Ma’aikata na ofishin uwargidan shugaban kasar sun tabbatar da hakan a ranar Litinin, 7 ga watan Agusta cewa uwargidan shugaban kasar ta koma Landana, a ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta.
Uwargidan shugaba Buhari ta dawo gida Najeriya daga birnin Landan a ranar Alhamis da ta gabata sannan kuma ta tafi Owerri, babban birnin jihar Imo, inda ta halarci taron watan Agusta 2017 da matan jihar suka shirya.
Wasu daga cikin ma’aikatan ta sun bayyana cewa aikwai yiwuwar dawowarta kasar tare da maigidanta a lokaci da ba’a tabbatar ba tukuna.
Kamar yadda HAUSATOP ta rahoto a baya, shugaba Muhammadu Buhari ya bar kasar zuwa birnin Landan a ranar 7 ga watan Mayu don ci gaba da jinya tare da likitocinsa.
Ya tabbatar da cewa yana samun sauki sosai sannan kuma zai dawo gida Najeriya don ci gaba da aiki da zaran likitocin sa sun basa damar yin haka.

Aisha Buhari Ta Sake Komawa Birnin Landan Akwai Yuwuwar Dawowar Su Tareda Buhari

No comments