Wasu rahotanni daga jihar Adamawa na cewa ana can ana tattaunawa da tsohon shugaban hukumar yaki da yiwa arzikin kasa zagon gasa ta EFCC, Malam Nuhu Ribado akan ya barwa dan uwan matar shugaban kasa, Mahmood Halilu Ahmad takararshi ta gwamnan jihar inda shi kuma akamai alkawarin bashi minista kokuma shugaban hukumar kula da yankin Arewa maso gabas idan ya yadda.
Sahara Reporters tace, ta samu bayani daga wani na kusa da Ribadon inda ya tabbatar musu da cewa me gidan nashi zai iya amincewa da karbar daya daga cikin wadannan mukamai amma dai har yanzu ana tattaunawa.
Ana so dai a samu hadin gwiwa me karfi dan kayar da gwamna Jibrilla Bindow a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar.
Rahotanni dai sun bayyana cewa, kwamitin gudanarwa na APC yana goyon bayan dan uwan A'isha Buharin haka kuma mutane irin su tsohon gwamnan Borno da Legas, Buba Marwa da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da sauran wasu manyan mutane na yankin shi suke goyawa baya.

An yiwa Nuhu Ribado tayin mukamin minista dan ya barwa dan uwan A'isha Buhari takarar gwamnan Adamawa

Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon na daya daga cikin wadanda suka samu zuwa kasa me tsarki wajan aikin Ibada, ta bayyana cewa, tana kewar masallacin Harami a wani sako da ta fitar ta dandalinta na sada zumunta.

Ina kewar masallacin Harami>>Hadiza Gabon

Jarumar fina-finan Hausa, Bilkisu Shema kenan a wannan kayataccen hoton nata inda take tare da 'yar uwarta, tubarkallah sun sha kyau, muna musu fatan Alheri.

Kalli kayataccen hoton Bilkisu Shema tare da 'yar uwarta

Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango kenan a wannan kayataccen hoton nashi da ya haskaka, muna mishi fatan Alheri.

Adam A. Zango dan kwalisa

Maryam Yahaya ta yiwa Rahama Sadau tallar jan baki
 Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya ta yiwa abokiyar aikinta, Rahama Sadau tallar jambakinnan nata na Sadau ta dandalinta na sada zumunta, ta yi amfani da kayatattun hotuna wajan yin tallar.





Maryam Yahaya ta yiwa Rahama Sadau tallar jan baki

Sabuwar wakar abdul d one kenan Mai suna ” Bani Fushi Kan So ” waka mai ratsa zuciyar masoya da masu sauraren wakokin soyayya ko basu bara soyayya ba kai abdul d one ba dama.
Kawai da abin da zance kada ku bari wannan wakar ta wuceku maza ku saurareta domin nishadantarwa.
GA KADAN DAGA BAITIN WAKAR:-
– Bani fushi kan soyayya ganin akwai ka a rai
– Nima nasan lallai na dace da mai share kuka
– Masoyi ka zamo rabin jiki
– Samun kane chikar farin ciki
– Rashinka zaihani cin abinci
– Yaka zo zo guna
– Maza kamo hannuna muje zuci kai ta aje
– Saboda kai nai aso bani so ka guje
– Abin da ke bata ranka korarshi nake
– Kazamo farin ciki mai kauda bakin cikina
Kunji kadan daga baitin wakar abdul d one mai suna Bani fushi gaskiya wakar tayi dadi sosai.


Sabuwar wakar abdul d one kenan Mai suna ” Bani Fushi Kan So

Sabuwar wakar hamisu breaker mai suna ” Zo Da Farin Ciki ” waka mai ratsa zuciyar masoya yayin da suke saurarenta harma sai sun dan taka ko sun bita.

Downlord mp3

Sabuwar wakar Hamisu Breaker -Zo DA Farin Ciki

Barkan mu da wannan lokaci masoya wakokin Umar m Shereef yauma Kamar Kullum mawakin naku ya zo muku da sabuwar wakar sa me suna So Hakayake.

