Wata mata ta biya dubu 10 an kashe mijinta saboda ya yi mata kishiya
Rundunar yan sanda jihar Osun ta kama wata mata mai suna Omotayo Salawudeen, yar kimanin shekaru 39, bisa zargin biyan kudi a kashe mijinta, Alhaji Salawudeen Hakeem mai kimanin shekaru 43 saboda ya yi mata kishiya
Kwamishinan yan sanda na jihar Olafimihan Adeoye, yace matar ta dauki hayar wani tsagera mai suna Osogbo a inda ta biyashi N10,000 ya kashe mijin nata saboda ya kara aure. Bayanai sunce matar ta gayyaci tsageran ya buya a cikin gidanta har zuwa lokacinda mai gidan nata margayi Hakeem ya dawo gida.
Hausa times ta ruwaito margayin yana dawowa ya kwanta barci sai matar ta sanya matashi (pillow) ta danne masa fuska a yayinda tsageran da ta dauko ya fito daga inda ya buya ya sokawa mijin nata wuka a kirji kuma a nan take ya mutu.
Kwamishinan ya cigaba da bayyana cewa bayan da matar ta fita tana kururuwar neman dauki bisa karyar cewa wasu makisa sun kashe mijinta sai daya daga cikin yan'uwan margayin Engineer Salawudeen Jimoh ya garzaya ogishin yan sanda dake unguwar ya sanar dasu halin da ake ciki.
Hausa times ta samu rahoton asirin matar ya tonu ne bayan da rundunar yansandan ta dukufa yin bincike game da faruwar lamarin. Yanzu haka dai kwamishinan yan sandan yace suna cigaba da bincike akai kuma zasu gurfanar da wacce ake zargin a kotu da zaran sun kammala.
Me zaku CE? Me ya kamata ayi?

No comments