Wata gambizar masanar kasashen Amurka,Sin da Italiya sun gano yadda zasu iya maida hamadar sahara dokar daji mai rukuki wanda ke cike makil da itatuwa tsanwaye shar.
Masanan sun sanar da cewa suna iya dawo da rayuwa ta hanyar kafa katafarun fankoki a tsakiyar hamada,da zummar a amfani da iskar wajen samar da lantarki,wanda haka zai ninka yawan hadarin da ake a ire-iren wadannan yankunan sau biyu.
An wallafa wannan labarin a mujallar fasaha ta "Science".
Da suke bayani,masanan sun ce zasu kafa fankokin a hamadar Sahara wacce ke da fadin murababbin kilomita milyan 9.Idan har suka cimma wannan manufar tasu, duniya za ta tanadi isasshen makamashin da za ta ci gaba da amfani da shi har illa mashallah.
TRThausa.

Masana sun gano yadda za su maida sahara tsanwa shar

No comments