Bincike ya nuna cewa jami’an tsaro sun kama shahararren marubucin nan da ya saba fashin baki akan al’amuran ta’addancin Boko Haram Datti Assalafy tun makonni uku da suka gabata.
Shi dai Datti Assalafiy mutum ne da ya saba rubuce rubuce akan al’amura da suka shafi tsaro inda yake bayyana fahimtar sa akan ta’addanci da kuma yanda yake ganin za’a iya magance su. Kamar yanda binciken mu akan shafin sa na facebook ya nuna.
To amma makonni uku da suka gabata, wasu dakarun sojoji sun je wurin aikin na Datti suka tafi dashi wurin da kawo yanzu ‘yan uwansa basu san inda yake ba.
A wani zantawa da wakilin mu Mahmud Isa Yola yayi da dan uwan Datti Assalafy ta wayar tarho, dan uwan nasa ya bayyana cewa suma daga baya ne suka samu labarin kama Datti.
Dan uwan na Datti yace: “Mu dai abunda muka sani shine an tafi dashi ne a ranar alhamis 19/07/2017. Kafin sannan yazo yayi hutu a gida kamar yanda ya saba kowani karahen mako. Bayan ya koma wurin aiki ranan litinin, ranan talata sai sojojin suka zo suka tattauna dashi (interview) kuma suka karbi wayoyin sa. Daga bisani ranar alhamis sai suka sake zuwa suka dauke shi zuwa inda har yanzu bamu sani ba,” inji dan uwan na Datti.
Shima mahaifin Datti da ya zanta da wakilin mu yace har yanzu bai san ina ne aka kai Datti ba, kuma layukan shi basa tafiya. Yace wani lokacin suka samu wayar ta sa amma babu wanda yake dagawa.
Mahaifin na Datti yace tun tasowar dan shi bai sanshi da wani abu ba illa son addini da kuma mutane.
Bincike da muka gabatar a shafin Facebook na Datti ya nuna cewa yafiye yin rubutu akan Boko Haram inda galibi yakan yi zafafan kalamai akan su, kana kuma a wasu lokutan yakan fadi hanyoyi da yake gani ya dace a magance matsalar. Kazalika wasu lokutan yakan fitar da rubutu da suke dauke da bayanai masu karfi akan Boko Haram ko kuma abunda ya shafe su.
Datti, wanda jami’in dan sanda ne kuma mai bada karatu a wata makarantar horas da ‘yan sanda yayi rubutu a ranar litinin din da aka kama shi inda yayi wa rubutun take “SUN MAYAR DA TA’ADDANCI HANYAN NEMAN KUDI”. a cikin rubutun, Datti ya bayyana cewa bai yadda jami’an ‘yan sanda ne aka kama ba, amma ya yadda cewa tabbas an kama matan. Su dai matan sun fada hannun Boko Haram ne a cikin garin Borno inda suka yi musu kwanton bauna.
Haka ma a ranan 11 ga watan da ta gabata yayi rubutu akan bidiyo da Boko Haram din ta fitar na farfaganda inda yace sun tura mishi ta hannun Albarnawey link din da za’ayi downloading. Ko kafin wannan lokaci yayi ikirarin cewa akwai yuwuwar sakin bidiyon.
Bincike ya nuna cewa, akwai wasu dake amfani da fakaitattun sunaye suna kalubalantar rubuce rubucen datti a matsayin suna ‘yan Boko Haram. Wasu lokutan sukan yi masa barazanar mutuwa, wasu lokutan kuma su yi comment da zafafan kalamai akan shi.
Bisa abunda ya bayyana akan Datti a shafin sa, alamu sun nuna cewa yakan boye adireshi da asalin sunan shi wanda wasu ke ganin yana haka ne saboda wadanda yake rubuce rubuce a kansu.
Datti dai yana da mabiya sama da mutum 15,000 a shafin sa na Facebook.
Tuni dai mabiyan rubuce rubucen sa suka fara korafin kama marubucin inda suke ganin hakan bai dace ba.

Jami’an Tsaro Sun Kama Mai Fashin Baki Akan Boko Haram, Datti Assalafy

No comments