Downlor mp3

#wakoki.com.ng

Umar M Shereef -So Hakayake

Sabuwar Wakar Abdul D One me suna Nakamu da ciwo wannan wakar Yayi tane game da yayani na soyayya da ya fada
GA KADAN DAGA CIKIN BAITOCIN WAKAR
– Nakamu da ciwo kece magani
– Ke akawa kauna Dan Allah zokije dani
– Tarko na fada ni
Taya zaki fiddani
– Lafiya kiyi mini gani
– Faruwar hakanne tunani.

Downlord Audio

#wakoki.com.ng

Abdul D One -Nakamu Da Ciwo

DJ Ab – Anzo Wajen, Iconic Northern Nigerian hip-hop star, DJ Ab comes with a brand new hit single entitled “ Anzo Wajen” .
Anzo Wajen comes months after the release of his last single tagged Bomba Man.

Downlord Audio here

#hausatop

Dj A.b – Anzo Wajen

Rapper Morell all the way from Northern Nigeria dishes out a new single titled “ Haba“.
The Hausa Hip Hop act, Morell is out again with this spanking single ‘ Haba ’ which was produced by Kahli Abdu and it was laced in hausa for his Northern fans.
Listen & Download “Morell – Haba” below:-

Downlord video

Morell – Haba (Official Video)

New Album ClassiQ – New North (EP)
New North (EP) is a studio album by Nigerian recording artist ClassiQ which was released through Arewa Mafia on September 21, 2018.
The Album houses 8 complete track with feature appearances from Ckay , Ice Prince ,
Yung L, M.I Abaga , and other talented artists.
The production list was also released with talents such as TUC, Supersonic , G-Plus Chang , Reinhard Tega , and others.
ClassiQ New North Album Tracklist Below;

1. Bad Man (Karya Su Ke)

Downlord mp3

2. Gargajiya

Downlord mp3

3. Sai Godiya

Downlord mp3

4. Manager ft Ckay

Downlord mp3

5. Up and away ft Ice prince

Downlord mp3

6. Sharp sharp

Downlord mp3

7. Binta

Downlord mp3

8. Wonder me ft Youngh L

Downlord mp3

©Arewarulers.com

New Album ClassiQ – New North (EP)

Ina so in haihu da yawa nima in dauki irin wannan hoton>>Dan majalisa Abdulmumini Jibril
Dan majalisar wakilai, Abdulmumini Jibril ya saka wannan kayataccen hoton iyalin a dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda ya bayyana cewa ya kayatar dashi sosai kuma wata ran shima zai so ya dauki irin wannan hoto da iyalinshi.
Ya kara da cewa, yana so ya haihu da yawa kuma ya kagara yaga ranar da zai dauki irin wannan hoto shima, a karshe ya yiwa wannan iyali fatan Alheri.

Ina so in haihu da yawa nima in dauki irin wannan hoton>>Dan majalisa Abdulmumini Jibril

