice Hyeladzira Ajiya Nganjiwa daga zargin da ake mata saboda tsaron da doka ta bata.
Kazalika, babban kotun Abuja ta wanke tsohon Alkalin kotun tarayya, Justice Adeniyi Ademola and da matarsa, Olubowale daga zargin aikata wasu laifuka 18 da EFCC ta shigar a 2017 duk da cewa EFCC tayi alkawarin daukaka karar.
Wata babban shari'a da EFCC ta rasa itace shari'ar Patience Jonathan inda kotu ta hana kwace kadarorin Patience tare da umurtar EFCC ta bude asusun ajiyar Patience Jonathan 16 da ta kulle da ake zargin akwai $5.9 miliyan a ciki.
Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya ce hukumar tayi karo da matsaloli ne wajen shari'ar wadanda ta ke tuhuma saboda suna bullo da dabarbarun tsawaita shari'ar kuma alkalai na amincewa da wadannan dalilan.
Ya kuma ce hukumar na fuskantar karancin lauyoyi da kudade.
Naija.ng.

Related Posts

No comments