Wato abin al’ajabi da ban haushi baya karewa a duniyar nan ta Maliki Yaumid-dini. Kuma in har da ranka, to, fa babu abinda ba za ka ji ko ka gani ba. Dama ai an ce “Inda Ranka Ka Sha Kallo”
Cikin labaran da za su saka takaici, shi ne na wani malamim wata makarantar sakandire da ya yi wasu dalibai ‘yan mata zindir, haihuwar uwa, sannan ya sa suka kwanta cikin turbaya kana ya sa bulaliya ya zane musu jikinsu, kawai wai don sun makara zuwa makaranta
Wannan labari da jaridar Nigerian Bulletin ta rawaito sun ce sun samu birbishinsa ne daga shafin facebook na wani Song Mudoh inda ya rubuta cikin harshen turanci cewa “A tube ‘yan mata ‘yan makaranta tunbur sannan aka zanesu a kasar Kamaru wai kawai don sun makara zuwa makaranta
“A Afurka kadai ne irin wannan abin takaicin zai faru. Wai a ce a tube dalibai ‘yan mata sannan a zanesu wai duk a matsayin hukunci. Babu ruwana da koma wane irin laifi suka yi, amma hukuncin sam bai dace ba. Kuma suma daliban abin kunya ne a garesu da suka amince aka aikata irin wannan bakin hukunci akansu”
Bincike ya gano cewa wannan abu ya faru ne a wata makarantar gwamnati a garin Baham, a yankin Arewacin Kamaru
Ga hotunan:

www.hausamini.com
No comments