Watan Agusta ya zo da ruwan fina finai masu
kayatarwa, daga masana'antar shirya finan finan
hausa da a ke kira "Kannywood", da masu kallo
ya kamata su nema don nishadin su.
1. Mata ta ce Shaida
Labari ne na wani magidanci da ke fuskantar
tuhuma a gaban bisa zargin aikata laifin kisan
kai, magidancin ya kasance bashi da wata
shaida da zai gabatar domin gamsar da kotu a
kan ba shi ya aikata laifin ba sai matar sa, hujja
da a yawan lokuta kotu bata karba. Shin ko kotu
za ta yi amfani da matar sa a matsayin shaida
domin wanke shi daga zargin aikata laifin kisan
kai?
2. Karamci
Shiri ne da yake nuna halayyar wasu iyaye
wajen yi wa 'ya'yan su zabin abokin zaman
aure.
3. Yar' Duniya:
Labarin wata tsintacciyar yarinya ce da wasu
ma'aurata suka dauko daga gidan raino saboda
basu samu haihuwa ba. Yarinyar ta taso cikin
wadata da jin dadi, saidai bayan girmanta
halayenta sun munana, sun saba da irin
tarbiyyar da iyayen rikon nata suka bata.
4. Mijin yarinya:
Shirin yana nuni kan halin kunci da takura da
'yan mata masu karancin shekaru ke fuskanta
wurin manyan 'ya'yan kishiyoyi yayin da aure ya
kai su gidan yawa.
5. Mansoor:
Shirin Ali Nuhu da tuni a ka nuna shi a manyan
sanimomi tun karamar sallah. Labari ne da yake
nuna halin tsangwama da kyama da yaran da a
ka haifa babu aure ke fuskanta a rayuwa duk
da kasancewar ba su suka zabi zuwa duniya ta
wannan hanya ba.

No comments