Jami’an kwastam na Najeriya sun kwace wadansu manyan motoci mallakar mawakin jam’iyyar APC Dauda Kahutu Rarara da yake aikin sumogal dinsu ta kan iyakokin da aka haramta a tsakanin Najeriya da kasar Benin da Nijar.

Rahotannin farko-farko sunce an kame motocin ne kirar fijo-fijo da toyota-toyota a jihohin Zamfara da Sakwato kuma aka kawo su Kaduna.
WASU gwamnonin APC guda uku suna ta ban baki ga shugaban kwastam Hamidu Ali cewa kayan dan jam’iyya ne, don haka a rufe maganar a sallamesu.

KWASTAM dai suna kama kayan marasa galihu su rike daga karshe su yi gwanjonsu, kuma babu wanda ya isa ya samu alfarma. ZAMU JI ko shima RARARA za a yi masa irin wannan walankeluwa tunda uwarsu tana gindin murhu, irin yadda aka yi wa sakataren gwamnatin tarayya Babachiri Lawal. Ya cinye kudin ‘yan gudun hijira,an same shi da laifi, amma shiru kamar an aiki bawa garinsu.

Jami’an Kwastam Sun Kama Mawakin Siyasa Rarara

No comments