ya kuma zargi gwamnatin Kano da daukar nauyin masu yada jita-jitar komawarsa PDP
Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya karyata jita-jitar dake yaduwa cewa da shi da wasu ‘yan majalisu sun sauya sheka daga APC zuwa PDP.
Da yake magana da majiyarmu ta ‘Daily Nigerian’ a safiyar yau Talata, shugaban ma’aikatan Sanatan, Aminu Abdulsalam, ya ce babu kanshin gaskiya a labarin kuma labari ne mara tushe.
Kamar yadda ya ce Sanata Kwankwaso da shi da magoya bayansa ba su da niyyar sauya sheka zuwa wata jam’iyyar a ko yaushe.
Ya ce gwamnatin Kano ce ta dauki nauyin yada jita-jitar saboda sun ga uwar jam’iyyar APC ta kasa ta tabbatar da Umar Doguwa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na Kano.
Aminu Abdulsalam ya ce wannan ba shine karo na farko da gwamnatin Kano take daukar nauyin yada irin wadannan jita-jitar ba don ganin ta batawa Sanatan suna.
No comments