SHARWARWARI>>Daga Malam Aminu Daurawa
🌹= Kafin kayi rubutu kayi nazari akai;
🌹= Kafin kayi magana kayi tunani akai; 🙉
 ðŸŒ¹= Kafin ka yanke hukunci kayi bincike akai;
 ðŸŒ¹= Ba kowacce magana ake yarda da ita ba;
🌹= Kuma ba kowacce ake karyatawa ba;
 ðŸŒ¹= Kafadi Alkairi ko kayi shiru;
🌹= Ka yawaita aikata Alkairi fiye da sharrii;
 ðŸŒ¹= Ka yawaita kyakyawar addu'a fiye da mummuna;
 ðŸŒ¹= Ba kowa bane mutumin kirki kuma Ba kowa bane mutumin banza;
🌹= Kada ka zagi kowa kuma in an zageka kayi hakuri yafi;
🌹= Kafun ka roki wani abu gun Allah ka yimasa godiya akan abunda kake dashi;
🌹= Ka yawaita neman gafara agun Allah kuma kar kacuci kowa;
🌹= Ka yawaita yiwa Annabi muh'd (s.a.w) salati a kullum kuma akoda yaushe saboda bakada kamarshi;
🌹= Kada kaji haushi idan kayi post a whatsapp, face book , instagram, mai ma'ana idan ba'ayi maka comment ba don ba kowa ne keson irin post dinka ba;
🌹= Kada ka fifita kayan shaidan fiye da na Allah ;
🌹= Kada kayi yaudara a soyayya saboda alhaki kyaiwkuyo ne Kaima watarana za'ayi maka ko ayiwa wani naka;
🌹= Idan kaga wani mai mummunar tarbiya Kada kayi saurin la'antarsa kai dai kayi masa addu'a ko kayi shiru;
🌹= Idan kaga mabukaci ka taimakeshi Allah zai biyaka;
🌹= Ka yawaita sadaka saboda tana yaye zunubai;
🌹= Ka taimaki tsoho ko tsohuwa , koda ba naka bane kaima watarana za'a taimaki naka;
🌹= Ka sada zamunci domin yana kara nisan kwana kuma yana kara Arziki;
🌹= Allah yakawo mana dauki ya kuma sa mudace;

SHARWARWARI>>Daga Malam Aminu Daurawa

Tattalin Arzikin Najeriya na fuskantar barazanar sake durkushewa>>Kwamitin Emefile
Kwamitin Tsara Harkokin Tasarifin Kudade na Kasa, (MPC) ya yin kakkausan gargadin cewa tattalin arzikin Najeriya daf ya ke da sake durkushewa idan babu kyakkyawan tsarin ayyukan tare tsakanin harkar kudaden kasa bangaren tafiyar da yadda ake kashe kudaden.
Kwamitin ya ce ta haka ne kawai za a iya tabbatar da dorewar kananan hanyoyin inganta tattalin arzikin kasar nan.
Kwamitinn ya yi karin hasken cewa a yanzu kalubalen da ci gaban tattalin arzikin kasar nan ke fuskanta sun hada da tsadar kayayyaki, takura wa kudaden ajiyar kasar nan da ke kasashen duniya.
Daga nan sai kwamitin ya bada shawarar matse aljihu wajen tsarin tasarifin hada-hadar kudade ta hanyar kokarin rike matsayin da aka cimma a yanzu ba tare da sakin talalar tattalin arzikin har a bari ya sakwarkwace ba.
Kwamitin ya kuma yi magana akan adadin kudaden da bankuna ke bayarwa lamuni da kuma adadin kason ribar da bankuna ke dora wa masu karbar lamunin ko bashi.
Akwai kuma adadin da sai bankuna na da wadannan kudade ajiye ne za su rika bayar da lamuni na makudan kudade.
Sannan kuma kwamitin ya jaddada cewa matsawar aka tsaurara matakan nan, to za a magance hauwawar tsadar kayayyaki, karancin hannayen jari da jarin kasan a hannayen jama’a, sannan kuma a rika yin azamar kara yawan kudaden asausun ajiyar gwamnatin tarayya na kasashen waje sannan kuma a kara inganta darajar naira a sikelin canji da takardun kudaden kasashen waje, musamman, Dala, fam da kuma Euro.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile ne ya bayyana wadannan dalili da ke neman kawo barazana ga tatalin arziki da kuma hanyoyin da ya kamata a magance barazanar, a wata ganawa da ya yi da manema labarai bayan kammala taron.
Emefiele ya ce yadda tattalin arziki ke tafiya daga watanni 18 zuwa yau, abin kai wa daukin gaggawa ne matuka.
Ya kara da cewa cancak din da aka samu na harkokin kudaden bangaren mai a farkon tsakiyar shekarar 2018 ma ya kara haddada alamomin barazanar.
Wani dalilin kuma shi ne yadda kudaden asusun ajiyar Najeriya da ke waje ya ragu daga dala bilyan 45 da ake da ita ajiye a karshen watan Yuli, 2018 zuwa dala bilyan 44 ya zuwa 201 Ga Satumba, 2018.
Harkokin musayar kudaden ketare ta ragu da kashi 38.34, wato dala bilyan 6 ta ragu a cikin watan Yuli, ba kamar watan Yuni da ya shude ba da aka samu hada-hadar dala bilyan 9.73.
Sai dai kuma a yanzu wannan kwamiti na da kyakkyawan yakinin cewa tashi da farashin danyen man fetur ya yi zuwa dala 80 a kowace ganga daya, za a samu karin karfin tattalin arziki a cikin watanni uku na karshen shekarar 2018.
A lokacin da Najeriya ta yi kasafin 2018 dai, an yi kasafin ne a bisa kowace gangar danyen man fetur na dala 51. Ga shi kuma a yanzu adadin danyen man da ake hakowa a kowace rana ya kai ganga miliyan 2.3.

