A kokarin ta na ganin maniyyata sun yi aikin hajji cikin saiki, Hukumar Alhazai ta Naijeriya (NAHCON) ta sanar da isowar ruwan zamzam ga maniyyatan aikin hajji na bana daga kasa mai tsarki.
An sauke kawowar farko a jihar Gombe.
Hukumar wacce ta bayyana haka a wata takaddar manema labarai da ta fitar, wanda ke dauke da sanya hannun shugaban yada labaranta Malam Uba Mana, tace matakin na kawo ruwan zamzam tun kafin mahajjata su tafi anyi shi ne saboda kawo karshen matsalolin da mahajjata ke samu wajen dawo da ruwan na Zamzam gida bayan aikin hajji.
Wannan shiri zai bawa kowane mahajjaci daman karban lita biyar na zamzam yayin da ya dawo daga kasa mai tsarki. Ko wane mahajjaci dan Nijeriya za’a bashi ruwan na zamzam kilogram biyar yayin da suka dawo daga Saudiyya.
Idan ba’a manta ba dai, bara ne hukumar ta alhazan ta fara kawo ruwan na zamzan kasar Nijeriya kafin tashin maniyyata daga kasa mai tsarki.
Hukumar tace a shekarar da ta gabata ta kawo ruwan Zamzam din kimanin lita 68,000 kafin kammala tashin mahajjata.
Zuwa yanzu dai, alhazan Nijeriya 17,000 daga jihohi 9 ne suke kasa mai tsarki saboda gabatar da aikin na hajji.

Hajjin Bana: Ruwan Zamzam Daga Kasa Mai Tsarki Ya Iso Nijeriya

No comments