Wani babban likita a tsarkakken birnin Makkah na kasar Saudiyya ya maka shugaban wata kungiyar Whatsapp, da aka fi sani da Whatsapp Group kotu,sabili da ya bata masa lokaci ta hanyar aika masa sakonni marasa kangado.
A cewar kafar yada labarai ta NTV,likitan wanda bai so a bayyana sunansa ba,ya dauki wannan matakin ne da zummar hukunta shugaban,saboda yayi sakaci sosai,wanda hakan yasa mambobin kungiyar suka dinka aika sakonni marasa alfano da kuma bannata masa lokaci.
Likitan wanda ya garzaya babban kotun Makkah don kai kukansa, yayi kacibus da wani kalubale,saboda dokokin kasar Saudiyya ba su tanadi wata hanya a shari'ance wacce za a iya amfani da ita don warware ire-iren wadannan matsalolin.
Da suke bayani a gaban manema labarai, kwararru a harkar shari'a na Saudiyya sun tattabar da cewa, babu wata ayar dokar da ke iya hukunta wanda ake tuhumar.
Tuni,dubban Saudiyyawa daga sassa daban-daban na kasar suka yi caa kan wanda ya kai kara.
Wasu masu amfani da shafuka sada zumunta na kasar,sun soki lamirin likitan,inda suka ce,
"Ai ba dole ba ne sai ka karanta sakonnin.In dai zasu hana ruwa guda a lamurranka,zaka iya fita da kungiyar".
TRThausa.

An kai wani me gudanar da Whatsapp Group kotu saboda aika sakonni marasa ma'ana

No comments