Tattalin Arzikin Najeriya na fuskantar barazanar sake durkushewa>>Kwamitin Emefile

Direban fadar shugaban kasa yayi yunkurin kashe kanshi saboda rashin kyawun albashi
Wani direba dake aiki a fadar shugaban kasa me suna Offre yayi yunkurin kashe kanshi ta hanyar rataya saboda tsananin rayuwa da kuma rashin kyawun Albashi.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa, mutumin na karbar albashin dubu 25 duk wata kuma yana da mata da 'ya'ya biyu, ma'aikatan fadar gwamnatin sun bayyana cewa an sami direban a dajin Kubwa dake babban birnin tarayya Abuja rataye a jikin bishiya ya rataye kanshi.
An gano cewa Offre na yunkurin kashe kanshine bayan da matarshi ta dawo gida ta tarar da sakon da ya bari na takarda da ya bayyana haka, ai kuwa bata yi wata-wata ba ta sanar da makwauta halin da ake ciki, nanne aka shiga nemanshi lungu-lungu inda aka tarar dashi sagale a jikin bishiya yana reto.
Mutane sunyi tsammanin ya mutu amma ana cikin tafiya dashi sai ya farka.
Da yake magana akan lamarin da ya faru yace aikin shedanne kuma bazai iya tuna yanda lamarin ya faru ba.
Babban sakataren fadar shugaban kasa, Jalal Arabi ya tabbatar da faruwar wannan lamari inda yace mutumin yayi nadamar abinda ya aikata kuma yayi alkawarin hakan ba zai sake faruwa ba.
Dangane da batun Albashin ma'ikacin kuwa, sakataren yace babu abinda zasu iyayi saboda tsarin gwamnatin tarayyane haka.

Direban fadar shugaban kasa yayi yunkurin kashe kanshi saboda rashin kyawun albashi

An hana musulmai yin sallah da ajiye gemu
A wani kauyen kasar India an hana musulmai yin sallar Jam'i da kuma ajiye gemu saboda zargin mutuwar wani dan saniya a hannun wani matashin musulmi na kauyen.
Jaridar Telegraph ta ruwaito cewa, matashin da ya aikata wancan laifi an koreshi daga garin sannan kuma ya jawa sauran musulman garin an hanasu yin sallar jam'i, saidai su yi a gida an kuma hanasu sakawa 'ya'yansu sunan musulmai.
Jaridar ta ruwaito wata kotu na cewa zata tuntubi mahukunta kauye dan daukar matakin da ya dace aka wannan lamari.
Daya daga cikin musulman dake kauyen yace basu iya saka hula ko kuma ajiye gemu tunda wancan lamari ya faru sannan sai sunje wani gari me nisa suke samun yin sallah.

