Shahararre kuma tsohon jarumin wasan Hausa fim Aminu Sharif wanda aka fi sani da Momoh ya fito yayi aman wuta tare da yin tofin Allah tsine ga yawan raye rayen da ake yi a mafi yawan wasannin Hausa Fim inda ya bayyana cewa basu da wani anfani.
Shahararren dan fim din Aminu Momoh ya yi wannan furucin ne dai cikin wata fira da yayi da wata majiyar mu inda jarumin yace tabbas mutum zai iya shirya fim din sa ya kuma yi kasuwa ba tare da an sa waka a ciki ba.
HAUSATOP ta samu labarin cewa a cikin firar dai dan jaridar ya tambayi jarumin ko meye matsayin sa akan rawa da waka a fina-finai? Sai ya kada baki yace ai rawa da waka kwata-kwata ba al’adar mu bace ba kuma suma indiyawan da aka kwafo ta daga gare su suma ba al’adar su bace.
Da jaridar ta sake tambayar sa ko ya taba shirya fim wanda yake da rawa a ciki sai ya kada baki ya ce a cikin fim sama da goma da yayi a kwanan nan bai fi fim daya ko biyu ba da ya sa waka a ciki.

Rawa Da Waka Basu Da Wani Amfani A Fim Din Hausa – Aminu Sharif Momo

No comments