Ana zargin wasu makiyaya 'yan fulani da laifin yiwa wata tsohuwa Akinseye, mai shekaru 72 a duniya fyade, har ta fita daga hayyacinta a cikin gonar ta a unguwar Ore ta karamar hukumar Odigbo dake jihar Ondo
A yayin da wannan tsohuwa take bayyanawa manema labarai irin ibtila'in da ya afka ma ta hannun wannan 'yan ta'adda, ta ce, tana cikin aiki a gonar ta ne a yayin da wasu makiyaya na fulani guda biyu suka yi ma ta ta karfi daya bayan daya.
Shafin DAILY POST ya ruwaito ta sanadin wannan tsohuwa, "Ina cikin aiki a gona ta lokacin da mutum biyu suka fado gonar, kafin na ankara wajen tambayar ko meke tafe dasu, ban yi aune ba suka daure min baki kuma suka yage kayan dake jina, kuma kowannen su ya shige ni daya bayan daya.
Sun yi min barazanar kisa idan nayi wani abin da zai jayo hankalin jama'a kuma suka kama gabansu inda suka barni cikin zulumi da ciwo".
Faruwar wannan abu ne ya sanya matasan yankin, karkashin kungiyar matasan jihar Ondo da ta manoma a kananan hukomin 18 na jihar, suka yi zanga-zanga.
Matasan da suka yi zanga-zangar, sun yi barazanar daukar doka a hannun su in har gwamnatin jihar da hukomomin tsaro na jihar ba su tashi tsayen akan wannan abu ba cikin gaggawa.
Shi kuwa wani wakilin wannan kungiya, Oluwatuyi Adekanmbi, ya bayyana cewa, makiyaya sun tsokano tsuliyar dodo sanadiyar sa hannunsu a laifi daban-daban a jihar, kama daga laifin fyade, garkuwa da mutane, kashe-kashe da sauran ta'addaanci.
Ya ce, "An kashe daya daga cikin manomansu, Orimisan Omowole, a gonar sa ta karamar hukumar Odigbo ta jihar Ondo, kuma aka ciro zuciyarsa aka dora ta akan kirjin sa bayan ana kashe shi."
"Mu bamu hana a yi kiwo ba kuma bamu ce gwamnati ta kaddamar da dokar hana kiwo ba, amma abinda muke so shine, idan aka cigaba da kiwo hakan yana janyo koma baya wajen harkokin noma domin kuwa dabbobin suna shiga gonaki su na yi ma na barna."
© Naij
No comments