An hana musulmai yin sallah da ajiye gemu

Kalli kare me kafafuwa biyu yana tafiya
 Allah me iko, wadannan hotunan wani karene da ke da kafafuwa biyu ammam kuma a haka yake tafiya.


Kalli kare me kafafuwa biyu yana tafiya

UEFA ta wallafa tarihin da wasu 'yan kwallo suka kafa wanda har yanzu Ronaldo da Messi ba su kafa irinshi ba
Taurarin kwallon kafa Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun kasance gwanaye da ke ta kafa tarihi kala-kala suna zarce tarihin da wasu taurarin kwallo na da dana yanzu ke kafawa to saidai duk da wannan kokari nasu hukumar kwallon kafa ta turai UEFA ta fitar da bajintar da wasu taurarin kwallo suka kafa wanda har yanzu Ronaldon da Messi basu kafa irin ta ba.
UEFA ta wallafa bajintar da taurarin kwallo suka kafa wadda Messi da Robaldo basu kafa irin ta ba kamar haka:
Yawan buga kwallo: Messi ya buga gasar cin kofin turai sau 126 shi kuma Ronaldo ya buga sau 158 amma wanda ya kafa bajintar yawan buga wannan wasa shine golan Porto Iker Casillas wanda ya buga wasan sau 179.
Yawan cin kwallaye a wasan karshe: Messi yaci kwallaye biyu ne kawai a wasannin karshe na gasar cin kofin turai da ya taba bugawa a shekarun 2009 da 2011 yayinda shi kuma Ronaldo ya ci kwallaye 4 a wasannin karshe na gasar da ya buga a shekarun 2008 da 2014 yaci kwallaye daya-daya sai kuma a shekarar 2017 yaci kwallaye biyu. Amma wadanda suka kafa tarihin cin kwallaye mafi yawa a gasar sune tsaffin 'yan kwallon Madrid, Alfredo Di Stéfano, Ferenc Puskás, wanda ko wannen su yaci kwallaye 7 a wasannin karshe.
Dan kwallo mafi yawan shekaru da yaci kwallo: Dan wasan AC Milan, Paolo Maldini ya ci wa kungiyarshi kwallo yana da shekaru 36 a wasan karshe da suka buga da Liverpool a shekarar 2005. Sai kuma Francesco Totti da yaci CSKA Moscow a shekarar 2014 yana da shekaru 38.
Dan wasan da ya samu nasara da kungiyoyi daban-daban: Clarence Seedorf ya samu nasara da kungiyoyi irinsu (Ajax 1995, Real Madrid 1998, Milan 2003, 2007) sannan kuma Zlatan Ibrahimovic wanda shima ya samu nasara da kungiyoyi irinsu (Ajax, Juventus, Internazionale, Barcelona, Milan, Paris Saint-Germain) wadannan 'yan wasa biyu duk sun fi Ronaldo da Messi.
Dan kwallon da yaci kwallo cikin kankanin lokaci: Dan wasan Bayern Munich, Roy Makaay ya ciwa kungiyar tashi kwallo cikin sakwanni 10.12 a wasan da suka buga da Real Madrid a shekarar 2007. Ronaldo ya taba ciwa Real Madrid Kwallo a cikin mintuna 4 a wasan da suka buga da kungiyarshi ta yanzu, Juventus a shekarar 2013, yayin da shi kuwa Messi ya ciwa Barcelona kwallo cikin mintuna uku a wasan da suka buga da Celtic a shekarar 2016 wanda ya kare da sakamakon 7-0.
Dan wasan da yaci kwallo daga guri mafi nisa: Tauraron dan kwallon Manchester United, Ryan Giggs ya ci kwallaye 16 daga guri mafi nisa yayin da Ronaldo kuma yaci guda 13, Messi na da guda 14.
Dan kwallon da yafi cin kwallaye akai-akai: Tauraron dan kwallon kungiyar Bayern Munich, Gerd Müller yafi Ronaldo da Messi yawan cin kwallaye akai-akai a tarihi.
Dan wasan da ya ci kwallaye uku a wasa daya cikin lokaci mafi kankanta: Tauraron dan kwallon kafa na kungiyar Olympique Lyonnais, Bafétimbi Gomis ne yaci kwallaye uku a wasa daya cikin lokaci mafi kankanta a tarihi inda ya ci kungiyar Dinamo Zagreb a shekarar 2011. Ronaldo kuwa yaci kwallaye uku a wasa daya cikin mafi kankanin lokaci na mintuna 12 lokacin yana Real Madrid inda yaci kungiyar Malmao a shekarar 2012, yayin da shi kuwa Messi ya ci kwallayenshi uku a wasa daya cikin mafi kankanin lokaci na mintuna 22, Arsenal ce yaci wadannan kwallaye a shekarar 2010.
Dan wasan da yafi yawan kwallaye a kakar wasa ta gasar ta cin kofin zakarun turai: Dan wasan kungiyar Porto, Radamel Falcao ya ci mata kwallaye 18 a kakar wasan cin kofin zakarun turai ta 2010/11. Messi kuwa a kakar wasan 2011/12 ce yqci kwallaye mafi yawa, 14. Shi kuwa Ronaldo yaci kwallayenshi mafi yawane a kakar wasan 2013/14 inda yaci kwallaye 17.

UEFA ta wallafa tarihin da wasu 'yan kwallo suka kafa wanda har yanzu Ronaldo da Messi ba su kafa irinshi ba

Kalli Ado Gwanja da Fati Shu'uma
Taurarin fina-finan Hausa, Ado Isah Gwanja kenan da abokiyar aikinshi, Fati Shu'uma a wannan hoton nasu da suka haskaka, muna musu fatan Alheri.

Kalli Ado Gwanja da Fati Shu'uma

 Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da tasha kyau, tubarkallah, a wasu hotunan tana tare da abokan aikinta irin su, Yakubu Muhammad da Umar M. Sharif, muna musu fatan Alheri.
Kalli wasu kayatattun hotunan Maryam Yahaya da abokan aikinta








Kalli wasu kayatattun hotunan Maryam Yahaya da abokan aikinta

Kalli wani kayataccen hoton Osinbajo da diyarshi
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo kenan a wannan hoton nashi inda yake tare da diyarshi, sun haskaka muna musu fatan Alheri.

Kalli wani kayataccen hoton Osinbajo da diyarshi

Tauraron fina-finan Hausa kuma Mawaki, Adam A. Zango kenan a wannan hoton inda yayi canjin shekar kungiyar kwallon kafa daga Manchester United zuwa Real Madrid.
 Abokin aikinshi, Ali Nuhu ma ya tayashi inda yace, 'Yan Man U sai ku yi hakuri, Madrid ta kwace shi.

Adam A. Zango ya canja sheka daga Man U zuwa Madrid

Mourinho da Pogba sun yi sa-in-sa
Wani faifan bidiyo ya nuna Jose Mourinho da Paul Pogba suna sa-in-sa a wajen atisaye a ranar Laraba, kwana daya da kocin ya karbe mukamin mataimakin kyaftin daga dan wasan tawagar Faransa.
Mourinho bai saka Pogba a karawar da Derby County ta yi waje da Manchester United a Caraboa Cup a ranar Talata a Old Trafford ba.
Bayan da aka tashi daga fafatawar Mourinho ya tabbatar da karbe mataimakin kyaftin din United daga Pogba, amma ya musanta zargin cewar ya samu sabani da dan kwallon.
Derby ta yi nasara a kan United a bugun fenariti da ci 8-7, bayan da suka tashi wasa 2-2.
A ranar Asabar United za ta ziyarci West Ham United a gasar Premier wasan mako na bakwai.
BBChausa.

Mourinho da Pogba sun yi sa-in-sa

Asirin Wasu Manya A Kasar Nan Zai Iya Tonuwa Idan Har Rikici Tsakanin Shahararrun Mata A Kafafun Sadarwa, Wato Jaruma Empire Da Layla Ali Othman Bai Kawo Karshe Ba
Rikici ya barke tsakanin wasu sanannun mata na kafafun sadarwar zamani wato Hauwa Sa'idu Muhammad wadda aka fi sani da Jaruma Empire da kuma Lalya Ali Othman.
A wani bidiyo na mayar da martani da Jaruma Empire ta fitar, an ga tana yi wa Layla Ali zagin kare dangi bisa yawan hannunka mai sanda da take yi mata a shafin sadarwa na Instagram, wanda hakan bai yi mata dadi ba.
Jaruma Empire wadda babbar kawa ce ga Rahma Indimi, ta kuma kara da fallasa yadda Layla take sharholiya da manyan mutane, inda a bidiyon da ta fitar har da zargin Layla na da alaka da Sanata Abdul Ningi, wanda a cewar ta an jima ana zargin tana tarayya da Sanatan.
Babbu shakka idan har rikicin da ya bullo tsakanin Jaruma Empire da Layla Ali Othman bai kawo karshe ba, za su iya tonawa wasu manyan kasar nan dake sharholiya da 'yan mata asiri, ganin yadda kowacensu ta daura damara domin amayar da abin da ya jima a boye a tsakaninsu.
Rariya.

Asirin Wasu Manya A Kasar Nan Zai Iya Tonuwa Idan Har Rikici Tsakanin Shahararrun Mata A Kafafun Sadarwa, Wato Jaruma Empire Da Layla Ali Othman Bai Kawo Karshe Ba

Kalli kayatattun hotunan Rahama Sadau daga kasar Amurka
 Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a birnin New York na kasar Amurka take shakatawa, taje kasarne dan halartar taron majalisar dinkin Duniya akan kawar da tarin Fuka.


Kalli kayatattun hotunan Rahama Sadau daga kasar Amurka

Kalli wannan hoton na Umar M. Sharif da Bilkisu Shema
Jaruman fina-finan Hausa, Umar M. Sharif da abokiyar aikinshi Bilkisu Shema kenan a wannan hoton nasu da suka haskaka, muna musu fatan Alheri.

Kalli wannan hoton na Umar M. Sharif da Bilkisu Shema

An kama mutuminnan da yayi barazanar kashe Atiku da kuma yiwa matarshi da diyarshi fyade
 'Yansanda sun kama mutuminnan da ya yi barazanar tarwatsa jirgin tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da kuma cewa zai yiwa matarshi da diyarshi fyade ya kuma kashesu.
Mutumin dan shekaru 43 da haihuwa me suna, Augustus Akpan ya fitone daga jihar Akwa-Ibom dake kudancin Najeriya kuma an kamashine a kan hanyarshi ta tserewa zuwa Birnin Legas dan gujewa neman da 'yansanda suke mishi kamar yanda kakakin rundunar 'yansanda ta kasa Jimoh Moshood ya bayyanawa manema labarai kamar yanda jaridar the nation ta ruwaito.
Mutumin yayi amfani da wayar satane yayi wancan barazana sannan ya amsa laifinshi, an kuma sameshi da laifin yaudarar wasu manyan mutane a kasarnan makudan kudaden Najeriya da na kasar waje, mutumin ya iya yaruka kamar su turanci, da yaren kasar Portugal dana Rasha da Ibibiyo.
Yace yayi kokarin amfarar iyalan Atikun kune ne sai baiyi nasara ba shiyasa ya buge da musu barazana kuma bashi da alaka da wani dan siyasa.
Hukumar 'yansanda tace da zarar ta kammala bincike zata tasa keyarshi zuwa kotu.

An kama mutuminnan da yayi barazanar kashe Atiku da kuma yiwa matarshi da diyarshi fyade